Chapter 60
Chapter 60
duba lambar aka ga ma ba tasa bace dole aka haƙura don ko ƴan sanda basu iya samo komai ba. Kuma bayan haka ni na zauna nayi jinyarta Amina, tun kafin a yanke ƙafafun har muka je India aka cire su gabaɗaya, shekara guda da rabi na ɗauka ina jinyarta, na hana kowa wannan ɗawainiyar hatta ƴaƴanta da ƴanuwanta tunda na san na samu abinda nake so, na san tsawo na da nata ba zai taɓa daidai a idanun Baffa ba, kuma hakan ya ƙara min ƙima a idanun kowa a gidan nan ta yadda nake cin kare na babu babbaka, kowa yana girmama ni da bani darajar dana siya a wajensu, hatta ƴaƴan Maimuna a idon kowa kamar nawa suke don babu adadi su Munaya zasu zo su faɗa min abinda mahaifiyar tasu ma baza su iya faɗa mata ba ko kuma su nemi shawarata akan abinda ita bata ma sani ba. Don haka yanzu na san kin fahimci cewa saboda ni kika samu soyayyar kowa gidan nan, da kuma abinda nake nufi cewa duknwanda kika furtawa wannan zancen kamar kin bude masa kofar lahirarsa ne." Muryarta tayi shiru a wannan lokacin, wucewar wasu sakanni sai kuma ta taso a hankali ta dawo kujerar kusa da inda Aminan ke zaune, kuma bata damu da rashin kallonta da har yanzu bata yi ba ta cigaba. "Mu dawo kan abinda ya kawo ni, dalilin da yasa na aura miki Ma'aruf Amina, kamar yadda na faɗa ba don ki zo kiyi rayuwar zaman aure bane kamar yadda naga kin fara kokarin yi a yanzu, na kawo ki gidan nan ne saboda ki taya ni mu ƙarasa babban burin da nake dashi a duniya. A farkonsa ban tsara dake ba, amma daga ranar da Baffa ya yanke shawarar cewa dole Ma'aruf ya ƙara aure, daga ranar kika shigo cikin lissafina Amina, don Ma'aruf ginshiƙi ne guda a cikin burin da nake son cimmawa a yanzu, ina ɗora shi ne akan matakan da zasu kaini ga yin nasara ɗaya bayan ɗaya, don haka idan har aka samu matar da zata raɓe shi wadda ba zan iya juyawa ba Amina abubuwa zasu lalace min ba kaɗan ba, shi yasa tun kafin kowa yayi wani yunƙuri musamman mahaifiyarsa dana san a tarin ƴanmatan dake danginsu zata iya haɗa shi da wata, na duba bayana na zaɓo ki." Sai da ta sake gyara zamanta tana fuskantar Aminan dake zaune a gabanta ta sunkuyar da kanta sannan tace. "Ɗago nan ki kalle ni Amina..." Ta kuwa ɗago da kan nata amma bata kalle ta ba, gashin idanunta sun hade suna shaida jiƙewar hawaye alamun kuka take yi, wani murmushin yaso giftawa a leɓɓen Hajiya Kilishin amma ta tare shi, don da kukan Aminan da kuma shi ɗin, duka bata ga muhallinsu a yanzu ba. "Sati guda zan baki kiyi tunani, idan har kika yarda dani, zan ƙawata rayuwarki da dukkan ƙawar da baki taba tunani ba Amina, zan miki liƙin alheri har sai hannayenki sun kasa tarewa, zan ɗaga ki ki zama tauraruwa a idon kowa musamman cikin danginki, zan kyautata rayuwarki da ta dukkan makusantanki idan har kika miƙo min hannunki na kama kamar yadda na tsara komai..." Ta sake yin shiru tana kallon haɗewar gashin idon nata, sai kawai ta haɗiye yawun dake bakinta sannan ta ƙarasa furta abinda ke tahowa tun daga ƙasan zuciyarta, abinda take jin ko da duniya zata taru akanta ba zai canja ra'ayinta ba. "... Idan kuma har kika zabi yin katoɓarar fallasa ni don ki tsira, na rantse miki da ubangijin da ya halicce mu rayuwarki zata dulmiya ne