Skip to content

Chapter 56

Chapter 56

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

ji lokacin da Ma'aruf ya shigo ba ko kuma don haka ta ƙudirta a ranta cewa cikin gida ya shiga. Da wannan tunanin ta ninke sallayar tare da hijabin ta ajiye su a gefe, ta ɗauko wayarta don kiran su Amma, sai dai daga layin nata har na Aminu bai shiga ba, kuma bata son kiran Baba a wannan daren, don haka ta bari zuwa gobe, ta nufi wardrobe ɗinta don ta ɗauko kayan bacci, wata sabuwar doguwar riga ta dauko sannan ta dawo gaban gadon don ta canja. Ɗankwalinta ta fara cirewa ta ajiye shi a kan gadon sannan ta shiga kokawa da zip ɗin rigarta, amma ga mamakinta saiya riƙe ɓam yaki ko motsi, gashi ciwon hannunta ba zai bari ta rike shi da kyau ba, na dama kuma yaki ƙarasawa can saman, dama tunda tazo saka kayan ta kula yana da matsala amma bata yi tunanin ta kai haka ba. Har sai da hannunta ya ƙage ta tsaya ta tattaro dukkan ƙarfinta sannan ta cigaba da jansa, kafin a lokaci guda kamshin turaren Ma'aruf ya shiga hancinta. *** A waje bayan Faruk ya tafi, sun dade a tsaye shi da Ishaq suna hirar tarin wasu abubuwan da suka shafe su wanda yawanci duk akan matsalolin dake baibaye da rayuwar Ma'aruf ne, sai kuma zancen Abdurrahim, ƙanin Ma'aruf ɗin dake can New York wata makaranta ta Bebaye irinsa, (Rochester Institute of Technology.) Don Baffa ya gaya musu cewa saura watanni biyu kawai ya kammala ya dawo gida. Bayan wannan sun tattauna zancen Hamida ma inda Ishaq yayi-yayi da Ma'aruf akan ya ɗauko yarinyar daga inda ya kaita ya dawo ta ita cikinsu, amma ya ɓata bakinsa a banza don ya riga ya rantse cewar Ruƙayya ba zata taɓa sanin inda Hamida take ba sai ya kammala da al'amarinta gaba ɗaya, ko shekaranjiya da Mami taso yi masa zancen itama kai tsaye ya dakatar da ita ta hanyar gaya mata cewa lokacin da zai ɗauko ta bai yi ba, don haka itama taja bakinta tayi shiru, don dukkaninsu sun sani cewar idan har ya furta abu, Baffa ne kawai zai iya sauke shi daga kansa, amma ko da suka yi magana da Baffan shima cewa yayi... "Wannan zancen naku ne kai da mahaifiyar yarinyar Muhammad, duk abinda kuka yanke idan har ba kuskure bane mu namu addu'a ne tunda kune kuke da iko akanta fiye damu. Kuma kowannen ku yana da ikon da zai riƙe ta, duk da dai a matsayinta na mace an fi so ta zauna a gaban mahaifiyarta, amma idan har za'a samu matsala wajen tarbiyarta ko lafiyarta kamar yadda aka fara yanzu, to zamanta a wajen naka zai fi." Wannan zancen na Baffa shi ya bashi ƙwarin gwiwar cigaba da shirin da yake da niyya wanda yake jiran lokacin kawai. Daga ƙarshe kuma suka ƙare da zancen ginin su wanda Ishaq ɗin ya gaya masa cewar ya samo wasu sababbin masu ginin da zasu fara aikin tunda Ma'aruf ya sallami waɗancan. Kuma baiyi mamaki ba da Ishaq ɗin baiyi masa zancen Amina ba, don ya riga ya fahimci cewa ba sai yayi ɗin bane, akwai wasu abubuwa da ba lallai sai sun furta su a tsakaninsu ba, wasu abubuwa ne da ƙarara kowannensu ke ganewa idan ɗayan yana ciki, don haka a yanzu ma Ishaq ya riga ya sani cewar ya riga ya yanke koma wane irin hukunci ne game da zamansu ba sai sun ɓata lokaci wajen biya shi ba. Da haka suka yi sallama, sabon maigadin da ya samo ya sake budewa Ishaq gate ɗin gidan, shi kuma ya koma ciki. *** Yayi sakanni