Skip to content

Chapter 58

Chapter 58

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,196 words 0 views Progress saved
Download Book

ce jikin nasa da sauƙi kar ki ɗaga hankalinki, yanzu mu ma zamu shiga mu ganshi..." Zancen ya katse a lokaci guda da Amina ta nemi wayar a kunnenta ta rasa. Hajiya Kilishin da a yanzu ke tsaye akanta riƙe da wayar tasa hannu ta ɓare bayanta ta fito da batirin ta jefar dashi gefe, sannan ba tare da ɓata wani lokaci ba ta karya wayar gida biyu itama. Kuma taku biyu kawai ya mayar da ita baya kan kujerar da ta taso, ta cigaba da kallonta har a yanzu da ragowar murmushin nan a fuskarta kafin muryarta ta fito cikin wani irin sauti da yake ainahin halittar ta, sautin da yake manne a kirjinta tare da zuciyarta dake ƙawata mata tarin hanyoyin da kullum suke ɓullewa ga nasararta, sautin da a duniya kaf, mutum huɗu ne kawai suke sanin da kasancewarsa, sai a yau da ta zabi Amina ta zaman cikon ta biyar ɗin, cikon da take fatan zai zama mataki na ƙarshe da take da yaƙinin zai kai ga nasararta. "Barka da shigowa cikinmu Amina." Kalamai biyar ɗin data furta kenan wanda ta lissafa cewa adadinsu ya dace da lambar matsayinta, murmushi kan fuskarta cika taf da tarin kalaman da take shirin ɓare mata a yanzu wanda zasu sa ta fahimci wacece Kilishi tun daga tushe da kuma dukkanin abubuwan data aikata a rayuwarta. *** Wane shiri Ma'aruf ke yi akan ƴarsa Hameeda da kuma Ruƙayya? Me ya yankewa zuciyarsa akan Amina da har Ishaq ya fahimta? Ku gaya min ina rayuwar gidan nan ke tafiya? Munaya and Ishaq, me kuke tunani? Hajiya Kilishi... Ina gaya muku har yanzu sunan matar nan kawai kuke ji, next chapter zata buɗe muku abubuwa da yawa game da ita... Babi na gaba zai nuna muku me ake nufi da ainihin kissa da kisisina irin ta mata kamar Kilishi, wanda suka yarda cewa kowacce mace zata iya samun duniyar da take so a tafin hannunta... Ba boka ba malam! #Aysha shafi'ee. #fikrawriters #FararWuta. BABI NA SHA UKU. ~~~~~~~ There's a part of me that likes to beleive everything will be okay, then there's another that breaks down every chance it gets. - Unknown. ** Dukkan wata ma'ana ta mamaki da kuma tashin hankali shine yadda fuskar Amina tayi a lokacin da take kallon Hajiya Kilishi. "Taɓa Aminu dana sa akayi tsaraba ce ga ƙwaƙwalwar ki Amina don ki saurare dukkan abunda zan gaya miki da kyau, ki yarda da dukkan kalamaina sannan kuma zuciyarki ta tabbatar da cewar Kilishin da zaki sani a yanzu da gaske take al'amuranta." Tayi shiru bayan ta faɗi hakan hannunta na jawo wayarta da ta ajiye a gefe, babu ƙarar kiran dake shigowa alamun a silent ta saka ta. "Ya akayi Awwalu?" Muryar tata da ta canja tar ta tambaya cikin wayar bayan ta kara ta a kunnenta... Har a lokacin Amina bata motsa daga yadda take zaune ba, idanunta basu canja daga yadda suke kallonta ba, sannan ƙwaƙwalwar ta bata wartsake daga mamakin dake zagaye da ita ba, Ƙirjinta dake ɗagawa cikin numfashi mai nauyi shine kaɗai abinda zai sa ka san cewa idan ka taɓa ta ba zata tafi ta faɗi ba. Wataƙila magana guda ɗaya aka fada a cikin wsyar wadda ta gamsar da Hajiya Kilishin, don bata ƙara cewa komai ba ta kashe ta kawai ta sake mayar da ita gefenta, sannan ta sake kallom Aminan, hasken fuskarta na yayewa alokaci guda "Duk abinda zaki ji a yanzu ya zama tsakani dake ne Amina, idan ba haka ba a