Skip to content

Chapter 29

Chapter 29

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

likitan ta shar'anta, da yatsa daya kawai yayi mata nuni da ta ajiye akan drawer dake gefe, kuma budewar kofarta wajen fita yazo daidai da shigowar Hajiya Kilishi da kuma Samira dake bayanta riƙe da kwandon abinci, duk da halin da yake ciki sai da yaji zuciyarsa tayi fatan yarinyar nan tana tuna Allah kamar yadda take tuna abinci. "Innalillahi wainna ilaihir raji'un, me ya faru mai gaskiya? A ina ka samo ta?" Muryar Mamin ta faɗa, sai da ya taso ya miƙe sosai sannan ya shiga gaishe ta, ta amsa tana ƙoƙarin riƙe hannun Hamidan da ya saki. Kuma sautin muryarsa a hankali ya shiga yi mata duk bayanin da zai iya a wannan lokacin yayin da take kallonsa da wannan tsananin kulawa da kuma damuwar da kullum ke ɗamfare a fuskarta game dashi. "Kar damu, komai zai daidaita insha Allah Ma'aruf, daɗin abin komai bai ja da nisa ba, ka kwantar da hankalinka dan Allah mu bi komai a sannu kar ka damu kanka da wani tunani, Baffa ya dawo na shaida masa, shima yayi mamaki sosai amma yace a bari ta fara farfaɗowa tukunna kafin komai ya biyo baya, don haka mu tsaya anan, mu tsaya a iya nan dan Allah mai gaskiya." Roƙon da take ya san har da wani bari na muryar Baffa a ciki, don dukkaninsu sun san irin abinda zai iya, don haka bai ce komai ba kawai yayi shiru yana sauraren ta, sauraren da a cikinsa ta fahimci cewa ko ta cigaba da maganar ba fahimtar ta zaiyi a lokacin ba don haka sai tayi shiru kawai ta juya tana kallon fuskar Hamidan. A lokacin Samirah ta zubo abinci a plate ta miƙo masa, kuma ganin ƙoƙarin ta ne kawai ya gaya masa cewa ya kamata yaci abincin ba wai don ya so ba, don haka ya karɓa a lokacin da itama ta koma gefe tana kallon fuskar yarinyar. A cikin tunaninsa yaji Samiran na waya dasu Munaya da kuma amaren da wai dawowarsu kenan daga wajen gyaran jiki suna tambayar sunan asibitin zasu zo, amma Mami ta karɓi wayar tace duk suyi zamansu don in suka ce zasu taho ɗin a yanzu ba'a san adadin wanda zasu biyo su ba kasancewar suna dab da fitowa yanzu ma wasu ƴanuwan Hajiya Maimuna ma suka sauka daga jigawa. Ma'aruf na jinsu bai ce komai ba, wayarsa kawai yake kallo idanunsa na wasa da adadin messages ɗin dake shigowa bi da bi suna nunawa akan screen ɗin, amma a cikin zuciyarsa tunawa yake da zagayen halin da yake ciki bayan wannan, cewar wannan shirye-shiryen bikin da ake shirin farawa har dashi a lissafin. Don tun daga lokacin da ya samu wannan takardar mai dauke da sunan Amina, kuma ya tabbatar cewa zancen auren bai lalace ba kamar yadda yayi fata a farko, sai kawai ya mayar da hankali kan aikinsa kuma yawan aikin ke sa shi sha'afa da zancen auren sai wasu abubuwa kamar wannan sun faru da zasu tuna masa cewar shima yana jiran faruwar auren ne don ya fara nasa sabon binciken da har cikin zuciyarsa yake jin cewa wannan hanyar zata iya kaishi ga nasarar da ya shafe shekaru yana lalubenta a cikin duk wani abu da ya danganci kayan Jamal. Misali irin lokutan da Mamin ke kiransa ta bashi wasu bayanai na cewar an kai kaya gidansu yarinyar ko kuma ya turo da wani adadin kudi za'ayi abu a kaza, abubuwan da suke sa shi yana jin cewa da gaske auren zai yi don Baffa ma ya kafa sharaɗin cewa gidan zai dawo ɓangaren da Baba Alhaji