Chapter 64
Chapter 64
da zata iya a yanzun ma zata kara masa lokaci ne, amma ta san ko ta kara ba zai barta ba don haka dole ne ta daurewa kanta a yau ta fuskance shi. A hankali ta ajiye kofin hannunta akan windon, sannan tace. "Ban manta ba J." Taji ajiyar zuciyarsa daga ciki kafin yace. "Then where did you decide?" (Ina kika zaba?) Ta sake cije lebbenta na ƙasa "Where we first met." (Wajen da muka fara haɗuwa.) Kalaman suka daki zuciyar Jawad da tasirin da ita bata san shi ba, don a nata ɓangaren ta zabi fadar haka ne don zuciyarta ta tsara mata cewar a wajen da suka fara haɗuwar anan ya kamata ta kawo ƙarshen alaƙarsu gabaɗaya, ko yaƙi, ko ya so. Kuma ƙarfe biyar da ƴan mintunan tayi mata a kofar Joint ɗin 'Harish', ta fito daga motar ta bayan ta jera ta a layin sauran dake wajen sannan ta gyara zaman dan mitsitsin mayafin data dora akan doguwar rigar jikinta ta atamfa, wadda akayi mata wani ɗinkin mai kyau daga kasa kuma tayi buɗewar umbrella, takalmin kafarta ba mai tsini bane wannan karon don ta sani rashin nutsuwar zuciyarta ba zai barta ta iya tafiya a cikin mai tsinin ba, ta shiga ciki babu mutane sosai, ƴan kaɗan ne kawai ke zaune akan kujerun wajen yayin da iskar yamma da kuma ƙamshin shuke-shuken wajen ke shiga hancinta. Daga can karshe ta hango Jawad, zaune akan table din da a wajensa suka fara haɗuwa, ba zata tantance idan tebur din ne ko an canja shi ba amma dai wajen ne, yana sanye da wasu dogwayen kaya Kaftan, yasa hula dark brown wadda ta fito da hasken fatarsa tar a cikin yammar, Jawad mai kyau ne ba sai kowa ya tuna mata hakan ba. Kuma da alamu ya jima a wajen don tuni an sauke shi da shishar da yake bula hayakinta a iska. Kafafunta suka ƙarasa wajen a hankali sanda shima ya hango ta, kuma a lokaci daya murmushi ya sauka akan lebbensa yana ƙara tuna mata da kammaninsa. "Kina da cika alƙawari Babe, yana daya daga cikin abubuwan da suke kara haukatani akanki." Bata yi murmushin da ta saba kamar kodayaushe ba sai kawai ta jawo kujerar dake fuskantarsa ta zauna. "Wane flavour za'a kawo miki?" Ya tambaya yana tasowa daga kishingiɗen da yake. Ta ajiye wayarta akan table din tare da earpiece ɗin hannunta sannan ta kalle shi sosai. "Ka san ba abinda ya kawo kenan ba Jawad, idan zaka kyauta ma just put yours aside muyi magana." Ya gyada kansa yana kallonta. "Zanyi duk abinda kika ce Barbie." Da haka ya ajiye tasan gefe yana cigaba da kallonta, idanunsa na lumshewa akan fuskarta. Bata damu da yadda yake kallon nata ba kai tsaye ta fara magana. "Jawad abubuwa sun cakuɗe a rayuwata yanzu, I've got alot going on table da ba sai nayi maka bayaninsu ba amma hakan ne yasa na yanke alaƙa ta da kai, don bani da wannan lokacin Jawad, abinda nasa a gabana ya karato don haka dole ne na ajiye ka a gefe. Kuma nayi ƙoƙarin nuna maka hakan ta duk hanyar da zan iya amma ka kasa ganewa, shi yasa na yarda muyi wannan haduwar don in shaida maka komai baki da baki." Tunda ta fara maganar bai ko kifta idanunsa ba, kallonta kawai yake da dukkan irin emotion din da zata iya tsinta a cikin idanunsa, wanda basu dame ta ba ta cigaba. "Idan baka manta ba Jawad, tun farkon alakarmu na gaya maka cewa babu aure a tsakaninmu na san baka dauki maganar da muhimmanci