Chapter 33
Chapter 33
hayaniyar su Aunty da Aminu daga waje akan motar da zata fara ɗaukan kaya, don gobe Tanti tace ya kamata a fara jere. Tsoro take ji da gaske, Tana ji kamar tana faɗowa ne daga wata sama mai nisa, kamar tana tafiya cikin idanun nasa inda ruwan cikinsu zai nutsar da ita da kuma numfashinta. Abinda bata sani ba shine har yanzu a gaɓa take, bata shiga koina ba ma balle ta fara nutsewar! *** Wasa farin girki! #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. Bari nayi sauri na wuce, a yafe min.🙏🙏🙏 BABI NA TAKWAS. ~~~~~ Ɗimbin jama'ar dake yin tururuwa suna ƙara cika kowanne ɓangare na cikin masallacin su suka shaida auren mutum takwas ɗin da aka ɗaura kowanne kan sadaki mabanbanci, motoci kawai kake gani daga koina an ajiye su yayin da wasu ke ƙara shigowa suna daɗa adadinsu. Jama'a kuwa babu wanda ya san adadinsu sai ubangijin daya tara su gurin, dattijai da samari har ma da yara masu tasowa, gasu nan kala-kala kowanne ango da ƙungiyarsa da sai faman gaisawa ake ana ɗaukar hoto. Daga can gefe, Kawu Ibrahim ya ƙaraso inda tasu tawagar ƴanuwan take, ya tsaya a kusa da Kawu Hamza yana girgiza kansa. "Ka san yaron nan har yanzu bai iso ba." "Ai ba zuwa zaiyi ba, gwara mu ma mu hanzarta mu bar wajen nan don ni jirgi na na ƙarfe uku ne ma, kuma akwai abubuwan da zanyi kafin nan." Kawu Ibrahim ya juya ya hango su Kawu Mallam dake tsakiyar mutanen yana gaisawa da sauran ƴanuwansu fuskarsa cike da irin kalar tasa murnan, sai kawai ya juyo da kansa yace. "Har yanzu na kasa gano dabararsu akan auren nan, babu wani abu dake nuna min cewa ba don saboda kudin mutanen nan komai ya faru ba." "Koma meye dalilin nasu, a yanzu komai ya riga ya faru, kuma duk matsalar data faru daga yanzu kuma na tabbata shi ɗin yana da hannun ɗaukarta." Kawu Ibrahim ya girgiza kansa. "Muyi fatan alkhairi kawai, don har cikin zuciyata ina tausayin yarinyar nan, Amina tana da hankali wallahi." "Hankalin da bai kamata ace an ƙuntata rayuwarta tun daga yanzu ba. Ai wallahi da nine da ikon Kawu mallam, auren nan ba zai taɓa faruwa ba." Kafin Hamzan ya sake magana wayarsa tayi kara don haka ya dauka yayi gefe yana ƙoƙarin amsawa. Kuma sai a lokacin idanun Ibrahim suka iya hango masa Baba (mahaifin Amina) yana daga tsakiyar mutanensa sai faman gaisawa yake dasu fuskarsa ɗauke da ɗimbin fara'ar da ya kasa auna nauyinta dana kuɗin sadakin auren dake cikin aljihunsa, dubu ɗari cif! A cikin ƙwaƙwalwar sa lissafi yake cewar ko da kudin zasu iya ninka adadinsu sau goma baya jin zai taɓa iya bada ƴarsa aure ga mutumin da akace yana da matsalar ƙwaƙwalwa, tunda gashi tun a yanzu sun fara gani, in ba haka ba wane ango ne yake ƙin halartar wajen ɗaurin aurensa? *** Motar ta shigo kamfanin da saurin da ya saka maigadin da ya buɗe gate ɗin juyowa yana kallonta, kuma duk saurin nata sai da ta isa ga layin da ake ajiyar motoci ta tsaya sannan ƙofar mazaunin direba ta buɗe. Ishaq ya fito sanye da wasu kaya kalar sararin sama, wayoyinsa rike a hannu ya rufe ƙofar sannan ya tunkari cikin ginin dake kallo shi, wani gini mai hawa uku da yasha adon gilasai tun daga samansa har ƙasa. Security ɗin daya bude masa ƙofa har sunkuyawa yayi bayan ya gane shi yana fadin. "Yallaɓai sannu da zuwa." Kuma maimakon ya amsa sai kawai ya tambaye shi. "Ma'aruf yana ciki ko?" "Eh tabbas, ai