ya taɓa zama, yaje kamar yadda Aa ya marta har sau biyu yaga gyaran da ake yi, amma daga haka bai kara tunawa ba ya cigaba da harkokinsa don damuwarsa ba sai ta komai yayi daidai bane, ta ya iya kammala abinda ke gabansa ne kafin lokacin don ya sami nutsuwar da zai yi dukkan bincikensa akan yarinyar. Ya cije leɓɓensa a hankali yana tuno kalaman da Faruk ya faɗa masa kwanakin baya. "Sake yin aurenka shawara ce mai kyau B, amma me yasa sai wannan yarinyar? Kace mahaifinta ba wani bane, kuma kaima ba saninta kayi ba balle ince kana sonta ne, beleive me akwai tarin ƴaƴan masu kuɗin da har layi zasu yi idan kace zaka zaɓa." Ya faɗi hakan ne ranar da Baffa yasa aka raba katin ɗaurin auren ga kowa a Office ɗin kuma mamaki ya kama su ganin cewa har da sunansa, don haka Faruk ɗin yayi wannan ƙorafin ne bayan ya shaida masa yadda al'amarin ya kasance. Kuma kallonsa kawai yayi a lokacin da dukkan tunanin da bai zo kansa ba, cewar iyayen yarinyar ba masu arziƙi bane, ya sani cewar maza irinsa basa aure a irin waɗannan gidajen, misali aurensa da Ruƙayya shine daidai, don ko irin manyan mutanen da suka halarci ɗaurin auren nasu daga bangaren mahaifinta ma wani abu ne. Amma baya jin ko bashi da wani abu da yake nema daga yarinyar hakan zai dame shi, don ba auren ko itace a gabansa ba, kuma kuɗin mahaifinta ba abinda zasu tsinana masa kamar yadda na mahaifin Rukayya ma basu kare shi da komai ba sai abinda yake ganin yanzu har dasu a silar sa. Tuna cewar bai ma taɓa ganinta ba har yanzu yasa ya jinjina kansa a hankali, bai sani ba idan ya kamata a kira wannan al'amarin auren gaske bane wannan. "Ina kika baro masu yin cin-cin ɗin ne da kika biyo ni?" Yaji Mami na tambayar Samirah bayan ta ajiye wayar, sai dai bai bari ita ɗin ta bata amsa ba ya miƙe tsaye, muryarsa da zurfi yace. "Zanje in dawo." Sai ta girgiza kanta.. "A'a, kaje ka kwanta ka huta kawai, ni zan kwana da ita anan, ka tafi da Samira ka ajiye ta a gida sai ta ɗebo min ƴan kayan kayan da zamu buƙata zuwa, zan kira Malam Sani ya kawo min." Ya cije leɓɓensa kaɗan yana bin maganganun nata kafin ya gyaɗa kansa sannan yayi mata sallama ya juya tare da ɗaukar hularsa da ya ajiye daga kan wata drawer a gefe. Samiran ta biyo bayansa, kuma har ya isa waje jikin motarsa, zuciyarsa na riƙe da yadda muryar Mamin ta fito da tsantsar damuwa da kuma kulawar da ba mai iya ƙiyasta yawanta, a lokuta da yawa yasha ƙiyasta yadda zuciyarta ke iya ɗaukar damuwar tarin mutane da tarin kyautatawa ga duk wani mahuluki da zai shigo hanyarta balle kuma shi da kowa ya sani cewa matsayinsa daban ne a wajenta. Ya san itace ja gaba akan komai na bikin nan, amma duk da wannan hadaniyar ta tsallake ta zata zauna, bai san irin son da yake yiwa Hajiya Maimuna mahaifiyarsa ba bayan tsananin girmanta da yake gani, amma Mami zai ajiye ta ne gefe ya tara dukkan ƙaunar waninta a wani gefen, don yana daga cikin abinda yasa yake son yayi tsawon rayuwa mai kyau don ya kyautata mata. A sanda lokaci ke wucewa da wannan tunanin a zuciyarsa, a lokacin Hajiya Kilishi ke girgiza kanta daga cikin ɗakin asibitin bayan fitarsu, zuciyarta na ƙara gaya mata cewar ba haka tsarinta yake ba, ita ke da ikon ƙaiyade duk mutanen da zasu shigo rayuwar

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73