Skip to content

Chapter 41

Chapter 41

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

gama lissafawa, wata budurwa ta shigo cikin kitchen ɗin hannunta dauke da wani katon food flask, doguwar riga ce a jikinta shade din albasa (onion color) da wani dan karamin mayafi data yafa a sama maroon colour. "Bata nan kitchen ɗin?" Ta sake tambaya tana ƙarasowa ciki fuskarta ɗauke da murmushi, a lokaci guda taji wani abu ya ratsa ta har tafin kafa, don babu wata kwana-kwana ta gane ƙannensa ne suka zo, kuma shigowar sa kitchen ɗin ita yake nema. Taga yadda hannayensa ke motsawa a cikin gashin nasa alamar bai san me zai ce ba lokacin da yarinyar ta tafi tana ajiye food flask ɗin can kusa da gas cooker. Sai kawai tayi karfin halin ɗauko wani jug a gefe sannan ta buɗe ƙofar store ɗin ta fito, zuciyarta na gaya mata ai tunda a yanzu ƙirgen ya tashi daga su biyu ta tsira. "Sannu da zuwa." Muryarta tasa duka su biyun juyowa suna kallonta, yarinyar ta washe baki cikin fara'a sannan ta taho da sauri ta rungume ta. "Ashe kina ciki, Barka da safiya." Sai da zuciyarta ta buga a kirjinta saboda mamaki, mamakin da ta daure cikin nata murmushin itama tana rungume ta. "Sunana Samira, tare muke da Surayya da Munaya suna falo, fatan kin tashi lafiya?" Ta faɗa bayan ta janye daga jikinta, sai ta ɗaga kai da nata murmushin mai fadi ta amsa da. "Lafiya kalau, nagode sosai." A lokacin ne kuma idonta ya kai kansa, ta san kallonta yake tun da ta fito don tana jin tasirin yadda idanun nasa ke shiga jikinta, gabanta ya faɗi sakamakon haɗa idanun da suka yi, kallon da yake mata mai cike da nazari ne, kamar yana saka scanner cikin idonsa yana son tantance ta. Kuma a lokacin ne babban al'amarin safiyar ya faru, bakinsa ya motsa da wani guntun murmushi yana rufe idanunsa ya buɗe su akanta, kamar ma ƙifta mata idanun yayi, abinda kafin ta gama tantacewa ya juya ya bar kitchen ɗin. A kusa da kafafunta taji cikinta ya faɗi gabaɗayansa har ƙasa tsabar tsurewa da kuma mamaki, ilahirin jikinta ya ɗauki rawa kafin muryar Samirah ta cigaba da magana cikin tunaninta, sai ta hango kanta ta tsugunna tana ƙoƙarin tattara jikinta waje ɗaya kafin ta iya fahimtar me take cewa. "Abinci muka kawo muku kafin mu fara zagayen gidan sauran amaren, gamu nan da kaya fal cikin mota kowacce tayi mantuwarta... Na san kema kinyi taki ko?" Bata gama daidaita tunaninta ba, don haka bata san sanda ta ɗaga mata kai ba tace. "Ina tashi nima naga na manta chager wayata." "Ai sai a hankali ma zaki yi ta neman wasu abubuwan, Ya Shukra har da system ɗinta gabadaya ta manta kuma project ɗin masters take yi..." Ta gyada kai tana ƙoƙarin murmushi sanda wata ta ƙaraso cikin kitchen ɗin itama, watakila itace zasu yi sa'anni ɗaya ko kuma ace ta fita da kadan, tana da glasses wanda kana gani ka san medicated ne, ita kuma bakar abaya ce a jikinta wadda ta fito da ɗan hasken fatarta don ita ba fara ce sosai kamar Samiran ba, zata iya jera su layi ɗaya da yayan nasu. "Ashe kina nan matar Yaya..." Ta fada da nata murmushin itama tana karasowa kuma ga mamakin Amina itama sai kawai ta rungume ta tana fadin. "Oyoyo, we welcome you into the Family dear, jiya mutane basu bar mu mun ganki ba." A yanzu ƙwaƙwalwar Amina kwancewa tayi gabadaya, don ita ko a gyangyadi bata taba kawowa haka abubuwa zasu kasance