Chapter 15
Chapter 15
Amina ta ƙara share hawayen idanunta, Abdallah ne ta sani, don dama tun jiya take tsammanin zuwansa dama don ta sani lokacin komawarsa makaranta yayi, sai dai yazo a lokacin da take jin bata son ganin fuskar kowa, maganganun Baba da Amma sun riga sun cike duniyarta ta yadda bata tunanin a cikin zuciyarta ma akwai wani waje komai kankantarsa da zai sake ɗaukan wani abu a daren yau. "Ki tashi kije, ganinsa zai sa ki sake yankewa kanki hukuncin da ya dace Amina, daga daren yau zuwa gobe kawai kike dashi..." Muryar Amman ta sake faɗa, taji kamar tayi ihu lokacin data ɗago ta kalle ta, Hafsa na tsaye har yanzu sai kallonsu take alamun rashin fahimta akan fuskarta, kuma daga yanayin Amman ta san ko ihun tayi ba zata canja maganarta ba don haka ta sake goge hawayen da bayan hannunta sannan ta miƙe a hankali tana jin yadda kowa ce kalma da iyayen nata duka furta tayi mata tsaye a zuciya bayan nauyinsu da take ji a kafaɗunta. Akan igiyar tsakar gida ta tarar da hijabin da Maryam ta goge ɗazu don gobe za'ayi musu hotunan photo album ɗin sauka a islamiyyar su, na sallar idinsu ne, dogo har ƙasa kalar ruwan ƙasa, ta jawo shi kamar zata saka amma sai ta fasa, ta nufi ƙofar soron ta tsaya, ziciyarta na ƙoƙarin ƙulla ta yadda zata yiwa Abdallahn bayanin komai, komai ɗin da itama bata gama sani ba, taji ɓangare da yawa a cikin ƙwaƙwalwar ta na gaya mata cewa fitar ta a wannan lokacin ba alkhairi bace, don haka sai kawai ta dawo ta kira Adam dake karo da kwanuka a kitchen. "Adam zo." Ya juyo riƙe da plate yana kallonta kafin ya ajiye shi ya biyo bayanta, suka koma har hanyar soron. "Adam dan Allah kaje kace masa bani da lafiya sosai, ya dawo gobe ba zan iya fitowa yanzu ba." Kamar ya tambaye ta dama ta sanshi ne tunda bai taba ganinsa a gidan nasu ba, sai kuma kawai ya fasa ganin yadda idanunta suka yi ja ya san ba lallai taso tambaya a lokacin ba, ya juya ya fita, ita kuma ta tsugunna a wajen tana ƙara share hawayenta ba tare da ta fahimci kuskuskuren da tayi ba. Lokacin da Adam ya fita, Ma'aruf na tsaye har a lokacin kuma ganin tahowarsa yasa ya ɗago da hannayensa duka biyu a hankali yayi baya da hular (hood) dake kansa, fuskarsa ta fito cikin hasken ƙwan fitilar barandar gidan, "Yaya tace wai dan Allah kayi haƙuri bata da lafiya ba zata iya fitowa ba ka dawo gobe." Ba shiri wani murmushin ya subuce a fuskar Ma'aruf, For real? Shine ma zai dawo goben? Bata san me ta tsallake bane, sai kawai ya gyada kansa tare da faɗin. "Okay." Har Adam zai juya yayi saurin tsayar dashi. "Kana ji ko, ɗan tsaya ka bata wannan." Adam ɗin kuwa ya tsaya, shi kuma ya buɗe ƙofar motar ya buɗe aljihun dake jikin dashboard ya zaro wata jotter da biro daya san Ishaq baya taba rabo dasu motarsa a matsayinsa na lawyer, ya yago takarda guda ɗaya ya ɗora daga saman yayi wani rubutu layi biyu da rabi kawai sannan ya rubuta sunansa daga ƙasa. Ya kalli abinda ya rubuta din yayi wani guntun murmushi kafin ya juyo ya mikowa Adam ɗin "Nagode sosai kaji." Ya faɗa yana sake yi masa wani murmushin, da fara'a shima Adam ɗin ya amsa yana masa a sauka lafiya kafin ya juya, shi kuma ya jefa kansa baya jikin motar yana cusa hannunsa na hagu cikin gashin kansa. Ba haka yaso ba, amma hakan ma yayi... Ya riga ya gama da