Skip to content

Chapter 19

Chapter 19

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

gidan wata ƴaruwarta a Goron dutse ta shaida mata al'amarin. "Ina yarinyar nan take?" Ta san Maryam yake nema don haka tace. "Ta tafi makaranta tun ɗazu." Sai ya ajiye flask ɗin a ƙofar kitchen sannan ya ƙaraso ya tsugunna a kusa da ita, muryarsa ɗauke da nutsuwar da zaka shafe rabin rayuwarka kafin kaji ta a wajen Aminu yace. "Hukuncin da kika yanke yayi daidai Amina, ba don Amma ba daidai ta faɗa ba, sai don kare mutuncin Baba da kika yi, kuma na tabbata Allah zai duba hakan ya kyautata rayuwarki." Kwalla ta taru a idonta lokaci guda, don haka ta gyada kai kawai ba tare da tace komai ba. Wucewar wasu ƴan sakanni shima yana tsugunee kamar yana sake biya abinda ya fada a zuciyarsa, sai kuma yayi gyaran murya sannan ya koma Aminun da yake. "Kin gayawa Malam ne?" Ta san Abdallah yake nufi don dama haka yake kiransa, saboda haka ya girgiza kanta tace. "Na san dai zai zo anjima." "Kice yau Malam zai danɗani baƙin cikin latecomer kenan." Bata san lokacin da ta watso masa ruwan wanke-wanken ba tana jin wani abu a zuciyarta na fadawa, ya kauce shima yana dariya sannan yayi hanyar fita yana faɗin. "Idan wannan ƙwalamammiyar ta dawo kice mata ga wainar masar da take ƙalata nan na samo mata." Bayan ta gama wake-wanken ta koma ɗakinsu har a lokacin ƴan islamiyar basu dawo ba balle kuma Amma, a ƙasan kayanta ta sake ɗauko wannan takardar tana karantawa, idanta suka tsaya akan sunan yayin da a yanzu bayan tsoron ma'anar rubutu wani sabon tsoro daban ke shigarta. Ma'aruf B. Ta karanta sunan tana jin yadda tsoron harafan kadai ke zanuwa a zuciyarta, ba wai don ta sanshi ta gane waye ba sai don zuciyarta bata cika manta fuskokin mutane ba koda kuwa sau ɗaya ta taba arba dasu, kamar dai shi rana guda ta taɓa ganinsa a rayuwarta kuma bata ƙara ba daga sannan. Ranar ɗaurin aurensa, ranar da Baba yasa suka tafi tunda sassafe ita da Amma don wai suyi yinin bikin da gaske kamar yadda aka rubuta, a lokacin da ya shigo gidan shi da abokansa da ƴanuwansa bayan ɗaurin auren, ita da Amman suna rakuɓe daga can jikin wata kujerar a falon Hajiya Kilishin, kuma duk da tarin ƴan bikin mata da suka yanyame shi da tsokanar 'ango kasha ƙamshi...' sai da idanunta suka iya hango mata shi yasha farar shaddar dake ƙyalli kamar murmushinsa, yana tsaye daga tsakiyar mutane yayin da masu hoto ke ta yi musu kala-kala. A wannan lokacin gani take kamar bambancin su ita da Amma da mutanen gidan ya zarta na mutum-mutum, don bayan Hajiya Kilishin da ta amsa gaisuwar su cike da fara'a ta kuma sa aka kawo musu abinci babu wanda ya ƙara lura dasu a gidan, sai wata mace guda ɗaya da tace Amma ta ara mata hijabinta lokacin sallar azahar, itama da alama irinsu ce don ta ɗebo tarin ƴaƴan da ta cika musu faranti taf da abinci suna ta ci. Daga baya ma dole suka bar cikin falon suka zagaya baya can wajen ɗakunan masu aiki, inda anan ne suka ɗan sake har Amma ma taga wata ƴar ajinsu ta sakandire a ƴaƴan dattijan da sune manya-manyan masu aikin gidan. Don haka kwatanta tsoron cewar a wannan karon ita zata maye gurbin wannan kyakkyawar amaryar da aka shigo da ita gidan wajen yamma abu ne da ta tabbata babu wanda zai iya kwatanta shi a duniyar nan. Tsaya ma tukunna... Ina matar tasa take?? ***** "Baffa