Chapter 43
Chapter 43
jin abinda yake faɗa?!" Ta faɗa tana juyawa wajen mahaifiyarsu Hajiya Nafisa dake zaune daga gefe tana haɗa mata tea, idan da sabo ta saba da wannan fada a tsakaninsu, don ko Ashraf da yake sakon Rukayyan basa faɗa tare kamar yadda suke yi da Ahmad ɗin, shi mutum ne kaifi ɗaya mai tsatsatsauran ra'ayi, Rukayya kuma ba'a taka ta tayi shiru, don haka inuwarsu bata taɓa zama ɗaya. A yanzu ma dalilin ɗaga jijiyoyin wuyan nasu, Ahmad ɗin ne ya zo ne yana shaida musu cewa shi ya sake kiran Ma'aruf akan zancen Hamida, tunda sunyi magana da Ashraf yace zai tuntube su kuma bai sake cewa dasu komai ba, don haka shi ya kira shi da ɓacin ran hakan wanda a ƙarshe wayar tasu bata ƙare da daɗi ba, don Ma'aruf ɗin har gargadi ya masa da cewar labarin zai canja idan har ya sake kiransa. Ita kanta bata ga aibu a abinda Ahmad ɗin yayi ba, don Allah ya sani idan da Ruƙayya zata bata dama a lokaci guda ne zasu juya dukkan tanadin da suke mata akan Ma'aruf ita da kawarta zuwa sharri, zata fi jin karfin gwiwar cutar dashi akan abinda suke yi a yanzu, don haka ta cigaba da haɗa mata shayin kawai tana jinsu, tana ji kamar Ahmad na furta rabin kalaman dake cikin ranta ne da ba zata iya faɗawa Rukayyan ita da kanta ba. Kuma sai da taji kalaman nasa na shirin yin tsauri da yawa sannan ta kalle shi tace. "Ahmad, fita daga wajen nan." System ɗinsa da ya ajiye akan Fridge din ɗakin bayan shigowarsa ya ɗauka cike da fushi sannan ya nuna Rukayyan da ɗan yatsa tace, "Daga yau kar ki sake kirana a matsayin danuwanki duk sanda wani abu ya haɗa da mutumin nan, idan ba haka ba daga ke har shi I'm gonna rip your as* off! (Zaku gane kuranku!)" Da haka ya fice tana bugo ƙafar ɗakin asibitin, Rukkaya ta koma da baya ta rufe fuskarta da duka tafukan hannayenta biyu lokacin da Hajiya Nafisan ke miƙo mata kofin shayin. "Kin san halinsa ai sarai, amma kika biye masa kuke ɗaga murya a cikin asibiti, na sha gaya miki da kin ga ransa ya ɓaci kawai ki rabu dashi, wannan shine girman." Ta girgiza kanta a hankali sannan ta buɗe fuskar tana karbar kofin. "Maamah ba zan iya shiru akan abinda yake fada ba, kina ji fa yace har gargadi Ma'aruf yayi masa, to waye ya san iyakar abinda ya gaya masa ma? me yasa zai sake ɓata min al'amura ya sake ɓallo wani abu kuma?" Ta ƙarasa tana karɓar shayin, kuma garɗin abubuwan da aka cika masa da kuma ɗuminsa ya sauka har cikin ƙirjinta, ya sanya ta lumshe idanuwanta a hankali kafin ta buɗe su sosai akan kofin, da ɗaya hannun nata shiga murza bakinsa a hankali ba tare da ta kalli Mahaifiyar tata ba tace. "Maamah kince kawai aura masa yarinyar akayi ko?" Taji sanda Hajiya Nafisan tayi ajiyar zuciya kafin tace. "Tabbatar min akayi cewa a cikin sati uku akayi komai, ance bai taba ganinta ba ma har aka daura auren, sannan yarinyar bata da wani daraja, mahaifinta ance irin sana'ar ƙananun aikin katakon nan yake yi, don haka na tabbatar miki akwai wata manufa ta daban dangane da auren nan da bamu sani ba, amma ba wai aure yayi irin wanda kika sani ba." Wannan karon Ruƙayya rufe idanuwanta tayi duka, tana jin yadda wani tiririn zafi na daban da yafi karfin shayin dake hannunta yana cigaba da zurara a cikin ƙirjinta yana kona duk inda ya bi. "Nima na sani ba auren