Chapter 63
Chapter 63
bata yi tunanin zuciyar tata zata yi ba a yanzu tare da abinda ya faru game da ita. A hankali ta juya ta koma ɗaki, wani pink dankwali ta ɗauko ta daura, ai kuwa ya hau sosai da kayan ya ƙara haska fuskarta, wanda bata ko gani ba ta sake ɗaukan ƴar ƙaramar jakarta da kuma wannan basket din ta fito, sai da ta tabbata ta kashe fitulu da switches ɗin ko'ina, na fridge kawai ta bari sannan ta fito. Yana tsaye daga bakin barandar falon yana jiranta, wani guntun murmushi da yayi mata yasa gumi fitowa a tsakanin yatsunta kafin ta bashi waje ya kulle ƙofar gidan, kuma juyowar da yayi yasa shi tsayawa dab da ita, wanda kafin tayi tunanin yin gaba idonta ya hango mata wasu manyan ledoji akan booth ɗin motarsa. "Mami ce ta aiko a kawo miki, yanzu muka yi waya tace ki kai musu." Muryarsa ta faɗa dab da bayanta. Zuciyarta ta buga a ƙirjinta, hannayenta suka fara rawa riƙe da kayan nan, ta sani bana tasirin muryarsa ne kaɗai bane har da na sunan Hajiyan Kilishin daya furta. Numfashinta ya shiga kakkatsewa a kirjinta ta yadda tayi tunanin zai iya jinta amma sai taji lokacin da yayi baya ya ɗauki waya yana cewa. "Zuwa 10 zasu iso Faruk, idan kana ƙaunar Allah ka tabbata kana nan..." Sai kawai tayi ƙarfin halin motsa kafafunta ta tafi wajen motar, ta isa wajen daidai lokacin da idonta ya nuna mata sauran kayan daga gefen motar, buhun shinkafa guda biyu da jarkokin mai suma guda biyu. Ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta kafin ta ajiye kayan hannunta, ta buɗe ledar farko inda kayan tea manya-manya gwangwanayen su Madara ya shiga idonta, a ɗaya ledar kuna wani ƙaton food flask ne shi kadai mai faɗi, taji har a lokacin hannunta na girgizawa a hankali sanda ta buɗe shi, kuma tun kafin ta gani ƙamshin wani farfesun naman kaza ya cika hancinta, shine fal ya kusan cika flask din har baki. Ba shiri ta rufe idanunta tana jin koina a jikinta na girgizawa. Fata take da dukkan imaninta cewa Allah ya kawo mata mafita akan matar nan. "Ya ubangiji kaine tanadin kowanne bawa idan ya fada masifa, Ya Allah na miƙo maka hannaye na ka taimake ni akan wannan al'amarin da yafi ƙarfina, ba zan iya ba ya rabbi! Bani da wata mafita da wata dabara wadda ta wuce taka ya Allah." Wani lokacin bawa yana yin addu'a ne akan gaɓa, wani lokacin ubangiji yana amsa addu'a ne a take! Kuma komai yana da tushe yana da asali, kamar yadda tafiyarsu Jigawa ke shirin zama tushen faruwar abubuwa masu yawa. Kuma rashin sani yana ɗaya daga cikin raunin ɗan Adam! *** Waye yake cikin wannan rashin sanin ne? A cikin dukkan wannan hargitsin, me yake jiran mu a jigawa ne?😉 Wace mafita Amina zata samu game da Hajiya Kilishi kafin zagayowar sati guda? A yau kun fara jin tarihin Hajiya Kilishi!😰 Ku shiryawa abinda ke faruwa daga ɓangaren Ruƙayya. Har da Jawad ma.😅 #Aysha shafi'ee. #fikrawriters #FararWuta. BABI NA SHA HUDU. ~~~~~~ I fall in love with your kindness, because it adds peace to my wounded but striving soul. - Unknown. *** Ruƙayya na tsaye daga jikin windon, hannunta rike da kofin wani shayi dake tiriri, idanunta na manne akan shukokin harabar gidan nasu dake waje, kamar nazarinsu take tana son gano wani abu a jikinsu, amma a zahiri kalaman aminiyar mahaifiyarta da ake kira da Hajiyar Sudan wadda ke magana a baya ne suka shiga kunnenta. " ... Da