ƙarshen zancena zaki gane abinda zai faru idan har kika sako mutum na ukun mu a wannan zancen koda kuwa mahaifiyarki ce. Da farko mu bar duk wani kewaye-kewaye mu tafi ga abinda yasa kika shigo gidan nan, tunda ni dake dama duk wani mai hankali mun san akwai dalilin aurenki da Ma'aruf..." Ta gyara zamanta kaɗan sannan ta cigaba... "... Cire mahaifinki ki ajiye shi a gefe, amma ko mahaifiyarki ta san ruwa baya tsami banza, a muryarta kawai na fahimci cewa irin zurfin tunaninta kika ɗauko Amina, ku duka kun san ba kowacce mace ce zata taka irin matsayin da kika taka a banza ba, zan ƙara tabbatar miki cewa shigowar ki cikin gidan nan dama cikin rayuwar Ma'aruf wani abu ne da ba don taimakona ba, ba zaki taɓa samunsa ba ko zaki mutu sau ɗari ki dawo, saboda a rana guda zamu iya samun mata dubu da zasu yarda da auren Ma'aruf ko da kuwa ciwon da yake dashi yafi haka tasiri, don ba'a wayewar kowacce rana mata ke samun namiji irinsa ba. Kuma shi kansa Amina, da an bashi zaɓi na sani tsaf zai kawo macen da zata fi ki a komai don irinsu kawai ya sani kuma yake mu'amala dasu, amma sai nayi amfani da ƙarfina da kuma ikona nace ke kaɗai za'a bawa wannan matsayin wanda dole kowa ya yarda da hakan, don haka duk wata soyayya da kika ga kina samu daga mutanen gidan nan dama shi Ma'aruf ɗin da ya fara saurarar ki duka saboda ni suke miki ba don komai ba, ni na ɗora su akan turbar zuciyarsu ta so ki kuma hakan ya zame musu kar dole." A yanzu Amina tayi ƙoƙarin sunkuyar da kanta tana kallon hannayenta dake faman rawa suna kakkarwa akan cinyarta, zuciyarta na bugawa ne kamar zata faso kirjinta ta fito yayin da kowanne kalaman Hajiya Kilishin ke shiga kunnenta da tsantsar rudani da kuma tashin hankalin da akace ba'a saka masa rana. Kuma shirun da Hajiya kilishin tayi baiyi tsawon da zata iya fitar da komai ba lokacin da muryarta ta cigaba da cewa. "Bari in ɗauko miki komai tun daga farko Amina, ta haka ne zaki fahimci zance na. Lokacin da ina yarinya a wajen kakata na girma, ita ta raine ni tun daga lokacin yaye har girma na, a wajenta na samu tarbiyya da kuma tarin wayo da dabaru irin na zaman duniya, har yasa tun a ƙananun shekaru ina iya kallon rayuwar mutum na bashi shawara mai kyau da zata ɓulle ga matsalolin sa, hakan yasa ƙawayena dama mutanen unguwar a lokacin suka laƙaba min sunan ƴar baiwa. Bayan wani lokaci sai wannan kakar tawa ta rasu don haka dole na koma gidanmu inda naje na tarar da tarin ƴanuwana, don mahaifinmu matansa uku ne kuma ƙaramar cikinsu wato mahaifiyata ce kawai mai ƴaƴa tara, sauran biyun akwai mai goma sha ɗaya da kuma sha uku. Rayuwar gidanmu ba dadi sam, saboda a wajen kakata na saba komai namu mu uku ne kawai dani da ita da kuma wani almajirinta Awwalu da take riƙewa, don haka sai rayuwar gidan yawan tazo min a wuya, gashi babu ruwan kowa dani hatta mahaifiyata kuwa da hankalinta yafi karkata kan yayyena da suka fi girma a lokacin, don haka da lokacin shigata babbar sakandire yayi sai na samu mahaifina nace ya maidani makarantar kwana don zata fi mun daɗi, al'amarin kamar ba zai yiwu ba da ƙyar da rabo dai na samu na tafi. A can na hadu da ƙawayena biyu kuma ƴanuwan da zan iya kira da na jini wato Salamatu da Saratu, wadannan mutane biyun Amina sunyi min duk wani gata a lokacin zama na a

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73