Skip to content

Chapter 16

Chapter 16

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

guda biyu iska da hasken rana na shigowa yayin da a lokaci guda kuma filutulun ɗakin suke a kunne haɗe da fankar da aka ware har ƙarshenta. Hajiya Kilishi dake zaune itama cikin nata adon daidai misali ta ajiye wayarta a gefe sannan ta kai hannu ga robar ketchup ɗin dake kan katon farantin da aka zubo musu kayan breakfast akai, ta sake zubawa a farantin dankalin turawan dake hannunta ta sannan tace. "Idan har zaki samo min me zai sa in ƙi sanya hannu Hajiya, kin san ai waje in dai da raɓa da kuma sirri ba na ƙinsa." Hajiya Salamatu ta sake kai kofin shayinta baki tana girgiza kai. "Ai kullum ina gaya miki al'amarinki abun mamaki ne Kilishi, wallahi duk yawona a doron duniya ban taɓa ganin mace irinki ba, yadda ba boka ba malam, kike juya komai da ɗan yatsa guda kuma hankalinki a kwance." Hajiya Kilishin tayi wata guntuwar dariya alamun ta saba da jin hakan daga bakin ƙawar tata. "Mu bar wannan zancen yanzu Salamatu, mu tafi ga abinda yasa na kira ki." Sai da Hajiya Salamatun gyara zamanta a hankali tana ajiye kofin daga durowar gefen gadon, idanunta kaɗai zaka kalla ka san cewar da gasken ta tattara dukkan hakalinta ga abinda Hajiya Kilishin ke ƙoƙarin ɗorawa akan tsohon shirin da suka saba. "Auwalu yana riƙe da ma'aikata har yanzu, sannan wannan auren kamar ya tabbata ne mu ajiye shi a gefe, me kika cigaba da shiryawa daga ƙarshen ƙullin da muka yi wa zaren, me kika tsara?" "Tsari na da yawa Salamatu, farko dole ne in fara sakin manufata tun yanzu akan ita yarinyar, dole ne ta ɓoyayyiyar hanya in ƙara bincike akan zuciyarta ta yadda zan fara ƙawata tunaninta da miƙakkiyar hanyar da zata ƙulle ta a gaba. Na biyu, dole ne a yanzu inyi taku mai nisa daga mahaifin yarinyar da kuma maigidana, zan ƙara zame hannuwa daga al'amarin na in zama ƴar kallo ta yadda ko ƙura ba zata hau kan farina ba, balle wani ɗigo na baƙi, amma zan kusanci mahaifiyar yarinyar dole, don haka ne ingantacciyar hanyar da kowa zai kalla a yanzu. Sannan na san Ishaq zai shaida min dukkan sabon tsarin magungunan Ma'aruf, don haka wannan ma babu matsala, komai zai cigaba ne daga inda ya tsaya. Game da auren su Salma kuma wannan komai tsaftatacce ne don kin san bana taɓa haɗa ƙasa da gari waje guda. Daga Auwalu kuma, mun sake bude wani sabon account zai loda kudaden wancan watan..." Ta faɗi hakan sannan tayi shiru a hankali, ramin bakinta na wasa da wani murmushi mai armashi. "A yadda lissafin komai yake Salamatu, shekara guda tayi yawa kafin komai ya ɓare!" Hajiya Salamatun tayi nata murmushin itama yayin da take kallon fuskarta. "Na fahimta Kilishi nima na lissafa wannan adadin tun a wancan karon. Sai dai kin san a kullum nice mai hasko miki ƙalubalen da ke bakya ƙirgawa dasu. Ƙalubalen da duk zare ɗaya ne ya ƙulle su suke reto a jikinsa, ƙalubalen kuma da shine raunin ki Kilishi, shi kadai ne raunin da na san ubangijin ya halitta a ƙirjinki, Ma'aruf!" Murmushin da kullum ke sauka a fuskarta duk sanda Hajiya Salamatun ta furta mata magana makamanciyar wannan shi tayi a yanzun ma, tayi shi tana ajiye farantin hannunta, ta jawo tissue a gefe ta goge maiƙon hannunta sannan ta miƙe, ta isa ga makekiyar wardrobe ɗin dake ɗakin ta buɗe waje na biyu, a ciki kayan Ma'aruf ne wanda ya cire daga jikinsa ranar da aka tafi dashi tafi London ba'a hayyacinsa ba. A