Chapter 2
Chapter 2
yaya zai iya wata dawainiya yanzu, in dai sallah tazo ai yana min kaya kin sani." Fatima ta tabe baki. "Wannan fa daban, kyauta kuma daban. Ni wallahi Amina na sha gaya miki ki ƙyale Abdallah nan, da tuni kin fara ganin wadanda suka fishi, don naga alama yanzu idanunki basa ganin kowa." Sai a lokacin Amina ta kalle ta. "Fatee, ke fa kin san ni duk wannan abin ma ba a gabana yake ba, shi yasa nake son mu'amala ta da Abdallah saboda shima yanzu karatunsa yake son gamawa, baya takura min nima kuma bana takura masa." "Wai har yanzu kina ganin zaki cigaba da karatun ne?" Ta daga kanta. "Wallahi ban fidda rai ba Fatee, duk da na san Baba ba zai iya ba, kuma babu wanda zai yi min bayan shi din.' "Shi yasa nake gaya miki ki hakura kawai, ba komai mutum yake samu a rayuwa ba, a yanzu auren kawai ya kamata kiyi, ki ragewa su Baba nauyi sannan kema ki sami wajen da zaki iya ɗaukar ɗawainiyar wasu ma." Kallonta kawai Amina take tana murmushi don ta riga ta sani cewa ba zata taba fahimtar abinda take ji a zuciyarta bane, sai da ta kai ƙarshe sannan ta shiga haɗa kayan tanafaɗin. "To shikenan, ki bari sai bayan maulidi, idan mun fara kai ki, sai in fara wannan lissafin. Jin haka yasa ba shiri itama tayi murmushi tana kara juya idanunta, don kamar yadda aka tsayar da rana, bayan maulidin ne bikinta ita da Ahmad din. "Baki san wani abu ba ma, wata mata na samu mai sayar da magunguna a can layin..." Da haka ta shiga bawa Amina labarin da yasa ta bar hada kayan ta zare idanu tana kallonta kafin ta shiga ɗaka mata duka alamun bata son zancen, ita kuma tana kyalkyala dariya. Mahaifin Amina mai suna Alhaji Sulaiman dattijon mutum ne mai sana'ar harkar aikin katako, ya samu wadata a da, don gidan da yake zaune da iyalansa na kansa ne, amma a yanzu abubuwa sun tsaya masa ta yadda ya ɗauki hakan ya sanya a ransa har ya zama shine damuwarsa a kodayaushe. Ƴaƴan sa biyar tare da matarsa Halimatus- Sadiya bafulatanar Niger da iyayenta suka dawo Nigeria da zama. Amina ce ta farko, sai Aminu, Maryam, Adam da kuma autarsu Hafsa. Maryam, Aminu, da Adam suna matakin secondary ne a karatu yayin da Hafsa kadai take Primary, amma da yake makarantar da suke zuwa wata community school ce dake waje ɗaya, tare suke tafiya dukkaninsu tare suke dawowa. Babban damuwar Alhaji Sulaiman a yanzu shine ganin ƴaƴan sa na ƙara tasawa kuma harkar samun sa na ƙara yin baya, karayar arziƙin da ya samu ta taimaka ƙwarai wajen karya zuciyarsa akan komai, kullum cikin lissafi yake da kuma damuwar da ƙarara kowa ke gane ta duk da irin nuni da kuma nasihar da matarsa ke yi masa a kullum. *** Ƙarfe Biyu da rabi. "Yaya dan girman Allah zaki bani naira dari? Ƙunshi zanyi." Maryam ta fada lokacin da take ƙoƙarin cire uniform ɗin ta bayan sun dawo daga makaranta. Amina na zaune tana ninke kayan wankinta tace. "Ƙunshin me zaki yi?" "Bikin yayarsu Na'imah fa, kin manta jiya nazo da katin." Jin tayi shiru yasa ta sake tambaya. "Zan baki Maryam, Allah ya kaimu gobe." "Me za'a bayar? Idan ana ƙaunar Allah nima a taimaka mun." Aminu ya fada yana shigowa cikin ɗakin. "Kaima ƙunshin zaka yi?" "Me kyau ma kuwa, don kin san sai yafi fitowa a hannu na ma akan bakar fatarta." Ya fadi hakan sanin cewar shi fari ne, don ƴan mazan biyu su suka yiwo