Chapter 37
Chapter 37
iya fitowa ba, tana kallonsa ta tagar ɗakinta ya juya da motarsa ya fita. "Babe I'm really sorry, ki manta maganar da na gaya miki dan Allah, just talk to me!" Sakƙon message ɗinsa bayan katsewar kiran ya nuna akan wayar, sai kawai ta ɗauke kanta tana kallon waje, bata lissafa Jawad a cikin matsalolinta na rayuwa ko kaɗan. Ta kalli wajen daidai lokacin da idonta ya kai kan su Ashraf da ƴan sandan nan, magana suke da wasu mutane a ƙofar wajen basu shiga ciki ba, kuma ta cikin hasken fitulun wajen taga Ibrahim ya dafo kansa ta baya tare da riƙe ƙugunsa alamun wani abu ake gaya musu da ya sa shi mamaki don ta hango mutanen na magana. Ta hango Ashraf daga gefen tsohon da ya rako su yana sauraren mutumin kafin ya dunƙule hannunsa ɗaya akan bakinsa alamun nasa mamakin shima. Ba shiri ta buɗe handle ɗin motar ta fita, hasken fitulun wajen na shigar mata ido amma bata damu ba ta ratsa ta tsakanin sauran ƴan sandan da kuma Bilal ta isa gabansu, ta isa gabansu lokacin mutumin ke cigaba da cewa. "... Ai na gane wanda yake bayani, shine dai Ma'aruf ɗin manajan kamfanin nan, sai dai idan kuna da hanyar da zaku same shi a gida, amma bana jin ko ranar litinin zai shigo, don yau aka ɗaura aurensa na gaya maka!" Ya rufe bakinsa lokacin da ta cikin hasken fitulun wajen ƙwaƙwalwar Rukayya ta karanto mats manyan rubutun dake saman ginin... 'Bakori Enterprises' Kuma wayar hannunta da ta fara faɗuwa, ita ta juyo da hankalin kowa a wajen kafin su ankara da tata faɗuwarta har ƙasa! *** Daga Babi na gaba labarin FARAR WUTA zai fara insha Allah! #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. BABI NA TARA ~~~~~ Let's go back to when we had not learn our names, when we introduced our souls, while our heart gasped for breaths. -Aliyu Jalal. * A cikin sabon gidan mutane sun fara raguwa sosai, ba kamar a ɗazu da koina yake a cike da mutane ba, Aunty Safiyya ta taho daga hanyar falo ta biyo wani ɗan dogon korido mai ɗauke da ɗakuna ta shigo ƙofar ɗakin dake gefe, a cikin ɗakin duk ƴan uwa ne na kurkusa sai kuma amaryar dake tsakiya kanta a sunkuye tana faman kukan da babu sauti sai hawaye kawai da take sharewa. Aunty Safiyan da ta shigo tace. "Na rasa yadda akayi aka manta da tsitsiyoyin nan wallahi, yanzu da ba sai a share gidan ba kafin mu tafi." "Aunty ai na zata sharar dare babu kyau." Ummi dake kokarin dora akwatuna can saman wardrobe din dakin tare dasu Momi ta fada tana juyowa. "Wannan ai kamawa tayi..." Cewar Aunty Ma'u. "Baki ga falon nan ba duk kasa ce wallahi, don bana ji akwai wanda ya shigo babu takalmi." "Ni maigidan ma nake ji, haka zai shigo yaga waje duk ƙura?" Ɗaya daga cikin matan Baban Kurna tace. "Da za'a iya tunda akwai kofa ta baya sai a shiga gidan a tambayo su wallahi. Mahaifiyarsu Ummi da itace zaune a gefen Amina rike da hannayenta ta girgiza kai tace. "A hakura kawai, gobe da safe insha Allah sai su Maryam su zo su kawo mata kawai, su taya ta sharar ma." Ta fada tana kallon Maryam din dake tsugunne a gaban Amina ta riko ɗaya hannunta. "Ɗan kunnayen nan naki suna cikin wata ƴar ƙaramar jaka pink, ina jin a cikin wata Ghana must go aka saka." Cewar Maryam din tana kallon idanun Aminan da duk yadda suka yi ja saboda kuka wannan kyallin na cikinsu na nan. Ta