yarinyar nan ya sani, don abinda su Baffa ke tunani ba zai taɓa yiwuwa ba. Aka ɗauke wuta a daidai lokacin, unguwar tayi wani irin duhu dinɗim kamar yadda yake jin zuciyarsa! Don haka ba shiri ya kunna motarsa ya shiga ya bar wajen. "Gashi yace in baki." Adam ya faɗa a cikin duhun soron bayan ya koma, Amina tayi saurin sake goge hawayenta kafin ta karbi takardar ba tare da tunanin komai ba don ta san ba wani abu bane Abdallahn ya iya rubuto mata fatan samun sauƙi dama, ta damƙe ta a hannunta sannan ta miƙe ta bi bayansa. A kitchen suka tadda Amma na kokarin kunna kyandir guda biyu Hafsa kuma na sake zuba abinci itama, kuma bayan ta amsa sallamarsu sai ta miƙowa Amina guda ɗayan yayin da Adam ya shiga fadan cewar Hafsan ta dauki farantinsa. Ta wuce ɗakinsu kai tsaye, ta ajiyewa Maryam Hijabin akan katifarta sannan ta manna kyandir din akan wata kwalbar magani, a gabansa ta tsugunna hannunta rike da takardar, daga jikinta har zuciyarta daban take jinsu, wucewar awa guda kawai ta tafi da Aminar da take a baya, a yau da safe ma... tana jin zata rubuta dukkan abinda ya faru a daren yau a wajaje da yawa ta yadda ba labarinsa ba zai taɓa gogewa ba. Ta sake goge wani hawayen sannan ta buɗe takardar a hankali, zuciyarta cike da fatan ta karanta wani abu mai rangwame daga Abdallan ko yaya ne wataƙila ya iya zaftare wani ɓangare na damuwarta, sai dai kuma rubutun da idanunta suka gani a jiki shine abu mafi tashin hankali fiye da duk maganganun da rayuwarta taci karo dasu a wannan daren. Kar ki yarda da auren nan, da gaske ne abinda suka faɗa miki, I'm a psycho, zan kashe ki idan har kika shigo rayuwata. Ma'aruf B. ***** 11:15Am. "Mai gaskiya kaci abincin kasha magunguna naka?" Muryar Hajiya Kilishi ta tambaya cikin wayar dake kare a kunnenta, kuma a cikin wayar aka bata amsar data sa ta gyaɗa kanta kafin ta sake cewa. "Zan kira Ishaq, zamu yi maganar komai dashi, idan zaka shigo kawai ka taho da magungunan duka." Har tayi shiru sai kuma tace. "Dan Allah Ma'aruf kafin ka shigo kaje ka aske gashin nan dan Allah, ko ɗazu da na shiga wajen Inna Danejo abinda ta fara tambayata kenan." Amsar da Ma'aruf ɗin ya bayar mai tsawo ce, don ta dade tana saurarensa kafin tace, "Shikenan idan ka shigo kayi mata wannan bayanin da kanka, akwai faten dankali a ɗaya daga cikin kwanukan abincin nan ka ganshi?" Ya fadi abinda ya saka ta yin dariya kafin ta sake cewa. "To aci lafiya, sannan idan ka wuce 1 baka shigo ba, zaka ganmu gabadaya gidan mun taho." Ya fadi wani abun da ya kara saka ta dariyar da tafi ta farko tana fadin. "Ai da ƴanmata zamu zo sai suyi muku sharar." Da haka suka yi sallama, tana sauke wayar daga kunnenta. "Wallahi na dade ina gaya miki Hajiya, da irin mahaukatan secret agent din nan na turawa ya kamata ki samu aiki, ko banza dukkanku zaku amfana da juna, ke da kudinsu su kuma da kissa irin taki." Cewar Hajiya Salamatu, wata hamshaƙiyar ƴar gayu dake zaune daga gefen Hajiya kilishin. Wajen ƙarfe goma sha ɗaya ne na safe a lokacin, kuma kasancewar ranar ta asabar ce kowa yana nan, gidan cike yake da hayaniya da kuma hada-hadar masu aiki da suka gama abincin safe suke kokarin ɗora na rana. A cikin ɗakin da suke zaune an ɗage labulayen tagogin dakin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73