ba a lokacin amma ni da gaske nake tun a sannan. Bari na fito fili na gaya maka gaskiya Jawad, a lokacin da na haɗu da kai ina cikin damuwar da ni kaina ban san mecece ita ba that is bayan mutuwar aurena na biyu, so na kula ka ne kawai don ka taimaka min in manta damuwa ta, and you really did help 'cox we wasted away ta hanyar ta hanyar da har sai da kasa na kusa manta cewa ina da abinda nake so bayan kai. Yadda kayi treating ɗina Jawad da tsananin kulawa da komai shi yasa zuciyata ta yi laushi akanka har kayi tunanin duk abinda nake yi maka zai iya sawa na canja ra'ayina akanka, but honestly ban ɗauke ka komai ba more than a toy (abin wasa), baka taɓa zama wani abu mai daraja har da zan kalla da sunan aure ba Jawad. Zuciyata ta mutum ɗaya ce a duniyar nan kuma ina jin cewa ko za'a tsaida tashin duniya akaina ba zan taba iya canja hakan ba. So ka taimaka min mu karkare komai a yanzu, Let's just end everything here don ni tuni na fara gudanar da da sabuwar rayuwar da a cikinta zan cimma burina, ka taimaki kanka ka manta dani kaima Jawad. Erase all those memories kayi pretending babu abinda ya taba faruwa tsakaninmu wanda na san a cikin kankanin lokaci zaka ji ka manta dani gabaɗaya. Ka kalli kanka, kana da komai the looks, status, kuɗi, age, time... You have it all J. (Kana da komai) zaka samu ƴanmata guda dubu da kallo ɗaya zaka yi musu and in no time they will be throwing themselves over you. Ka fahimta dan Allah Jawad cewa ni ba komai bace a rayuwarka." Ta ƙarashe da dukkan fatan ya fahimce ta a cikin idanunta, kuma har a lokacin kallonta yake shima, sai da ta kai ƙarshe ɗin sannan ya ƙifta idanunsa a hankali, yana komawa da baya, ya jingina sosai da kujerar da yake kamar kwanciya zai yi sannan muryarsa ta fito. "Anything more Barbie?" (Akwai wani abu kuma Barbie?) Ta haɗiye yawu a makogwaronta sannan ta girgiza kanta. "Nothing more Jawad, shikenan idan har ka fahimce ni." Sai ya gyada kansa haɗe da rufe idanunsa ya buɗe kafin yace. "Thank you." ( Nagode.) Ta kalle shi tsawon wasu sakanni zuciyarta na son nazarin yanayin dake kan fuskarsa wanda bata gane ba kuma ta kasa gano komai ɗin, hakan yasa kawai ta dauki wayarta data ajiye sannan ta mike tsaye. "Nagode nima, sai wani lokacin." Ya sake gyada mata kansa ba tare da yace komai ba, kuma da haka ta juya ta tafi, idanunsa suka bi bayanta da kallo, zuciyarsa na tsagewa da yadda jikinta ke kaɗawa da tafiyar da take yi yayin da ƙwaƙwalwar sa ke dawo masa da kalaman abokinsa Haro. "Ka sake gwada ta for the last time Man, idan har tana nan akan bakan ta cewar ba zata saurare ka ba, nayi maka alƙawari ni zan taya ka yarinyar nan tayi biyu babu a rayuwar ta, dama na tsane ta J, kaima ka san na tsane ta!" Ya cije bakinsa da ya bushe yayin da wani guntun murmushi ya sauka akan leɓɓen nasa lokacin da Ruƙayya tayi kwana ta fita daga wajen tana ɓacewa ganinsa. Wayarsa ya zaro a cikin aljihunsa ya shiga neman nambar Haron, bugu kaɗan kuwa ya ɗaga lokacin da ya jawo kan shisharsa, kuma sai da ya zuƙo hayaƙinta ya busa a iska sannan yace. "Tayi biyu babu Haro, let the plan start!" *** Jigawa, 11:05 Am. "Gwara ki fito fili kawai ku fadi gaskiya, yanzu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73