biyu tsaye daga bakin kofar yana kallon yadda take kokawa da zip ɗin rigarta kafin ta ankara dashi, watakila jikinta ne kawai ya bata cewar yana daga bakin kofar, don a lokaci guda ta juyo da sauri tana kallonsa, fararen idanunta suka zare akansa yayin da a lokaci guda ta saki hannayenta duka biyun suka sauka a gefenta. "I'm sorry banyi sallama ba ko?" Sai ta girgiza kanta. "Babu komai ban ji lokacin da ka shigo bane." Ya cije lebbensa tsaye a jingine kofar kafin yace. "I'm sorry bana so in ɗauki lokaci ne kiyi bacci." Idanunsa na kallon fuskarta da yaga kamar tana ƙoƙarin kore wani abu wani abu mai kama da mamaki kafin ta tambaya. "Wani abu kake so?" Lokaci ne ya tsaya cak a cikin kansa da wannan tambayar yayin da fatar bakinsa ta bude kamar zai ce wani abu yana kallonta, tsakaninta da Allah ta fadi hakan ba tare da ta san tarin ma'anonin da za'a iya fitarwa daga kalaman nata ba, ganin tana cigaba da kallonsa yasa ya sake cije leɓɓensa na ƙasa sannan ya girgiza mata kai. "I want to treat your hand." (Hannunki zan duba.) Ya faɗa yana kallon yadda fuskarta ke nuna tarin yanayi kala-kala, ƙafafunsa suka tako cikin ɗakin a hankali zuwa inda take tsaye, kuma kamar a wani shiri sai iska ta buso daga windon da yake fuskantar su daidai lokacin da ya tsaya a gabanta, kuma bai ɓata lokaci ba yasa hannunsa ɗaya ya ɗauko nata mai ciwon nan. Gabaɗaya tsawonta iya kafadarsa ne, gashin kanta da babu dankwali ya taso sama yana shaida laushinsa, da zai iya a wannan lokacin zai zare ribbon din data ɗaure shi ne don ya sauko kafadunta yaga iya tsawonsa, amma sai ya daurewa wannan tunanin ta hanyar kallon yatsun hannunta da yake riƙe dasu. Ya san cewa shi mutum ne da yake ƙarbar respect daga ɗimbin mutane, kuma a iya kokarinsa yana kokarin ganin ya kyautatawa duk wanda ya shigo hanyarsa, da kuma kaffa-kaffa musamman a yanzu don ganin bai yi wani abu da zai iya cutar dasu ba, amma Allah ya sani bai taɓa haɗuwa da wanda a lokaci guda yaji zuciyarsa na tsoron ciwonsa akanta ba irin yarinyar nan, yarinyar da a baya bai damu da yadda zaiyi kokarin samun bayanin da yake so daga gare ta ba, Wani bandeji ne mai haɗe da audugarsa a jiki, don haka magani kawai ya ɗiga a jiki daga cikin wata ƴar kwalba sannan ya rufe ciwon nata dashi, ai kuwa ta runtse idanunta a lokaci guda tana jin zafin na tafiya har tafin ƙafarta. "Zuwa safe zaki iya cirewa sai a saka wani, insha Allah a kwana biyu zai warke." Ya faɗa yana sakin hannun nata, kuma duk da zafin da take ji haka ta shiga daga kanta da sauri alamun ta fahimta. Ya rufe maganin sannan ya wuce ta zuwa wajen da mudubin ɗakin yake, ya ajiye roll ɗin plaster da kuma kwalbar maganin akai sannan ya juyo ya dawo inda take tsaye tana cigaba da danne ciwon. Kuma bata yi wani tunani ba lokacin da ya tsaya a bayanta, dab da ita sosai, don haka da sauri ta juyo gabadaya ta kalle shi amma sai ya saka hannayensa duka biyu akan kafaɗunta ya juyar da ita. "Zan taimaka miki da zip ɗin ne..." Ya faɗa muryarsa na fitowa dab da kunnenta sosai, kuma kafin tayi ƙokarin kamo tunaninta muryar tasa ta cigaba da cewa. "Akwai abubuwa da yawa game dani a zuciyarki na sani, amma ina so a saman komai kisa a ranki cewar ba zan taba cutar dake

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73