Skip to content

Chapter 27

Chapter 27

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

cikin idanunsa, tana kallon yadda yanayin dake cikin idanun nasa ke juyewa zuwa wani abu da ba zata iya fassara shi ba. "Saboda me?" Yayi tambayar kamar iyakarta zata sa ta canja ra'ayinta. "I'm sorry J, amma saboda gidan tsohon mijina zan koma kuma na riga na tsayar da zuciyata akan hakan, idan har ba zaka iya rayuwa ba sai da ni, to ni wataƙila munyi tarayya akan hakan, don nima ba zan iya rayuwa babu Ma'aruf ba Jawad." Bata san me yake tunani ba, bata san me yake lissafawa ba, kawai kallonta yake ɗauke da wannan yanayin da, da ace lokacin da ta buɗe ido daga bacci ne ta ganshi a hakan, zata rantse cewar ba shi bane. Saboda haka tayi baya a hankali ta fita daga cikin hannayensa, kuma sai ƙarar wayarta tazo a daidai wannan lokacin don haka ta isa wajen jakarta dake yashe daga can gefen gadon ta ɗauko wayar, bata ko tsaya tantance lambar dake kiran ba, ta ɗauka ta kara a kunnenta. Kuma abin da muryar cikin wayar ta faɗa tun kafin ta kai ga cewa komai, shi yayi sanadin da zuciyarta ta doka a cikin ƙirjinta sannan wayar ta zame daga cikin hannayenta ta faɗo kasa ta tarwatse! *** Ina Ma'aruf yake? Kuna tunanin saƙon cikin wayar nan ya dangance shi? Meye gaskiyar labarin Fatima? #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. Please go and read RAI DA ƘADDARA by LUBNA SUFYAN... that story is touching me.😍 BABI NA BAKWAI ~~~~~~~ "Mark my words, idan har wani abu ya same ta, babu wanda zan saurara Ishaq, babu wanda zan saurara." Muryar Ma'aruf, ta faɗa a cikin ɗakin asibitin da misalin ƙarfe takwas na wannan daren, yana zaune daga gefen gadon ɗakin da waya kare a kunnensa yayin da daga tsakiyar gadon, wata ƙaramar yarinya ce kwance tana bacci. Da hannunsa ɗaya ya shafo kansa sannan ya sake cewa. "Saboda me? Shekaru biyu ta hana ni ganinta amma yau sai na tsince ta a tsakiyar wannan gidan arnan? Idan kana yiwa Allah ka gaya min cewa zan iya maka ta a kotu a hukunta ta." Daga cikin wayar Ishaq ya sake cewa. "Ka taimaka ka fara kwantar da hankalinka yanzu B, ba dai yarinyar tana hannunka ba? ai anci rabin matsalar abinda zai biyo ba mai yawa bane. Sannan na tabbata shi kansa Baffan yanzu idan yaji komai, ba zai sake goyon bayanta ba, mu godewa Allah ma da ba'a dauki shekarun da suka fi haka ba." Baice komai ba ya cigaba da motsa yatsunsa a cikin gashin kansa kawai yana sauraren duk bayanin da yake yi kafin wayar tasu ta kai ƙarshe, suka yi sallama bayan Ishaq ɗin ya gaya masa cewa sai jibi zai dawo don aiki ya kaishi wani gari a can hanyar Abuja. Ma'aruf ya sauke wayar a lokacin da idanunsa suka sake komawa kan yarinyar, Hamida ce... ƴarsa, har yanzu tunaninsa ya kasa gasgatawa, ya kasa yarda cewa ita ɗin ya gani bayan tsawon shekaru rabonsa da ita kuma a wani waje da bai taɓa zato ba. Tsawon sati uku kenan da ya sadaukar da duk lokacinsa da komai wajen ƙoƙarin daidaita al'amarin da yake faruwa a kamfanin nasu. Wata irin asara suka yi da bata da tushe, bata da reshe kuma babu wani abu da yaja zuwanta. Dawowarsa kawai aka wayi gari da report din ɓatan maƙudan kuɗaɗen da babu ma wanda ya kula dasu sai a lokacin da aka zo fitar da wani kaso na harajin ƙarshen shekara da ake cirewa a duk ƙarshen