Chapter 8
Chapter 8
ya kamata yaga Baffa a yau, idan yana gidan kuma fa? Sai yasa yatsan sa ɗaya ya share dukkan messages ɗin sannan ya lulubo nambar mahaifin nasa amma sau biyu ya buga bata shiga ba, don haka ya nemo ta Mami. Bugu ɗaya kuwa muryarta ta shiga kunnensa. "Mai gaskiya na, kun taho?" Ta kira shi da sunan data laƙaba masa tun yarintarsa. Sai ya sake lumshe idonsa ya koma da baya jikin kujerar lokacin da Ishaq da Baba Sani suka buɗe ƙofofin motar suka shigo. "Eh Mami, Baffa yana gida kuwa?" "A'a yana office shima har yanzu. Na bayar direban Hajiya Madina zai kawo muku abinci yanzu, wataƙila ma kuyi daidai dashi." Wani abu ya motsa a kirjinsa, don yayi kewar irin wannan kulawar tata a ƴan kwanakin nan, sai dai kafin ya saurari abinda ta cigaba da cewa hankalinsa ya kai ga abinda Ishaq ke cewa cikin wayar sa da aka kira ya amsa. "To shikenan gamu nan insha Allahu..." "... Akwai maganar da zamu yi Ma'aruf, nima nafi son ka samu hutu sosai zuwa goben." Sauran maganar Mamin ta shiga kunnensa bayan Ishaq ya kashe wayar da yake yi." "Ma'aruf, kana jina kuwa? Da kaci abinci ka sha magungunan da aka baka " Yaji ta sake faɗa lokacin da Ishaq ke cewa Malam Sani... "Sakataren Baffa ne yakira, wai Baffan yana son ganinmu a office ɗinsa kafin muje gida, ka juya ta wanna U-turn ɗin sai mu koma." Ba shiri Ma'aruf yaji wani abu ya zarce cikin maƙogwaronsa, don tun bayan farkawar sa sau ɗaya kawai yayi waya da Baffan, a jiya daya kira ta wayar Ishaq, ya tabbatar masa da cewar lafiya yake jin kansa shikenan bai kara nemansu ba, amma ko Baba Usman ya sake kira a safiyar yau kafin su taho. Yana jin yadda Mamin ke cigaba jero masa tarin tambayoyi ta cikin wayar amma hankalinsa sam baya kanta har Malam Sani yasha kan U-turn din da Ishaq ya nuna wanda zai komar dasu baya zuwa hanyar Office ɗin Baffan, wani ƙaton branch na kamfanin su inda iya ma'aikata ne kawai a wajen. "Muhammad..." Muryar Baffan ta kira shi kuma a lokaci guda amonta ya ratsa har cikin kansa bayan sun isa Office ɗin, bayan sun shiga ciki kuma Baffan ya sallami wasu mutum biyu da yake tare dasu a lokacin, sannan bayan Ishaq ya dauki wata wayar ƙarya ya fita don dukkaninsu sun fahimci cewa dashi kadai yake son magana. Don haka ba shiri Ma'aruf yaji maƙogwaronsa ya bushe a lokaci guda, saboda Baffa baya taɓa kiransa da wannan sunan sai idan har wani zance mai muhimmanci zasu yi, kuma rana ta karshe da zai iya tuna ya kira shi da hakan shine ranar da aka daura auren sa. Ya gyara zama a hankali yana jin yadda Baffan ya cika masa office din ta koina saboda kwarjini. "Sun turo min da takarda wadda take bayanin ciwon naka." Ya san takardar shima, sun tura ta email ɗinsa sannan sunyi printing ɗinta a cikin tarin takardun da aka sallamo shi dasu. "Sun ce a cikin shekaru biyu kawai ciwon ka ya kara haɓɓaka har ya kai matakin karshe, shi yasa abinda kayi ya faru..." Baffan ya faɗi haka sannan kuma yayi shiru, wannan dai al'adar ta manya. Ƙarar sautin shigowar saƙo daga wayar dake aljihun Ma'aruf ya cika shirun dakin kafin ya cigaba. "Ko zaka iya gaya min a shekaru biyun baya kana ina Ma'aruf?" Sai ya gyara zamansa a hankali, yana tuno ranar da Baffan ya naɗa shi a matsayin manajan kamfanin 'Bakori Enterprises' ranar da burinsa na farko ya fara cika a duniya. "Baffa... Shekaru biyu baya shine