Chapter 9
Chapter 9
da kyar tana kallonta. "Menene Hameeda? Me ya kawo ki?" Ta tambaya ranta a ɓace. "Mammy I'm hungry. (Yunwa nake ji.)" Taja tsaki a hankali. "Ina Nannynki?" Sai kawai ta miko mata takardar hannunta, kamar ba zata karba ba sai kuma ta yatsunta biyu ta sakala ta cikinsu sannan ta buɗe ta. 'Ajiya I'm sorry Oo, dey don call me now say my mother dey hospital. I'll return tomorrow by God grace.' Ta sake jan wani tsakin mai tsayi, bata san sau nawa take gayawa Mary cewar ta daina yi mata pidgin a gida ba, amma don rashin mutunci shine har rubuto mata take yi a takarda. Ta juya ta sake kallon yarinyar data tsura mata idanu, dogwayen gashin idanunta sun kusa haɗewa da juna, yadda take lumshe su ya tuna mata da fuskarsa a lokaci guda. ...idanunka kake gani ko Ma'aruf? Irin naka ne sak! Muryar Mami ta haska a cikin kanta ranar farko na zuwan Hameedan duniya, ta tuno fuskarsa, yadda ya kalmashe ta cikin hannunsa, lumsassun idanunsa na haskawa da tarin ƙaunar da kamar wani abu ba zai taɓa giftawa a cikinta ba. Ruƙayya ta sake yin wani tsakin da ya riga ya shiga cikin dabi'arta kafin ta ture bargon gadon ta miƙe, wata lallausar doguwar rigar bacci ce a jikinta da idan ka kalle ta zaka ga kamar tana zamewa ne tsabar santsi da kuma kyallin da take yi. Ta kalli agogo wajen karfe bakwai na dare. "Baki ci abinci bane da rana?" Ta tambaya tana daure gashin kanta da za'a kwana a yini ana musu da wani akan cewar nata ne, don human hair ne (gashin mutum) da aka dinka mata shi cikin nata ya saje tsaf! "Mami tun da na sha tea, Mary bata bani komai ba. Waya take ta yi." Gwarancin yarinyar mai daɗi ya fito tana kallonta. Wani tsakin ta sake ja kafin ta dauki wayarta sannan tace. "Oya, taho muje to." Da sauri yarinyar kuwa ta sauko tabi bayanta, suka fita daga ɗakin zuwa wani dogon korido daya hada fuskokin ɗakuna, suka isa wani rantsatstsen falon da komai na cikinsa kalar ruwan gwal ne da kuma makuba, a gefensa akwai matattakalar bene, suka sauka har kasa zuwani falon da yafi wannan girma, ta jikin dining area suka shiga wata kofar da take ta kitchen ce, wani katon kitchen da yake a gyare tas. Babu ko tukunya guda daya akan gas don haka ta san babu wanda ya dawo a cikin kannen nata uku maza, suma can yawonsu waye ma zai gansu yanzu da magaribar nan? Dama Ashraf mai bi mata ne idan ya dawo daga aiki sau da yawa zai shigo ya dafa abincinsa tun bayan da suka rasa Josh (mai yi musu girki) yanzu kuma yayi aure sati uku da suka wuce don haka babu mai shigowa kitchen din. Hameeda ta ɗane kan ɗaya daga cikin kujerun da suka zagaye worktable din kitchen din sannan ta zuba mata idanun tana jiran taga me zata yi, Allah ya sani ita bata son wani girki yanzu, da safen nan fa dawowarta kenan Nigeria daga ƙasar Paris inda suka tafi ita da mahaifiyarta, shi yasa ta kwanta take ta sharɓar baccin ta kuma yanzu ta tashi ta kama girki?... sai kawai ta dago da wayarta ta shiga nemo nambar Mariya, babbar ma'aikaciyar gidan. "Hajiya barkanmu da safiya. Ina kwana." Muryar dattijuwar ta cika kunnenta, bata ko amsa ba tace. "Mariya, abinci zaki kawowa Hameeda yanzu, a dafa mata duk abinda zata iya ci kawai." Daga cikin wayar Mariyan tace. "Hajiya ai bana gidan, yau kwana na uku a madobi, mahaifina