kowanne wata. Anyi duk wani bincike amma babu abinda aka tarar daga ƙarshe, don haka Baffa yace a rufe zancen kawai su karɓi hakan a matsayin ƙaddara,. kasuwancinsu ya cigaba da gudana, amma haka kurum sai zuciyarsa taƙi bashi cewa hakan daidai ne, wannan aiki ne da ya riga ya saka ransa akai... Ba yana yinsa don yana sonsa bane yana yinsa ne don ya zame masa dole, dolen da a cikinta ba zai taɓa bari a lissafa da wata tangarɗa ba, don haka ya bi maganar Baffan ya cigaba da gudanar da aikinsa a gefe guda kuma shi da Faruk suna cigaba da bincike akan lamarin. A cikin binciken nasu Faruk ya samo wani mutum ne a cikin ƙananun ma'aikatan wajen da yace yana yana da wani bayani da zai iya basu, amma bayan Faruk ɗin yaje ya same shi har gida, sai ya ƙi bashi haɗin kai game da hakan duk kuwa yadda yayi dashi. Sun fahimci tsoro ne ya kama shi don haka shi yace zai je ya same shi duk kuwa da magiyar da Faruk ɗin yayi masa akan cewar kar yaje, magiyar da ya riga ya san ta mecece don dukkansu du niyun sun san cewar idan lamarin ya ɓaci babu wanda zai iya kallon Baffan a cikinsu da wani bayani. Amma shi kansa Faruk ɗin ya san cewa tunda har ya saka ransa babu abinda zai tsaida shi don ba tun yau ya sani cewar idan har ya furta abu zai yi to tabbas zai yi ɗin, bai taɓa ganin ya sa kansa yin abu ya fasa ba. Don haka kai tsaye bayan ya tashi daga aikin ya nufi unguwar sabongari da address ɗin da Faruk din ya turo masa don ba yadda zai yi. Ya isa da kyar bayan ya haɗa da tambaya sannan kwatancen ya tsayar dashi a daidai kofar gidan mutumin da yake nema. Sunansa Okafor, wani dattijo ne arne daya dade yana aikin shara a kamfanin, ya san shi tun lokacin da idan sun dawo hutu daga makaranta yake zuwa kamfanin, kuma har sai bayan ya fara aiki ne sannan aka ƙara masa matsayi zuwa aikin hada takardu saboda tsufan da ya kama shi, ya kalli takurarren gidan dake gabansa, mutane ne ke ta fitowa daga ciki kamar gidan tururuwa, a ransa ya ayyana cewa idan har Okafor yana da sa'a watakila zaman gidan ya kusa kare masa shi da iyalansa. Wani saurayi da ba ko riga a jikinsa sai gajeren wando da kuma sarƙa ya samu ya raka shi zuwa cikin gidan, kuma duk inda suka wuce juyowa ke an kallonsu da mamaki saboda manyan kayan dake jikinsa, nasa mamkin ya fara ne daga lokacin da suka shiga ciki inda yaga ashe gidan wani irin ƙato ne mai kuma tsawo, ga tarin ƙofofi birjiki daga kowanne gefe sannn da ɗimbin mutanen da ya san zasu iya tashin unguwa guda, ƙaton tsakar gidan ya cika taf da kaya da kuma igiyoyin shanya kota'ina, ga kwata layi-layi dake tashin wari kamar bola aka buɗe, sannan hayaniya kamar zata fasa kunne. Ba shiri ya haɗiye yawu yana sake damƙe mukullin motar dake hannunsa lokacin da idonsa ya fara arba da tiƙa-tiƙan mata sanye da ƙananan kaya suna ta harkokinsu tare da maza da kuma tulin yaran dake yawo koina, daga can gaba ya hango wasu suna faɗa, mata biyu ne sai ihu-ihu da zage-zage suke cikin yarensu, yaga masu raba su basu da yawa kowa harkarsa kawai yake a wajen. "Abeg no vex eh, this is Mr. Okafor's room." (Kar ka damu dasu kawai, ga ɗakin Mr. Okfor ɗin nan.) Saurayin nan ya katse shi lokacin da suka tsaya a kofar wani ɗaki mai ɗauke da ragwajajjen ƙofar

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73