lokacin da ka bani matsayin manaja a kamfanin nan." Bai kalle shi ba, amma yaji sanda ya girgiza kansa. "Ba wannan ba, rayuwarka personally Ma'aruf, kana ina?" A yanzu ya rikice, yana jin kamar ma bai warke ba gabaɗaya, kamar ya sake bin jirgi ya koma asibitin nan ya kwanta. "Ka manta?" Ya tambaya amma bai bari ya amsa ba ya cigaba. "... Bari ni na tuna maka, shekaru biyu baya kana tare da iyalinka Ma'aruf, shekaru biyu baya kana tare da matar da naje na karba maka aurenta har ma da yarinya, a shekaru biyu baya kai cikakken mutun ne mai kamala da mutunci a idon mutane, kuma a tsawon shekarun da kayi cikin wannan mutuncin, hankalinmu da naka bai taba tashi kamar yadda yayi a yanzu ba." Wani abu ya zarce a maƙogwaron Ma'aruf, yaji wani ɓangare na ƙwaƙwalwar sa na gaya masa cewa wannan ce damarsa, yau shine lokacin da zai gayawa Baffa abinda shi da ishaq suka dade suna ɓoyewa, yau ya kamata ya gayawa Baffa cewa ba haka bane, abinda ya faru a zamansa da Ruƙayya har zuwa rabuwarsu ba yadda suke tunani bane sam. "Na san da wannan tunin da nayi maka ka fahimci abinda ni dama duk sauran al'umma suka fahimta Muhammad, don haka kaje ka fara shirye-shirye, nan da wata guda zan karɓa maka wani auren tare da na ƙannenka." Sai da aka shafe sakanni kafin maganar ta shiga cikin ƙwaƙwalwar Ma'aruf, da wani irin ƙarfin da sai da yayi da gaske kafin ya iya jawo iska ta shiga ƙirjinsa, sannan a karo na farko tun bayan fitar Ishaq ya ɗago idanu ya kalli mahaifin nasa. Sai dai me? Maimakon fuskar Baffan, sai hoton wajen ya canja a idonsa da wani lokaci da ya faru a shekaru biyu da suka wuce... Lokacin daya shaƙe wuyan Rukayya da duka hannyensu biyu, yaji ƙarar sautin karkarin da take fitarwa a lokacin da kuma yadda hawaye ke zuba daga idanunta yayin da take kallon ƴarsu da bata fi watanni shida a sannan ba... Babyn da ya karɓe daga hannunta ya wancakalar da ita a cikin falon, kanta ya bugu da kujerar gefe ta shiga ƙwallara kukan daya karaɗe gidan gabaɗaya, wannan sautin kukan da a kowanne daren duniya, dashi yake kwana a kunnuwan sa! *** Me ya faru shekaru goma da suka wuce? Wane bincike Ma'aruf ke yi da har ya kai ga tashin ciwonsa? Wacece Rukayya? Me ya faru da ita da kuma ƴar ta? Sannan wacece amarya ta huɗu a bikin iyalan gidan Alhaji Mansour Bakori? #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. BABI NA UKU. **** A wannan daren... NO. 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano. . A cikin ƙawataccen ɗakin, wata yarinya ta buɗe ƙofar ta shigo, ba zata fi shekaru uku da kaɗan ba, tana sanye da irin kayan yara kamarta, wani ɗan gajeran skirt kalar lemon greeen, (lemon tsami) sai farar rigar da itama akayi mata da ado da irin kalar, gashinta da ba wani yawa ne dashi haka zalika tsawo ba an tufke shi cikin kalba guda biyu da ribbon masu kalar kayan. Ta karaso cikin ɗakin daya gauraye da sanyin A.cn da aka kai maƙurarta, akwai wani tebur irin na ado dake gaban hadadden gadon dakin, ta kansa ta taka ta isa kan gadon, ta hau tana bi ta kan ƙafafun wadda ke kwance har ta isa daidai fuskarta da ta rufe da bargon data lulliba gaba ɗaya. "Mammy Mammy Mammy...." Ta kira ta na bubbuga daidai kanta da ƴan hannayen nata, a lokaci guda mahaifiyar tata ta yaye bargon daga fuskarta ta buɗe idanunta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73