Skip to content

Chapter 42

Chapter 42

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

safe shi yasa na riƙo shi kar ta zube." Wannan karon Amina ta tabbata mamakin da take ciki ta kai ta har wuya tana shirin nutsewa. "Kar ki wani damu idan yarinyar nan ce ina jin sai kin dinga korarta daga gidan nan akan abinci..." Kafin Munayan ta karasa fada wayarta tayi kara. Sai ta miƙe tana cewa... "Ya Shukra ce, kuzo mu tafi kafin ta fara mitar nan tata." Surayya ta mike kuma ga mamakin Amina sai suka zo suka sake rungume ta daya bayan daya suna gaya mata cewa in suka dawo zasu shigo sai suje cikin tare ta gaida su Mami. Itama ta rako su har kofa tana fadin su gaishe su. Bayan sun fita, ta tsaya daga barandar falon tana kallon compound din gudan da yasha wasu interlocks masu ƙyalli, da kuma shukokin wasu kananan bishiyu a jikin katangar da basu fara girma sosai ba. Ji tayi zuciyarta ta washe da wani abu da baza ta iya fassara shi ba, mamaki na yawo akanta har yanzu na yadda abubuwa ke canjawa daga zaton ta, kirkinsu yasa taji sun burge ta sosai yadda basu ɗauki kansu wani abu ba, taji zuciyarta na dokin ta saba dasu fiye da haka, kafin ta juyo ta dawo tana rufe kofar ɗakin, idonta ya kai kan tarin flasks din nan tana tunanin yadda zata yi da abincin, ko da yake ba ita kaɗai suka kawowa ba har dashi ta sani. Zuciyarta ta buga da ta tuno cewar zai sake dawowa gidan ya same ta, ta tuno kallon da yayi mata har da murmushi da yadda taji a lokacin tana kasa tantance tsoro ne ko akasin sa... Ashe dukkan abubuwan da take hangowa da sauki sun sha banban da tunaninta... Kwankwasa kofar da akayi ya katse tunaninta, ta tafi da sauri ta bude tana fatan su Maryam din da take jira ne, su din kuwa... Har da Hafsa dasu Mimi da Fatima da wasu daga cikin ƴaƴan Baban kurna, su takwas, sun riko wasu sauran tarkacenta da tsintsiyoyin nan... Ranta ya karasa yin fari ƙal ta hau rungume su daya bayan daya tana murna, rungume sun da bata san tayi ba sai da taji Fatima na cewa. "A ina kika koyo wannan sabuwar gaisuwar kuma?" Ita kaɗai ta cije lebbenta tana murmushi. ** A cikin ɗakin Hajiya Kilishi, ta kalli kawarta Salamatu tana girgiza kai. "Banbanci na dake kenan, bana faɗuwa na hakura, a sannu nake bin abu ina gutsira har in kai ga ci, kuma nasha gaya miki hakurin da kika kasa a tare da Shamsu (mijinta) kenan. Shi yasa har rayuwa ta kawo ki wannan gaɓar." Hajiya Salamatun ta girgiza kanta itama. "Gaɓar da nake cin duniya ta da tsinke ba, kar ki kawo wannan zancen kuma bayan mun gama na Saratu, mu tattauna abinda ya kawo ni, Ya zaki yi da al'amarin ƴar tasa?" Hajiya kilishi ta kalle ta sosai tace. "Na gaya miki ai, saboda ban samu nasara akanta a asibitin nan ba hakan baya nufin na hakura, ai na rantse sai naga bayanta don ko wajen uw*rta ba zan bari ta koma ba tunda har zata fara zame min ƙalubale tun daga yanzu. Babu wanda ya isa ya shiga zuciyar Ma'aruf da tasirin da yafi nawa Salamatu kema kin sani. Saboda haka matsalolin nawa zan hade guri guda, bayan tsinannun asibitin nan da suka hana ni kwana a wajenta sun sallame ta, wani Creche wai ya kaita a hanyar Bompai saboda kin san muna cikin sha'anin bikin nan. Saboda haka a yanzu da komai ya lafa zan saka ne ya dawo da yarinyar wajen ita Aminar, ta