tun safe ya iso yallabai" Jin haka yasa Ishaq ɗin yin gaba zuwa hanyar matattakalar da zata kaishi sama, wata receiptionist (mai karbar baki) a wajen mai suna Rafi'at ta shiga gaishe shi tana murmushin da ke manne cikin tsarin ayyukanta, kuma da mamakin yadda akayi bata manta fuskarsa ba duk da karancin zuwansa wajen ya ɗaga mata hannu yana zarcewa zuwa saman. A hawa na farko can ƙarashe ofishin Ma'aruf ɗin yake, don yana tuna lokacin da yake gaya masa cewa ya canja office, ya isa ƙofar daidai lokacin da sakatariyar Ma'aruf ɗin mai suna Martha ke fitowa riƙe da wasu files a hannunsa. "Sannu da zuwa yallabai, yana tare da wasu baki ne a ciki, ko zaka jira su kammala." Martha ta fada da murmushin dake nuna masa da gaske take, kuma ya san lallai baƙin masu muhimmanci ne don babu ta yadda za'ayi ta tsaida shi idan ha haka ba. Gyada kansa kawai yayi alamar ya fahimta sannan ya ƙarasa kofar ya buɗe ta, idonsa ya gane masa wasu inyamurai biyu da kuma wani ɗan china, dukkansu suna zaune a kujerun dake tsallaken teburin Ma'aruf ɗin, kuma budewar kofar tasa dukkaninsu suka juyo suka kalle shi, Ma'aruf na sanye da wani bakin yadi mai sealed ɗinkin da ya fito da tsarin jikinsa, hular kansa ma baka ce data dace da shigar da ita kadai ya kamata ta tabbatarwa da Ishaq cewar abinda yake tunani tabbas haka ne, dama baiyi niyyar zuwa wajen daurin auren ba. "Bismillah, ka shigo mana." Ma'aruf ɗin ya faɗa yana kallonsa, sannan a lokaci guda ya maida kansa kan takardar dake gabansa yana ƙarasa rubutun da yake yi, ya kuwa karaso cikin daidai lokacin da ya rufe takardun ya miƙowa mutanen tare da murumushin daya dace da fuskarsa. Ɗaya daga cikin inyamuran ne ya karba tare da yin godiya kafin dukkanninsu suka mike a lokaci guda, Ma'aruf ɗin ma ya mike yana miƙa musu hannu, ɗaya bayan ɗaya suka gaisa kowanne da murmushi yayin da yake sake yi musu alkawarin cewar kar suji komai, suyi aikin da zasu yi kawai babu abinda zai gifta a tsarinsu. Kuma watakila yanayin fuskar Ishaq ɗin suka kalla don babu wanda yayi masa magana a cikinsu suka yi hanyar kofar suka fita. "Wanne za'a kawo? Tea ko Coffee" Muryar Ma'aruf ɗin tasa hankalinsa dawowa daga rakiyar da yayiwa mutanen nan, ya juyo ya kalle shi. "Kaima ka san ba abinda ya kawo ni ba kenan." "Na sani..." Ma'aruf ya faɗa yana komawa kan kujerarsa. "Shi yasa na tambaye ka hakan ai, don idan ka fara muryarka zata fi fitowa idan da abu mai zafi a kusa." Sai kawai ya girgiza kansa, yace. "Wane irin rashin mutunci ne wannan B? Ya za'ayi ranar da za'a ɗaura maka aure guda ka taho Office? Ka san tarin mutanen da suka neme ka a wajen nan?" "Really? Ai da ka sani kawai su biyo bayanka ku same ni anan sai su ganni." Wani irin abu ya sake tasowa Ishaq, sai kawai ya karaso gaban teburin nasa ya zube wayoyinsa sannan ya kalle shi sosai yace. "Abinda kake yi ba daidai bane Ma'aruf, me yasa ko sau ɗaya a rayuwarka ba zaka yi abu irin na mutane ba? Ka nuna baka son auren nan da farko, daga baya kazo ka nuna ka yarda saboda Baffa, to idan haka ne me yasa zaka kunyata shi a yau? Me yasa baka je wajen ba alhali ka san rashin zuwan naka zai iya haifar da wani abu?" "Me zai haifar?" Ya tambaya alamun hankalinsa a kwance, kafin ya cigaba. "Zai haifar da rashin faruwar auren ne? Kana tunanin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73