Chapter 62
Chapter 62
masa mun dawo gida, gobe kuma zamu tafi jigawa gidan wannan ɗanuwansu Fatiman mai gyaran karaya, saboda duka ƙafafun nasa biyu sun karye Amina." Sautin kukan da ya fito daga bakinta shi yasa Amman cewa. "Ba kuka zaki yi masa ba Amina, addu'a zamu yi Insha Allahu zai samu sauƙi don ance shi mutumin ya iya aikinsa, ba za'a haɗa dana asibiti ba." Muryar Amman dake lallashinta itama a karye take kawai, ta sani suna da kuma matsayinta na Uwa shine abinda ke rike ta daga nata kukan. "Ku duka zaku tafi Amma?" Tayi ƙokarin tambaya ta cikin kukan muryarta a rarrabe. "A'a, dani da Baba da kuma Fatiman da zata kaimu gidan zamu tafi, su Maryam suna nan saboda makaranta, ita kuma Hajiyan Fatiman saboda jinyar Inna (kakar Fatiman) ne ba zata samu zuwa ba." Sai da tayi wata ajiyar zuciya mai nauyi sannan tace. "Ina Aminun?" "Bacci yake Amina, tun jiya sai yanzu bayan magaribar nan sannan ya samu baccin, idan ya tashi na kira ki, wannan nambar waye?" Bata amsa ba don bata san me zata ce ba, kuma shirunta ya bawa Amma amsarta don haka sai tace. "Addu'a zaki yi tayi masa Amina, kowanne ɗan adam baya wuce ƙaddararsa, komai zai zo da sauki insha Allah." Kalaman kaɗai sun isa su kara tsoratar da Amina, don ta san idan har Amma zata faɗi haka to al'amarin ba ƙaramin abu bane, don komai tsananin rashin lafiyar mutum Amma bata zuzuta shi haka, balle ma akan Aminu da yake namiji, don haka bata san lokacin da bakinta ya ƙara talewa da ƙoƙarin yin kukan da har yanzu take dannewa ba. "Zan saka Maryam ta kira ki da safen kafin mu tafi, su can gidan Kawu Malam zasu koma kafin mu dawo." Ɗaga kai kawai take kamar Amman na kallonta yayin da sautin kukan ke shaƙewa a ƙirjinta yana fitowa a kakkatse, Allah ya sani rabonta da irin wannan kukan tun Maryam bata da lafiya, lokacin da aka nemi kuɗin maganinta aka rasa, tana kallonta a kullum tana tunanin mutuwa zata yi. Ma'aruf yasa hannu ya karɓi wayar daga wajenta bayan sunyi sallama, ya maida ita aljihunsa, bata kalle shi ba har yanzu tasa bayan ɗaya hannunta tana ƙoƙarin share hawayenta, da hannun da ya mayar da wayar ya sake riko ɗaya hannun nata ya tsayar da ita daga goge hawayen, sannan a lokaci guda ba tare da ta ankara ya jawo ta jikinsa, karo na farko ya rungume ta, hannunsa ɗaya ya zagayo wajen ƙugunta yayin da kanta ya samu mazauninsa a kusa da wuyanta. "Kar ki maida shi zai cutar dake... Just let it out." Muryarsa ta faɗa a cikin kunnenta da wani sauti daya shiga dagargaza dukkan wata jijiya ta dauriya a jikinta. Kuma a karo na farko Amina ta manta komai akan Ma'aruf ta sunkuyar da kanta a jikinsa don babban abinda take buƙata kenan, kukan da sautinsa kaɗan ne ya suɓuce daga bakinta yayin da jikinta ke girgizawa a cikin hannunsa. *** Bayan kwana biyu. "Kin shirya?" Ma'aruf ya tambaya yana kallon Amina data fito riƙe da wata ƴar ƙaramar jaka a hannunta da kuma wani madaidaicin basket, doguwar riga ce a jikinta ta baƙar abaya, ta yafa baƙin mayafin kawai akanta ba tare da ta saka ɗankwali ba, tana tsaye daga hanyar koridon dakunan tana cakuɗa yatsunta cikin junansu, har yanzu ta kasa yarda da abinda yazo dadaddare ya gaya mata jiya cewa ta shirya zasu je jigawa a yau. Jiya da safe a wayar tasa suka yi waya da Amma ta shaida mata lokacin tafiyarsu