ya gaya maka komai ko?" Hajiya Kilishi ta tambaya tana kallon Ma'aruf ɗin dake zaune a gabanta, a cikin falon ɓangarenta suke su biyu sai Surayya dake can wajen dining tana danne-danne a wayarta, yana zaune a kujerar dake kallon Tv yana kokarin canja channel daga ta india zuwa wata channel da ya san a lokacin ana wani Tv show na likitoci mai suna 'Code Black'. Sai da ya kai tashar ya karo volume sannan hankalinsa a kwance ba kamar yadda ta zata ba ya juyo ya kalle ta. "Ya gaya min, and I was surprised har dake Mami." Tayi murmushi tana kallonsa daɗi na cika kowanne lungu da saƙo na zuciyarta na ganinsa a gabanta, zata rantse da alƙur'ani ko ya'yan da suka fito daga cikinta basa ƙarasawa inda Ma'aruf ke kaiwa a zuciyarta, matsalar ɗaya ce kawai... duk wani ado da zai ƙawata kusancinsu dole ana kaiwa gabar da za'a yaye cewar shi ba mallakinta bane, kuma tana jin cewa da zata iya samun mai gyara mata hakan babu makawa zata bada komai na duniyarta don kawai a wayi gari duniya ta shaida cewa shi nata ne. "Baffa ya riga ya gama yanke hukuncinsa shi da Alhaji Baba, daga ƙarshe kawai suka tuntubeni Mai gaskiya kuma ka san ba zan iya cewa Baffa A'a ba, shi yasa sai na bada tawa gudunmawar ta hanyar zaɓo maka yarinyar da na san zata dace da yanayinka. Wannan ba irin ba irin Ruƙayya bace Ma'aruf, don nayi Imani yarinyar nan zata baka kulawar da kake buƙata." Wani murmushi yayi kaɗan sannan yace. "Na dade ina gaya miki kulawarki kaɗai ta ishe ni in rayu Mami, tunda har Rukayya ta kasa bana tunanin akwai wadda zata iya jurewa mess ɗina a duniyar nan kuma." Maganganun suka taɓo wani abu a can ƙasan zuciyar Hajiya Kilishi, wani abu da sai da ta ji shi har a ƙarƙashin tafin ƙafarta musamman yadda muryarsa ta fito da wannan amon mai zurfi da kuma sanyi. Kuma sai da ta maida wata ƙaramar ƙwalla a idanunta sannan tace. "Yanzu dai ka san baza'a fasa ba ko? Don haka zamu fara shirye-shirye, za'a kai musu lefe dole sannan idan kana so ma zaka iya zuwa ka ganta." Maimakon ya bata amsa, sai kawai ya juyo ya kalle ta, lumsassun idanunsa suka tsaya a nata. "Wai zaman me Ishaq yake yi ne ma? Me yasa Baffa baice a haɗa dashi ba?" "Sai gida ya koshi ake kallon na waje Ma'aruf, kaine damuwar mu a yanzu ba shi ba." Kamar bai ji dadin maganar ba, don juyawa yayi yana cigaba da kallonsa ba tare da yace komai ba. Hakan yasa tayi saurin gyara zancen ta. "Kar ka damu amma, da an gama zancen nan ni da kaina zan saka shi a gaba sai ya motsa." Murmushin da ya sake yi ya sata jin wani ɗaci a zuciyarta, ba sau daya ba sau biyu ba tasha tunanin kawar da Ishaq daga hanyarta kamar yadda ta kawar da abubuwa da yawa a rayuwar Ma'aruf, don duk wani abu da zai jawo ya raba zuciyarsa da kowa bayan ita, bata ƙaunarsa sam! Amma matsalar shine Ishaq ba ƙaramin amfani yake mata ba, amfanin da shi ta lissafa har ta bada shawarar dawo dashi wajensu bayan ya rasa iyayensa ba don kyautatawar da duniya ke kallonta dashi ba. "Akwati nawa kake so a haɗawa yarinyar?" Kamar bai damu ba, hankalinsa kwance yace. "Duk yadda kika yi Mami daidai ne, ni yanzu abinda ke gabana daban harkar Office ce da zanje in gyara, Baffa yace anyi asara da yawa a wannan watan." Ba shiri maganar ta doka wata tsawa a cikin kan Hajiya Kilishi tana janyo

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73