Chapter 24
Chapter 24
kanta idan har Ummi ta kira shi da wannan zancen? Ai ko a mummunan mafarki ta san wannan rashin sa'a ce babba a rayuwarta. Ummin ta kalle ta sosai. "Amina auren masu kuɗin nan fa dama ce da kuma rabo, ki saki jikinki ki ci kuɗin gayen nan son ranki, don baki san irinsa ba, ba lallai ne in kin shiga ma ya buɗa miki ba." A yanzu ta dawo Ummin data santa, ƙanwar ƴanmatan Kawu mallam me cike da buri, don haka sai kawai ta faɗaɗa murmushin ta tana fadin. "Toh shikenan." Da haka suka koma wajen su Momi, inda suka dasa hira su da ƙawayensu, hirar da taso tafiya da yawan tunanin zuciyarta, don hira suke har da dariyar da har ƙasa suke kaiwa wajen ƙyaƙyata ta, daga baya ta zubo musu abinci a ƙaton faranti suka zagaye shi su bakwai suka cinye tas, a lokacin su Tanti duk sun tafi kuma har Amma ta yaba da atamfar da suka siyo bayan an nuna mata. Maryam ma ta dawo ita da ƙawayenta da suka tafi gidan wata mata tambayar Beads ɗin da zasu yi amfani dasu a bikin, kuma ganin atamfar murnarta ta ƙaru don tace tayi kalar beads ɗin da ta bayar ayi mata na atamfar da Baba yayi musu na fitar bikin. Kallonta kawai Amina take don ta lura ita mantawa ma take da zancen cewar ba auren da suke so za'ayi ba, don gabadaya ma ta manta da zancen saukarsu da suke ta shiri, yanzu bikin ne a gabanta don ko jiya tana jinta tana takurawa Aminu cewa ya ƙara mata kuɗi zata siyo kayan da zata yiwa ƙawayenta 'takeaway'. "Tun safe Fatee, tun ɗazu nake ta kallon hanya, baku dawo da wuri bane?" Ta faɗa lokacin da Fatima ta shigo gidan da daddare, don tun safe tace mata zasu je bikin ƴaruwarsu. Sai dai maimakon Fatiman tayi dariya kamar yadda ta zata sai kawai tace. "Go slow ne wallahi ya rike mu a wajen Gandu." Da haka ta juya ta gaishe da Amma dake yankewa Hafsa farce anan tsakar gidan sannan a lokaci guda ta jawo hannun Aminan dake jikin durum tana kokarin ɗiɓan ruwa a buta suka yi soro. "Amina dama wanda zaki aura da kika ce min ɗanuwanku ne shine wani Ma'aruf Bakori wanda gidansu yake a sharada?" Sai da gaban Amina ya faɗi duk da bata san me zata ce ba, ta gyada kai tana kallonta da fararen idanunta da ake gani tar a cikin rashin hasken soron. "Eh, baki gani a jikin katin? Me ya faru?" "Bikin da muka je a sharada ne Amina, kuma a layin gidansu, ƙanwar amaryar ce take gaya min cewa ta san duka ƴan gidan kuma da gaske bashi da hankali." Sai ta girgiza kanta. "Su Baba fa sun gama duk bincikensu Fatee, har ganin sa ma sunyi, sun ce ciwon ba mai yawa bane, sun ce har aiki yake yi a kamfanin babansa, ba wai bashi da hankali bane gabaɗaya." Fatima ta girgiza kanta. "Amina baki san me tace min bane..." Da sauri ta sunkuyar da kanta sannan ta shiga girgiza shi itama tana faɗin. "Mutane sun iya yaɗa irin wannan jita-jitar Fatee, ba yau aka fara ba, musamman a sha'anin aure..." "Yana da wa sunansa Jamal?" Fatiman ta katse ta, ba shiri ta ɗago ta kalle ta yayin da muryar Baba ta kwanakin baya ke haskawa a cikin kanta, lokacin da Amma ke tambayarsa idan Ma'aruf ƙani ne a wajen wanda suka je bikinsa a shekarun baya. 