gaske bane Mami, don wallahi na san babu ta yadda za'ayi yarinyar nan ta shigo cikin tsarinsa, a yanayin arzikinsa dana gidansu ko haukacewa yayi akwai ƴanmatan sa suka fita daraja da yawa da zasu so shi a haka." Shi yasa bana son inyi wasa da kowacce irin dama Mami, a yanzu ban damu da duk hanyar da zamu bi mu lalata komai ba, don ban damu da manufar kowa ba, burina kawai kada yarinyar nan ta daɗe a rayuwar Ma'aruf, don ta haka ne kawai zan iya cimma burina Maamah, idan akwai ta, na sani ba zan taɓa iya samun abinda nake so ba." Kafin Hajiya Nafisan dake kallonta tace wani abu, ƙarar ringtone ɗin wayarta ya cika ɗakin, don haka ta dauko wayar tata dake gefen bedside drawer ta miko mata, Ruƙayya ta karba tana kallon sunan da ya fito akan screen ɗin, Jawad... Taji ranta ya ƙara dugunzuma ya ɓaci a take, bata san wane irin mutum ne shi marar zuciya haka ba? Me yasa zai cigaba da damunta alhali da kowanne yare da zai iya fahimta ta gaya masa cewa ya rabu da ita? Sai kawai ta danne buttton ɗin wayar gabaɗaya ta kashe ta sannan ta ajiye ta a gefe. Takaicin dake cike fal da tausayin ƴar tata ya nuna akan fuskar Hajiya Nafisa kafin ta girgiza kanta a hankali. "Na gaya miki ki kwantar da hankalinki ki samu sauƙi mu koma ki gida, don Hajiya Saude ta gaya min sai da haɗin kanki tukunna sannan komai zai daidaita, nayi miki alƙawarin Ma'aruf da ƙafarsa zai tako har inda kike ya neme ki." Wani abu kamar murnushi ya fito kan lebben Ruƙayyan yayin da ta sake jingina kanta baya da jikin gadon kafin a hankali kuma ta ɗago da kofin shayin nan ta kai bakinta. Daga can jihar Abuja, a cikin gidan rawar da Jawad yake a can sama, inda yaken wani lungu yana zaune akan luntsememiyar kujerar wajen shi kadai, a gabansa wani haddadden kwandon shisha ne da yake zuƙa yana hurawa lokaci zuwa lokaci, a ɗaya hannun nasa kuma wayarsa ce da hasken screen ɗinta ke haska fuskarsa yayin da yake danna number guda cikin contact list ɗinsa ana kuma maimaita masa abu guda daga daya bangaren wayar. "The number you're trying to call is currently switched off, Please try again later." (Lambar da ake kira a kashe take, a sake gwadawa bayan wani lokaci.) Hannunsa ya sake danna number yayin da aka sake maimaita masa maganar. "Jawad?? For real? Kai kadai anan sama? Na zata wasa su Sa'id suke da suka ce kana nan ai." Wani abokinsa da suke kira da Haro ya ƙaraso daidai wajen yana zama daga gefen kujerar, bai ce dashi komai ba don haka ya sake kallonsa yace. "Naji rumours din, it was bad man, amma bai kamata hakan ya dame ka ba, kar ka jawowa kanka depression." Sai a yanzu Jawad ya juyo ya kalle shi, ya san abinda yake magana, jita-jitar dake yawo cewa za'a cire mahaifinsa daga kujerar Minister, har a tunaninsa abinda zai dame shi kenan? To me zai same su idan an cire shin tunda ko a yanzu sun tara dukiyar da ya san har su mutu ba zata kare ba, ya zuki hayakin ya fesar sannan yace. "Kar Allah yasa a fasa cire shin, al'amarin wannan tsohon ya isa ya dame ni ne Haro? abinda yake gabana daban." Kan shishar Haro ya karɓa yana dariya sannan yace. "Pray tell." Sai kawai ya jefo masa wayar hannunsa shima sannan ya jingina da kujerar. Haro ya cafe wayar sannan ya kalli
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73