yadda zan aiwatar da manufata hankali a kwance. Kin san dai dalilin da yasa na shiga na fita ya auri yarinyar nan, saboda daga ita har iyayenta zan iya juya su sannan an tabbatar min tana da sanyi halin da al'ummar gidan nan kaf zasu karbe ta cikin ƙankanin lokaci, na gaya miki tana da irin fuskata Salamatu, fuskar da zata daɗe tana yin abun da ba mai iya ɗora zarginsa akanta." Hajiya Salamatu ta kalle ta tsawon wasu sakanni tana nazarin maganganunta kafin ta girgiza kanta tace. "Kin san nice mai gano miki da matsalar dake ba kya taba hangenta Kilishi, jiya da suka kawo yarinyar nan banga fuskarta ba, amma daga yanayin jikinta kawai na san ƙarama ce, kuma idan har halinta ne zai sa jama'ar gidan nan su sota, ba kya tunanin zuciyar yaron ma zata iya ta karkata kanta?" Hajiya Kilishi ta gyaɗa kai tana murmushi. "Daɗina dake ragon azanci Salamatu, ai dama haka nake so, in ba haka ba don me nake ta koɗa ta da ƴanuwanta a wajensa, so nake ta siye min zuciyar kowa har shi ɗin kamar yadda nima nayi, ta yadda a nutse zan sa ta dinga kai min saƙona kowacce kusurwa babu mai zarginta." Hajiya Salamatu ta sake girgiza kanta. "Baki gane ba Kilishi, abinda nake nufi shine idan har ta siye zuciyar Ma'aruf da darajar da zata fi taki nauyi fa? Idan har yayi nisa a duniyarta ta yadda ba zai iya jiyo ko da muryarki ba fa?" Wannan karon dariyar da Kilishi tayi sai da ta ratsa kowanne bango a dakin ta kuma fita ta windon ɗakin da yake a rufe, tabi iska zuwa nisan da ƙarfin amonta zai iya kaiwa, hatta jikinta sai da ya girgiza saboda nauyin dariyar, kafin ta kalle ta sosai tace. "Ita kanta yarinyar ai na shirya mata Salamatu, sau nawa zan gaya miki ne Ma'aruf nawa ne ni kadai?!" *** Tafiyar ta fara! Insha Allah. #Aysha shafi'ee. #fikrawriters #FararWuta. BABI NA GOMA. Ina mai baku hakuri, an samu jinkirin wannan babin ne saboda rasuwa da aka yi min ba a gari ba don haka har tafiya sai da ta kama ni zuwa can... Ina rokon ku taya ni addu'ar Allah ya jikanta ya gafarta mata. Sannan duk a cikin kwanakin nan mun rasa Abdallah ma, ɗan gidan Sanah S. Matazu editar Fikra, ina rokon Allah ubangiji ya bata hakurin rashinbsa yasa mataryin can ne, sannan ina yiwa duk wanda ya rasa wani nasa ma addu'a, mutuwa na taɓa mu a bangarorin da bamu san muna dasu ba, Allah yaji ƙan wadanda muka rasa mu kuma ya kyautata namu zuwan. Ameen ya Allah. ~~~~~~~ We should talk. - Unknown ** "Maamah don me yasa zai kira shi? Nace ya kira shi ne? Me yasa zai yi deciding abinda bai shafe shi ba kai tsaye?" Muryar Ruƙayya ta fito da ƙarfi a lokacin da take kallon ƙaninta Ahmad dake tsaye a gaban gadon da take kwance. A cikin asibitin da aka kwantar da ita ne, tun bayan lokacin data faɗi take asibitin ba'a sallame ta ba sakamakon hawan da jininta ke tayi babu sauka, don hatta fuskarta da kafafunta dukkansu a kumbure suke suntum. "To hell with you and him! Shi waye da baza'a kira shi a gaya masa yayi ba daidai ba? Me yasa akan Ma'aruf ƙwaƙwalwar ki ba zata taba hankali bane Rukayya? Meye a duniyar nan ki gani a jikinsa da sauran maza badu dashi? I swear to God idan kika kara daga min murya a yanzu zan sake kiranshi na zage shi a gaban idanunki." "Maamah kina jinsa ko? Kina

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73