mun tura wanda za'a samu ya kwance abin nan ke kin sani Nafi, yadda na ake da tabbacin na kabari baya dawowa haka aiki na yake ci..." Sai kawai ta juyo a hankali tana kallon Hajiyar Sudan ɗin kafin kai tsaye ta katse ta. "Ban gane ba, ta yaya zamu iya kai abin har cikin gidan?" "Yanzu duk bayanin da muke yi baki ji komai ba? Tunanin me kike yi bayan wannan?" Cewar Mahaifiyarta Hajiya Nafisa, amma ga Hajiyar Sudan ɗin wani shu'umin murmushi tayi tana kallonta sannan tace. "Ƙyale ta Nafi, yanzu zata fahimce ni tsaf." Ta fada ba tare da ta ɗauke idonta daga kan Rukayyan da itama ke kallonta ba, kuma da hannunta na hagu ta yi mata inkiya da alamun ta ƙaraso ta zauna a gefenta. Rukayya ta kalli wajen, ta sake kallon fuskarta... Allah ya sani bata son matar sam, don ta daɗe tana zargin itace ta bawa mahaifiyarta shawarar data fito da ita daga gidan Ma'aruf, sai a yanzu da suka ga da gaske babu yadda zasu yi da ita akansa sannan suka hakura, ko kuma tace mahaifiyarta ta hakura don har yanzu bata gama yarda da ita Hajiyar Sudan ɗin ba sam, amma sanin cewar bata da wata hanyar da ta wuce tata yasa ta cije lebbenta kawai sannan ta ƙarasa ta zauna ba tare da kallonta ba. Kuma kai tsaye sai ta fara bayani daga inda ta san zata fahimta. "Yanzu mun aika masa da takardar sammaci, ba nufinmu a shiga shari'a ba kamar yadda nayi miki bayani, a iya gaban alkali za'a sulhunta komai a tsakaninku kin san duk abinda zaki faɗa da kuma shaidun da muka samu wanda zasu saka komai ya tagi daidai, don haka daga nan za'a baki ƴarki ki taho gida da ita. Kwana ɗaya kawai a tsakani, zaki haɗa kayanta wanda a ciki zamu san yadda za'a dinke ƙullin nan a cikin jakar yadda babu wanda zai tiya gani, sai ki kirashi wani waje inda zaku haɗu ki kalallame shi da zancen wannan yarjejeniyar taku, ki karbi kuskurenki da komai ki kuma bashi yarinyar da cewar kin yarda ta koma hannunsa kamar yadda kuka shar'anta, ki gaya masa cewa bayan wani lokaci ya dinga kawo miki ita kina ganinta. Da wannan zamu barta a wajenta tsawon sati guda inda a sannan ne za'a sami wadda zata je gidan da sunan ta kawo sauran kayanta, a wannan lokacin za'a sami dabarar da zata kwance ƙullin nan, wanda da anyi hakan Ruƙayya, shikenan sai ki cigaba da kurbar shayinki kina kallon abinda zai biyo baya." Ta ƙarashe zancen da wani faffaɗan murmushin da ya sassauta zuciyar Rukayyan a lokacin, don sosai yasa ta jin cewar kamar da gaske sunyi nasarar sun gama, tayi niyyar magana amma sai mahaifiyarta ta riga ta. "Idan komai ya tafi daidai, sai ke kuma ki bar hakarƙarin mu ya huta haka kije can ki ƙarata." "Ai babu abinda zai kuskure ma, na gaya miki idan kinga an samu saɓani a wannan abin Nafi, to gawar da aka binne zata fito ta dawo duniya, don haka ku kwantar da hankalinku kawai." Wannan zancen yasa su yin dariya dukkaninsu kafin hankalin Ruƙayya ta juya ga wayarta da ta shiga ƙara daga can inda ta baro ta a jikin windon data tsaya. Ta mike a hankali riƙe da kofinta ta koma wajen, sunan Jawad daya nuna akan screen din wayar yasa ta kurɓar shayin kafin ta ɗauki wayar ta kara ta a kunnenta. "Barbie yau kika ce, 5pm." Me yasa zai tuna mata? Ta sani, ta sani cewa shekaranjiya ta gaji da nacinsa da ba zai kare ba tace masa zasu hadu a yau, kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73