wanda bayan hakan tayi ta binsa da kallo tana so taji yace wani abu amma bai faɗa ɗin ba har ya fita, ya barta a zagayen halin da take ciki, kuma Allah kaɗai ya san yawan abubuwan data saka ta kwance a cikin kanta a jiyan wanda duk iya tunanin nata yana ƙarewa ne a gaɓar da bata san yadda zata yi ba. Haka ta yini har a jiyan tana share hawaye duk lokacin da ta tuno cewa duk irin halin ciwon da Aminu ke ciki saboda ita ne, saboda itan da bata san yadda zata budi baki ta gayawa wani ba, ko da Ma'aruf ɗin ne kuwa tunda shi kansa babu alamun yana da wata masaniya irin wadda ita ta sani yanzu akan Mamin, duk da cewa bata gama sanin ainihin abinda take nufi game dashi ba ko kuma shi nasa ra'ayin akanta. Sai da daddare bayan ya dawo ne kawai yace ta sako mayafinta zasu shiga cikin gida, wajen Mami suka fara zuwa kamar yadda suka zata, kuma gaishe ta kawai suka yi kafin ya furta abinda yasa kowannensu mamski daga ita har Hajiya Kilishin. "Gobe zamu wuce Jigawa Mami, na san kin samu labari, brothern ta ne ya gamu da hatsari zan kaita ta dubo shi." Har yanzu tana jin nauyin yadda idanun Hajiya kilishi suka dinga kallon fuskarta, tana jin tafiyarsu a ko'ina na fuskar tata, yadda ta dinga kallonta da wani irin yanayi da yake nuna mata cewa itama a lokacin taji zancen, da kuma yadda tata zuciyar ta dinga bugawa har sai da taji kamar ta tsugunna ƙasa ta ɗauko ta lokacin da suka miƙe tsaye, don tsabar tsoro ƙirjinta fayau ta dinga jinsa kamar yadda jikinta ya zama kamar fallen takarda har lokacin da suka tafi ɓangaren Hajiya Maimuna, idan acan ma suka sha addu'ar Allah ya kiyaye hanya kamar yadda Mamin tayi tata. Jiya haka ta kwana tana juyi akan gado, da asuba kuma tunda tayi sallah bata koma ba, don yace mata ƙarfe takwas zasu tafi a yau ɗin zasu je su dawo kamar yadda ya tsara. Abincin breakfast ɗin da tayi ma bai ci ba don yace mata azumi yake yi kasancewar ranar Alhamis ce. A yanzu ya shigo daga wajen maigadi ne da ya gama wanke masa motarsa, yana tsaye daga bakin ƙofar falon yayin da karar yadda maigadin ke share ruwan wankin motar daga waje ya cika falon. "Kin shirya a haka?" Ya ƙara tambaya yana kallonta, sai ta sunkuya ta kalli kayan jikinta sannan ta dago ta kalle shi tace. "Eh na shirya." Shi nasa kayan dogwaye ne kalar sararin samaniya, ya saka hula wadda ta dace dasu, da ace zuciyarta a nutse take ta sani tsaf zata tsaya yabawa yadda kayan suka karɓe shi amma a yanzu ba abinda ke gabanta kenan ba, tashin hankalin dake kwance a ƙasan zuciyarta ya isa ya binne ta da ranta. Sai kawai ya taho gabanta riƙe da mukullin motarsa a hannu, kuma bata matsa ba, don watakila a yanzu ta saba dashi a kusa da ita, kar a lissafa da shekaranjiya lokacin da ya rungume ta, wannan don ba'a cikin hayyacinta take ba kowannensu ya sani. Hannunsa taji ya sauka akan gashinta da ya fito ta gaba kafin yace. "Shi wannan ba'a rufe shi?" Zuciyarta ta buga yayin da wani abu ya tsarga tun daga saman kan nata har zuwa tafin ƙafafunta amma ta haɗiye shi, sai ya matsa baya kadan sannan yaba cigaba da kallonta yace. "Bana son wani yaga gashinki." Bata ɗago ta kalle shi ba amma kalaman sun daki zuciyarta ta yadda duk tarin hargitsin dake ciki sai da suka girgiza. girgizawar da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73