'A'a, shine dai wanda kuka je auren nasa, ai ya rabu da matar ne daga baya. Wa ɗaya yake dashi sunansa Jamal kuma ya rasu shekaru goma da suka wuce...' "Ya rasu shekaru goma da suka wuce ko?" Muryar Fatiman ta tambaya tana karashewa da tunaninta. "Me ta faɗa miki?" Bata san lokacin da bakinta yayi tambayar ba yayin da zuciyarta da abinda take tunanin ƙasusuwanta ne suka shiga rawa ba tare da kwakwaran dalili ba. "Shi ya kashe wan nasa Amina! Shi ya kashe Jamal ɗin shekaru goma da suka wuce!" **** "Kar ki ɓata min rai Saratu, don me Allah ya halicce ki a mace? Me zaki yi da ƙwaƙwalwar da ake cewa ko shaiɗan na tsoron kaidin da zaki iya fitarwa ta cikinta?" Muryar Hajiya Kilishi ta faɗa cikin shirun ɗakin yayin da wayarta ke kare a kunne. Ƙawarta da ta kira Saratun tayi ajiyar zuciya a cikin wayar kafin tace. "Baza ki gane bane Kilishi, ba zaki gane yadda nake gaya miki cewa matar nan ta addabe ni ba, shi yasa naje wajen malamin nan, amma gashi yanzun ma kuɗin da na zuba na neman tafiya a banza." Wani murmushi ya suɓuce a fuskar Hajiya Kilishin yayin da fuskarta take fayau! Sai dai a cikin murmushin akwai wani ɓari na sirrin mafi yawan nasarorinta. "Tsafi gaskiya ne Saratu, amma gaskiyar da bata ɗorewa, kuma na sha gaya miki babu amfanin mallakar abinda ba zai ɗore ba, har wani ƙato a gefe ya isa ya magance miki matsalar da ke kike cikinta? Sau nawa zan biya miki karatun nan ne? Shekarata talatin a gidan nan kin sani amma babu rana ɗaya da na taba takaws wajen wani malami da sunan taimako. Da yatsa ɗaya nake juya kowa a gidan nan yadda nake so kuma kin san ko ƴanuwana da muke ciki ɗaya su ma basu san wata fuskata bayan wadda Iyalan gidan nan suka sani ba. Shi yasa nake son ki gaya min meye amfanin buɗe miki cikina da nake yi ke da Salamatu? Ba don mu taru akan bigire guda bane? To don me a yanzu zuciya zata ja ki ki kauce?" Tambaya ce, amma Hajiya Saratun bata amsa ba, don ta san halin Kilishin sarai, ranta ne ya ɓaci amma har a cikin ɓacin nata halayyar ta kan yi rinjaye a zuciyarta. Don haka tana jinta tayi ajiyar zuciya a cikin shirun sannan tace. "Yanzu a ina kuka tsaya?" "Yace ita zai mayar can Egypt ɗin Kilishi, ni uwar garke in zauna in kular masa da ƴaƴa." Ta furta hakan tana furzar da wani irin huci da Hajiya Kilishin zata rantse tana jin zafinsa tun daga nan. "Bi shi a hakan, kar ki sake ki nuna ranki ya ɓaci, kiyi kwalliya ki tausasa muryarki, ki gaya masa zaɓin da yayi daidai ne, ya duba ɗawainiyar yaranki ya taimake ki. Sannan ki faɗaɗa murmushin ki a gabanta itama, ki gaya mata ko da ke ya zaɓa ba zaki bishi ba dama. Bayan haka kiyi mata ɗawainiya a lokacin da zai gani, misali, samu yaji da irin su busashshen tattasai kice tunanin amfaninsu kika yi musu, don kwana biyu ne abincin can zai gundure su. Idan kin aikata hakan, ki kira ni sai mu ɗora." "Kina ganin zan iya Kilishi? Ba kowa Allah ya halittawa irin zuciyarki ba fa?" Muryar Saratun ta tambaya ɗauke da rauni da kuma wani irin tuƙuƙin dake cin ranta. Sai ta sake wani guntun murmushin tana miƙewa tsaye kafin tace. "Zuciyar da Allah ya halitta min nazo duniyar nan daban take da wadda nake da ita yanzu Saratu, ni da kaina na sami wannan zuciyar don haka kema ki tashi ki samarwa kanki abinda zai ɗore. Ki kira
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73