ba, ko jiya sai da su Aunty Ma'u suka gaya mata cewa tayi taka-tsan tsan da ƴanuwansa. "Ƴan gayu ne na karshe Amina, kija jikin ki ki tsira da mutuncinki..." Haka Aunty Ma'un ta raɗa mata a kunne. To me yasa ne komai yake faruwa saɓanin tunaninta ne? Ko dai akwai wani abu da ba daidai yake tafiya bane? "Sunana Munaya.." Ta kara faɗa tana miko mata hannu, sai tayi karfin halin mika nata tana murmushi itama. "Yanzu zaki ganta kamar normal mutum amma idan kika tabo wajen karatu zaki fara tunanin aljana ce." Samirah ta faɗa tana kallonta. Sai kawai ta girgiza kanta. "Yarinyar nan ta raina ni da yawa, kar ki yarda da ita." "Wallahi da gaske nake Aunty Amina idan kina da ƴanuwa a Buk ki tambaye su kowa zai ce miki ya san GB (Genius Brain) haka suke ce mata, irin ƙwaƙwalwar su ɗaya da Yaya." Munaya ta girgiza kanta tana murmushi. "Astagfirullah, Allah ka tsare ni daga sharrin yarinyar nan, zo muje ku gaisa da Surayya, tana can tana ta aikin pressing waya." Da haka Munayan taja hannunta suka yi hanyar fita, Samurah ta biyo bayan su. A falon wadda suka kira da Surayya na zaune kan kujera mai zaman mutum ɗaya tana ta faman danna wayar hannunta, daga ƙasa kuma wasu ƴan mata biyu ne su ma da kallo daya zaka yi musu ka san ƴan aiki ne, gabansau dauke da wasu trays din dake dauke da food flask har hudu da kuma jug na lemo shima kala biyu, alamu su suka shigo dashi daga motar da Samirah tace suke. Kuma da shigowarsu Surayyan da zata ce sun yi sa'anni da Munaya ta dago da nata murmushin itama sannan ta ajiye wayar ta taho ta rungume ta, a yanzu Amina taji kamar ta saba ne ma da yanayin gaisuwar tasu. "Na san ma wannan mai bakin ta gaya miki sunana koh?" Ta tambaya tana kallon Samirah da tayi wajen ƴan aikin nan tana gaya musu akwai wata baƙar keda da badu shigo da ita ba. "Nima tun kafin in shiga ta gabatar dani ai." Cewar Munaya tana neman waje kan daya daga cikin kujerun. Amina ta daga kai tana murmushi. "Ta fada min, naji dadin ganin ki kuma." "Haba dai godiyar tamu ce ai, na san na samu wajen zuwa idan Mami ta matsa min da zancen waya, da fatan dai ba zaki damu ba idan kina ganina a compound din gidan nan." "You dey mad? Kike fada a gaban yarinyar nan? Kema kin san kamar Mamin taji ne ai." Cewar Munaya tana dariya, Surayya ta kalli Samiran dake tsaye tana jinsu. "Ta gaya mata mana, itama ai tana da nata secret din a wajena." "Ba dai zancen wannan cake pack din Ya Salma bane, wlhy sai inyi confessing in fada, tunda idan nayi cake din ai har da Mamin ake ci ace yayi dadi." "What? Kayan Salman kika dauka? Amma bata sani ba har yanzu ko?" Cewar Munaya. Surayya ta koma kan kujera tana sake ɗaukar wayarta. "Ki bari kawai, kuma wallahi guda daya ne a cikin kayanta, ranar da ta nema ta rasa, inaga Yaya Ishaq za'a kira yayi aikinsa a gidan nan." Suka kyalkyale da dariya gabadayansu yayin da Amina ke tsaye har yanzu da jug din nan data dauko a hannunta tana taya su da murmushi. A lokacin ɗaya yarinyar nan ta dawo daga waje. Samirah ta karbi kedar tana miko mata tace. "Gashi Aunty Amina, cupcakes ne na san zaki iya yin baƙi a cikin satin nan, wadannan kuma abinci ne breakfast da Dinner, naga yayan ma ya fita, flask din da na kai Kitchen kuma miya ce a ciki, murfin suka balla yanzun nan da

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73