a baƙin ruwan da zaki yi ta yin ihun da babu wanda zai taɓa jiyo muryarki!" *** Tun da ya shigo gidan jikinsa ya bashi akwai wani abu da ya faru, don fitilar falo ma a kashe take, iya hasken ta korido ne kawai yake a kunne, a falon ya ajiye wayoyinsa da su kaɗai ne a hannunsa sannan kai tsaye ya nufi hanyar koridon, ɗakinsa yayi niyyar wucewa ya watsa ruwa don Allah ya sani a gajiye yake, amma a lokaci guda idanunsa suka kai kasan ƙofar dakinta da nan ma fitilar a kashe take. Har ya wuce ya dawo ya tsaya ya kwankwasa, kusan sau uku amma shiru bata amsa ba, sai yayi tunanin sallah take don a lokacin masaltai ke kiran isha'i, don haka sai kawai ya juyo ya dawo ɗakinsa. Ya kunna fitulun ciki da suka gauraye da haske a ɗakin komai yana fitowa tar cikin kammalen da yake. Ma'aruf yana da tsaftar da duk wanda ya zauna dashi zai gane, don indai abu nasa ne to ba zaka taɓa zuwa kaga komai ba'a muhallinsa ba, sannan kuma yana da haƙurin da zai zauna da wanda bai damu da hakan ba, shi yasa ya iya zama da Ishaq dake wular da komai inda yaga dama. Minti goma kawai ya ɗauke shi gama shiryawa cikin wasu kayan bayan yayi wanka, ya dawo falon daidai lokacin da wayarsa ke ƙara a inda ya ajiye ta, lambar mutumin da yasa ya nemo masa bayani akan Mr. Okafor ne, ya tsaya kawai yana kallon kiran ba tare da ya dauka ba har ya katse sannan ya tura masa dan guntun saƙo cewar suyi magana zuwa gobe. A yanzu ya sani cewar tarawa kansa abubuwa yana ɗaya daga cikin abinda ke saka shi damuwa har ciwonsa ya tashi don Allah ya sani a yanzu yana tsoron ciwonsa fiye da kowa, ya sani cewa idan abubuwa suka lalace masa a yanzu bai san me ya cimma a rayuwarsa ba. Shi yasa bai ɗauki kiran mutumin ba, don a yau kaɗai abubuwan da ya fuskanta suna da yawa. Takardar sammacin da ya samu ɗazu a Office ta girgiza shi ba kaɗan ba, ya kasa hango inda Rukayya da iyayenta suka samu karfin gwiwar kaishi kotu akan zancen Hamida, kalaman Baffa su suka bashi damar ƙin saurararsu amma bai taba tunanin hakan daga garesu ba. Ya kira Ishaq sunyi maganar amma duk tsawon tattaunawar su ya gaya masa cewa chance din da suke dashi kaɗan ne don a matsayin Hamida na mace dole ne a wajen mahaifiyarta ya kamata ta zauna har girmanta kuma ƴan bayanan da suke dashi game da dalilin su na dawowarta wajensa basu da karfi sosai. Sannan bayan yayi haka ya san yayi aiki a Office din amma ya tabbata idan ya koma gobe zai samu kura-kurai da yawa, don a cikin aikin ya gama yanke dukkan abinda ya riga ya tsara game da zancen kotun da kuma Hamida. Kuma baya buƙatar yin zancen da kowa shi yasa ko cikin gida bai shiga ba tunda Baffa baya nan yayi tafiya Abuja, yaga kiran Mami amma shima bai bi bayansa ba kuma itama bata sake kiran ba har yanzu. Ƙafafunsa suka sake komawa kitchen ɗin bayan ya kunna fitila yana nazarin komai, akan table ɗin kitchen ɗin, jerin kayan abincinsa ne kamar yadda take tsara su kullum, yaji wani abu ya zarce cikin makogwaronsa, a cikin ƴan kwanakin nan ya sani cewar yarinyar nan ta taimakawa ƙwaƙwalwar sa wajen samun hutu ta wani ɓangaren, don akwai nutsuwa sosai ace idan aiki ya zuƙe shi da rana akwai inda zai iya zuwa ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73