gaban kayan akwai dukkan tarkacen dake cikin aljihunsa a wannan ranar, muƙullin mota, chewing gum, chapet, biruka da kuma wallet ɗinsa, wallet ɗin ta dauko sannan ta rufe wardrobe ɗin ta dawo gaban Hajiya Salamatu ta miƙo mata ita. Sanin halinta sarai yasa Hajiya Salamatun ta karɓa ba tare da ta tambaya ba, ta ware cikinta, kuma bayan tudun kuɗin da taji a ciki da kuma jerin credit cards, wani hoto da aka maƙala a jiki shi ya ɗauki hankalinta, samari biyu ne a jikin hoton wanda kallo ɗaya kawai zai shaida maka cewar wa da ƙani ne, don bayan girman da ɗaya yafi ɗaya, akwai kammani sosai a fuskarsu. Suna dariya mai cike da nishaɗi yayin da babban ke miƙo hannunsa kamar zai naushi ƙaramin. Ƙaramin Ma'aruf ne Hajiya Salamatu ta sani, babban kuma... "Jamal..." Sassanyar muryar Hajiya Kilishi ta furta tare da tunanin Hajiya Salamatun. "Jamal shine ƙalubale na kuma shine rauni na Salamatu, shi yasa na rufe idanuna nayi abinda ya kamata akansa, don haka kamar kullum zan gaya miki cewa ki yarda bani da wata matsala a duniyar nan yanzu idan ba kuma ƙaddarar ubangiji ba. " Ta fadi hakan yayin da take tsaye akanta, Hajiya Salamatun ta ɗago ta kalle ta, wannan murmushin na baya ya tafi, idanunta sun canja ta yadda ko ɗigon raha babu a cikinsu. "Kar ki ƙara lissafa Ma'aruf a cikin ƙalubale na Salamatu, don kinfi kowa sanin matsayinsa a waje na." Kuma a cikin idanuwan nata, Hajiya Salamatun ta shiga hango abubuwan da suka faru wasu tarin shekaru da suka wuce! ****** 11:20 Am "Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Wai baka da imani ne Ishaq? Tun da na tashi kake ta masifa a gidan nan kana mita, nace maka wallahi ko ganin yarinyar banyi ba balle inyi mata wani abu, do I have to bury myself before you believe?" (haƙa kabari zanyi in shiga kafin ka yarda dani?) Ma'aruf ya fada a lokacin da yake zaune kan dining table din falon gidansu, inda ya samu ya ture wasu litattafai da kuma kayan wankin Ishaq ya dora plate ɗin abincin da yake ci. Ishaq na tsaye daga cikin falon shima rike da nasa kofin shayin da kuma remote ɗin da yake kokarin chanja channel daga ta labaran da Ma'aruf ya kai. "Ka gayawa wani ba ni ba, na san halinka sarai B, hankalinka ba zai taba kwanciya haka ba idan har ba kayi abinda kake so ba. I'm just advising you (shawara nake baka) komai zai iya faruwa idan har maganar nan ta lalace kuma Baffa ya san da saka hannunka." Ma'aruf yayi murmushi a hankali sanda yake jin zafin faten dankalin dake sauka cikin maƙogwaronsa wanda motsawar Adam's apple ɗinsa kadai zai shaida maka hakan. "Wai ina zaka je ne ma? Yau asabar fa?" Ya canja akalar zancen nasu ba tare da ya kalle Ishaq ɗin ba, don tun da farko kayan jikinsa sun riga sun nuna masa cewa Office zai je. Babu adadi na lokutan da zuciyar Ma'aruf ke motsawa a duk lokacin da yaga Ishaq na yin wani abu da ya danganci aikinsa, aikin da yake so kuma abinda shine mafarkinsa ya fito dashi zahiri kuma yake yi ɗin. Shi nasa burin da kuma mafarkin sun dade da kaɗewa shekaru goma da suka wuce. Abinda yake yi a yanzu, ba rayuwarsa bace ko kaɗan, wata rayuwa ce da ta zama dole ya ƙarasawa mai ita. "Thanks to you, nayi missing tarin ayyukan da dole inje in san halin da ake ciki kafin Monday, Idan ciwon ka ya sake tashi Ma'aruf wallahi ka nemi mai raka ka asibiti." Murmushi Ma'aruf keyi har a lokacin yana cigaba

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73