mahaifinsu sak a kammani da kuma hasken fatan, matan kuma Suka yo mahaifiyarsu, har gwara Maryam ma ana cewa idonta irin na babansu ne, amma Amina da Hafsa babu abinda suka bari a kammanin Amman. "Wallahi ni ba baƙa bace kaima ka sani, irin wannan kalar fatar sai ka zagaye garin nan kaf baka samu irinta ba." "To idan ma an samu me za'ayi da ita? Da dai irin ta Amina kika ce sai in yarda, amma ke duk gidan nan ma akwai mummuna kamar ki." Maryam ta kara haɗe ranta tana saka hijabin data ɗauko. Amina ta jefo masa wata riga dake hannunta tana murmushi. "Haɗa mu kayi kawai kake zagi Aminu, dani da ita ɗin me ya banbanta damu, ka takurawa Maryam wallahi." "Haba ya zaki hada kalar ki data wannan fingilar? itama ta hakura ta karɓi kanta yadda take ne taƙi, sai faman iyayi fal ciki." Da ƙunƙuni Maryam ta faɗi wani abun kafin ta tayar da sallarta. Hakan yasa shi dariya don shi kansa ya sani girman dake tsakaninsu ne kawai yasa take raga masa a azababbiyar magana da kuma rashin kunyar dake cikinta. "Sai yaushe zaka fita yau?" Amina ta tambaya sanin cewar da ya dawo baya dadewa a gidan yake tafiya can inda yake koyon gyaran mota a can hanyar gidan zoo, har ma ya fara kwarewa don kusan shekara biyu kenan da Baba ya kai shi wajen. "Sai na ƙarbowa Baba, kayansa daga wajen guga..." Ya shafo kansa. "... Tun dazu ma fa ya kamata in je, sun ce sun gama." Kafin Amina tayi magana, Hafsa ƙaramar ƙanwarsu ta shigo gidan hannunta riƙe da ƙullin farar ledar atturuhun data siyo na girkin dare da kuma takardar yashin madina tana zubawa a ɗaya hannunta tana lashewa. Amina ta ɗaga murya ta kirata ganin bata da alamun shigowa. "Ki shigo ki cire kayan nan ki saka na islamiyya, ga uku nan har ta kusa, Adam har ya tafi kina nan." Tana jin hakan Idanunta irin na Amina suka kaɗa a take sannan muryarta ta koma ta kuka, ta shigo ɗakin da sauri tana faɗin. "Dan Allah kice Ya Maryam ta raka ni, wallahi zane ni za'ayi..." Kafin Aminan ta amsa, Aminu yace. "Saka kayan muje in raja ki daga nan sai in wuce. Ai kuwa da murnarta ta ruga da gudu zuwa dakin Amma inda kayanta suke, ta sani ba wanda ya isa ya dake ta makarantar tunda Aminu ne zai raka ta. Aminu ya ciro Naira dari biyu daga aljihunsa ya cilla kan sallayar da Maryam ke sallah yana faɗin. "Gashi nan kije a zana miki abinda ba ganinsa za'ayi ba." Amina tayi murmushi tana godewa Allah a zuciyarta, tana son yadda suke tallafar junansu akan irin ƙananun buƙatun nan. Hafsa bata dawo ba suka tsinci sallamar mahaifinsu, dukkaninsu suka kalli juna a lokaci guda sanin cewa lokacin ba lokacin dawowarsa bane, ƙa'ida ne sai bayan sallar magriba kullum yake dawowa don har Aminu yana yawan riga shi isowa ma. "Allah yasa kar ya tambayi kayan nan..." Aminu ya faɗa yana dafa kansa. Ta tsakanin raga-raga labulen Amina ta hango yadda mahaifin nasu ya dafa kan Hafsa da ta taho ta rungume shi, sannan kai tsaye ya nufi hanyar ɗakinsa. Taga Amma ta fito daga falo sanye da hijabi alamun salla tayi ta bin bayansa tana fadin sannu da dawowa. "Ke maza ki dauko takalminki mu fita." Cewar Aminun, sannan ya juyo ya kalli Amina. "Kice masa tun dazu na tafi karɓi kayan." Ai kuwa yana sanya kafarsa waje suka ji Baban yace. "Fita ce ta kama ni Halima, ina kayan da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73