san ba zata amsa ba saboda haka ta cigaba da cewa. "Hijaban sallarki ma suna cikin wannan karamin akwatin na undies, Amma ce tace in sa miki anan." Sai ta gyada mata kai kawai tana ƙara share hawayenta lokacin da Aunty Safiyya ke tambayar su Ummi idan sun kwashe kayan cikin akwatunan kafin su dora su. "Duk mun zuba su a cikin wadrobe ɗin, na kayan kwalliyar nan ne da kuma wannan Ghana must go ɗin zamu bari a ƙasa. "Eh, ku barsu ta gyara ta kanta, sai ku zo mu tafi kuma don goma ta wuce." Jin haka yasa Fatima ta taho daga wajen su Ummin tana ƙarasowa gaban Amina, lokacin da Maryam ke cewa. "Idan zamu zo goben zamu zan taho da Hafsa insha Allah." Fatiman ta sunkuyo tace. "Amina litattafan nan naki ba'a ɗebo ba, sai dai daga baya ko Aminu ya kawo miki." Sai a lokacin ta ɗago da idanunta ta kalle su, me yasa ne suke ta yi mata zancen kaya bayan ba abinda ke gabanta kenan ba? Mantawa suka yi cewa tafiya zasu yi su barta? Su barta a wannan wajen da bata san makamar abinda zata fuskanta ba, ko Abdallah ta aura ai dai sun san cewa wannan lokacin mai ciwo ne a wajenta, balle kuma mutumin da bata san ya yake ba balle takamaimai halinsa. Aunty Ma'u ta miƙe tsaye tana gyara mayafinta tace. "Sai hakuri Amina, kin ji dai duk nasihar da akayi miki daga can gida, sannan su ma iyayen mijin naki kinga yadda suka karɓe ki, sunce ƴa suka karba ba suruka ba tunda dama duk ɗaya ne, kuma kowa ya san halinki Amina, duk wanda ya sanki yabonki yake yi... Mutanen nan sune basu sanki ba, kuma yanzu ne mafarin zamanku, dan Allah ki ɗorar da halinki a wajensu Amina... Don wannan gaɓar itace mafi alkhairin rayuwarki, ki sa su zasu zo suna bamu labarin kyautatawarki..." Ba shiri Amina ta sake fashewa da wani sabon kukan da ya nemi mazauninsa a zuciyar duk wanda ke ɗakin, taji zuciyarta na sake karyewa da tausayin kanta, kalaman suna tuna mata da na Gwaggo Balkisa a dazu kafin tahowarsu, ɗakin Amma da suka cika aka kaita don ayi mata wannan fadan na al'ada, kuma sai da kowa ya gama nasa sannan ita Gwaggon ta kamo hannayenta duka biyu tace. "Amina kin sani cewa daga yau sabuwar rayuwa zaki fara wadda babu iyayenki bale kuma sauran ƴanuwanki a kusa, zaki zama ɓarin wani mutum daban da zai bukaci tsananin kulawarki, Kiyi amfani da hankalinki da kowa yake yabo ki zame masa mata kuma Uwa, ki kokarin zame masa komai a rayuwa ta duk wata hanyar da zaki iya. Ba abu ne mai wuya ba Amina, don maza banbancin su kadan ne dana yaro ƙanƙani, kulawarki kawai yake buƙata sai ki ganshi a tafin hannunki. Kar ki dauki kulafucin barin gida ki sa a ranki fiye da ƙima, shima nasa iyayen zai bari yazo ya zauna dake, banbancin kawai shi namiji ne da zai daure ke kuma mace ce, ki saki ranki ki saba da sabuwar rayuwar da zaki fuskanta don itace rayuwarki ta yanzu dama ta gaba. A kowanne aure akwai sirri Amina, ki riƙe sirrin gidanki ki riƙe sirrin sa, ki zauna lafiya kamar mahaifiyarki, kina ganinta dai shekaru fiye da ashirin kenan da muka kai ta daki amma daidai da rana guda bamu taba jin bakinta ba. Kiyi wa mijinki biyayya, ki girmama shi, idan kika yi haka kema kin girmama kanki. Mace mai wayo ita ke gina gidanta Amina, sakarya kuma da hannunta take rusa shi." Don haka a yanzu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73