ne ya rasu wallahi, amma su Jamila da Aisha suna nan." Ta ɓata rai a lokaci guda don ta manta lokacin da suna can taji mahaifiyarta ta na fada, sai kawai tace. "Allah ya jiƙansa." sannan ta kashe wayar. Ba zata yarda ƴarta taci abincin waɗannan kazaman yaran ba su tsaya a iya gyaran gidan da suke yi kawai, don ko Mama Mariyan ma da suka saba da ita tun yarintarsu ba kowanne girkinta suke ci ba, tunda Josh ya mutu shikenan kowa ya ta'allaƙa akan siyan abinci a waje tunda dama gidan ƴan maza ne ita kadai ce mace. "Hameeda me zaki ci?" "Mammy banda indomie." Ta fadi hakan alamun da gaske ta gaji da cin indomien, haka yasa ta gane cewar Indomie kawai Maryn ke ɗura mata da basa nan don haka ta gyaɗa kai kawai. Ta ajiye wayar akan table din sannan ta juya ta shiga store, ta fito da kwai guda uku a hannunta, ta kunna ruwa a kettle sannan ta fasa kwan ta soya shi cikin ƴan mintuna, ta haɗa mata tea da ruwan zafin da yayi sannan ta ɗauko biredi a fridge ta saka mata kwan a tsakiyar, ta zauna a kusa da ita tana kallon murnar dake kan fuskarta sanda ta fara cin ƙwan, har yanzu bata kai shekara hudu ba amma tsaf ta iya cin abinci da kanta, sai kawai tayi murmushi sannan ta janyo wayarta. Ta shiga whatapp tana fara ganin yadda messages ke tururuwa har da sababbin nambobi, sai da suka gama tsaf sannan ta danna kan sako guda ɗaya mai sunan Jawad da mintuna biyu kawai akayi da turo shi. "Baby kin dawo ko? I'm badly missing u here... Zanzo anjima kinji." (Ina mutukar kewar ki anan.) "Mammy nayi missing dinki." Muryar Hameeda ta katse ta daga amsar da take shirin rubutawa. Ta juyo ta kalle ta, tana ta cin biredin da sauri alamar da gaske yunwa take ji. Itama tayi kewarta da gaske shi yasa ma ta kasa jiran Maamah ta taho. Bayan bikin Ashraf ne suka tafi Paris ɗin ita da mahaifiyarta don medical check-up kasancewar hidimar bikin ta wajiga su da yawa, kuma satinsu ɗaya acan ta gaji ta taho don ranar da suka tafi ma Hameedan na bacci a hannun Mary ko sallama basu yi ba. Allah ya sani ta fara gajiya da wannan rayuwar, ba haka take hango ta ba sam, ba haka ta dinga hango abubuwa ba lokacin da mahaifiyarta dama kawayenta suka bata goyon bayan kashe aurenta ba, Maamah cewa tayi... "Idan baki fito daga gidan nan ba kin kusa kashe kanki ki tsufa a banza Ruƙayya, ta yaya zaki zauna babu wani isasshen hutu sannan kuma ki fara tara ƴaƴa bi da bi? Yanzu kika fara rayuwar ki fa, kina da dama mai yawa a gabanki Rukayya." Haka take gaya mata kullum, shi yasa ta rufe idanunta a wancan lokacin ta danne zuciyarta tayi abinda ya fito da ita ɗin, kuma har bayan aurenta da Alhaji Ahmad, tafiya take akan wadannan kalaman na mahaifiyar tata, takunsu take bi har ya kai ga mutuwar aurenta da Alhaji Ahmad ɗin shima, kuma ko a yanzu ma bata fasa gaya mata cewar komai kaddara ce ta cigaba da cin ganiyarta ba, amma ita ta sani cewar bayan wannan ƙaddarar har da ƙaddarar zuciyarta akansa shi ma. Ta san duk irin halayen da zuciyarta ta shiga a gidan Alhaji Ahmad, ta san duk irin wahalhalun data fuskanta a kowanne lokaci na zamanta a gidan yadda ta dinga kwatanta abubuwa a gidanta na farko da kuma nasa tana ganin bambanci su a baiyane har suka kai ga matakin ƙarshe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73