Skip to content

Chapter 45

Chapter 45

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

lokacin kuma kudin bai kai ba, ita ta daure musu tunani. Don basu san yadda za'ayi alert ya shigo da wani adadin kuɗi ba alhali ba hakan aka turo ba. Anan suka tsaya kasancewar magriba ta taho kusan kowa a Office din ya tashi tunda dama a ƙa'ida ƙarfe biyar ne lokacin tafiyar kowa. A wajen Hamida ya daɗe bayan yayi sallar magaribar, kuma wannan karon har nuna alamun cewa zata biyo shi tayi, ransa ya cika da farin ciki kafin ta ƙarasa da cewar zata bishi ne ya kaita wajen Maminta, kuma Allah kadai ya san sau nawa ya zura hannunsa cikin gashinsa ya fito dashi kafin ya iso gida, don game da al'amarinta bashi da wata mafita ko kaɗan, abu ɗaya ya sani shine ba zai taɓa iya sake rabuwa da ita ba ko da me Ruƙayya da iyayenta zasu tunkare shi. Ya tuno wayar da suka yi da Ahmad kanin Ruƙayyan a jiya, yaron bashi da hankali ya daɗe da sanin hakan, tunda har sunyi magana da Ashraf ya gaya masa cewa zai neme su bai ga dalilin da zai sa shi ya sake kiransa ba, kuma yadda yake masa magana ma ji yayi idan akwai wani mataki da yafi na haukan, zai iya saka shi a wannan layin, don haka ƙarara yayi masa gargaɗin cewa zai iya sawa a kama shi idan har ya sake kiransa da wannan batun. Ya riga ya sani cewa duk cikinsu babu wanda zai iya ja dashi don yana da da hujjar da zai kaisu ƙasa ko a gaban waye za'a tsaya, bama wannan ba ya sani cewa babu inda Ruƙayyan zata je ta samo karfin halin da zata iya fuskantarsa a yanzu, tana yawo ne da nauyin waɗannan kalaman ɓoyayyiyar yarjejeniyar da suka yi kamar yadda koda da rana guda shima bai taɓa manta su ba. Ya isa gida bayan ya tsaya a wani masallaci yayi sallar isha'i, ya shiga da motarsa ciki sannan ya fito ya rufe gate din yana takaicin yadda sai wani satin zai samu maigadi kamar yadda kamfanin suka shaida masa. Kuma bayan ya ɗauko wayoyinsa biyu daga cikin motar ya dade tsaye a wajen yana waya da Ishaq, a yanzu haɗuwarsu ta ɗanyi wuya, yana ta yawon zuwa Abuja ne akan wani workshop da suka fara a kotun tasu, don haka a cikin satin ma sau daya kawai suka haɗu. Magana suke tayi akan gininsu, wasu filaye da suka siya a Lamiɗo Cresent ana musu gini iri ɗaya, bayani yake yiwa Ishaq ɗin cewa zasu canja masu gini don na yanzun an basu kudin kaya mai kyau amma sun siyo wani siminti da bashi da kyau har wani waje a cikin ginin Ishaq din ya rufta. Daga karshe suka tsaya akan Idan ya dawo zasu fara neman wasu ma'aikatan kafin suyi sallama da kalaman da Ishaq din ke gaya masa a mafi yawancin ƙarshen maganarsu. "Dan Allah ka kula B." Ya cije leɓɓensa yana kallon wayar, har yanzu Ishaq bai yarda dashi ba ya sani, gani yake a kowanne lokaci wani abu zai iya faruwa saboda yanayin ciwon nasa, amma shi baya jin hakan, akwai abubuwan da yawa a gabansa amma baya jin sunyi yawan da a cikinsu zai iya samun abinda zai canja yanayinsa, don haka yana amsa masa ne kawai don ko yayi bayanin ba zai yarda dashi ba. Ya kashe wayar sannan ya debo kayansa na cikin motar ya shiga ciki da ƴar karamar sallamarsa, babu kowa a falon amma ƙamshin turaren wutar daya kula kwana biyu ana yinsa a gidan ya shiga hancinsa. Yayi sallamar da babu mai amsa masa sannan ya cire takalmansa daga gefe ya taka zuwa ciki, zuwa hanyar korodon nan, fitilar dakinta a kunne take kamar kowanne lokaci irin haka idan ya dawo, ya jiyo motsinta daga ciki har da ƙara ma kamar wani abu ya fadi kafin ya zarce zuwa dakinsa. Wanka zaiyi ya fito ya shiga cikin gida, a can wajen Mami yake cin abincinsa kullum, kafin ya fita dai ya san watakila zai ganta su gaisa, amma zuwa lokacin da zai dawo ma ta riga ta kashe fitilar dakinta ta kwanta, ta kasan kofarta yake ganin hakan idan zai wuce. Ya isa ɗakin nasa lokacin da yake tuno maganganun Baffa sanda yake masa fadan rashin halartarsa wajen daurin auren nan, Baba Usman yana daga gefensa yake cewa. "... Idan kana tunanin zaka wulakanta yarinyar nan saboda iyayenta ba masu arziki bane Muhammad, ina so ka kalli iyayenka biyu da suke cikin gidan nan, daga ita Kilishin har Maimunan da ta haife ka, ka gaya min waye ya fito daga gidan mai kuɗi, ko kuma ni kaina da nake mahaifinka, ka gaya min gidan iyayena na gado da yake Bakori yaya yake, Mahaifina har ya mutu ɗakin kwanansa na ƙasa ne bai ko kai girman ɗakin nan ba ka sani. Saboda haka na daura aurenka da yarinyar nan ne saboda shaidar halayen kirki da aka yi mata ita da iyayenta, ba don abin duniya ba babu ruwana da abinda mutane ke faɗa wai kwarya tabi kwarya, zaman aure nutsuwa da kwanciyar hankali ake nema a cikinsa ba suna ba, game da aurenka na farko kaima shaida ne akan hakan, don haka ina rokonka kar ka bani kunya a karo na biyu Ma'aruf." Ya rufe idanunsa lokacin da ya saki ruwan shower akansa, indai Baffa zai kira shi da sunansa na asali ya sani cewa babban al'amari ne. *** Doguwar riga ce a jikin Amina ta atamfa kalar milk da sea green, ta daura dankwalin sannan ta yafa wani karamin mayafi shima kalar sea green ɗin da ya tsaya iya kafadunta, ba kwalliya tayi ba don babu ko hoda a fuskarta amma fatar ta da'a kwana biyu ta kara washewa sakamakon canjin ruwa tana haskawa tare da fararen idanunta, kuma kawai ta yafa mayafin ne don bata son fita haka, taji lokacin da Ma'aruf ya shigo, har wucewarsa ta gani ta kasan ƙofar dakin daidai lokacin da robar vaseline ɗin dake hannunta ta subuce ta fadi. Sati guda kenan da fara rayuwarta tare dashi amma har a yanzu duk sanda ya fita ya dawo sai taga kamar shine ganinta dashi na farko, taji zuciyarta ta kasa tsayawa waje guda duk da cewar wannan taraddain da take ji a farko ya fara tafiya, don bata san me yasa ba komai yazo ne sabanin tunsninta kuma lokaci yana saukaka mata abubuwa fiye da zatonta. Ko kaɗan bata ga wani yunƙurin cutar da ita a tare dashi ba, hasalima harkokin gabansa yake, da sun gaisa shikenan ba zai kara bi ta kanta ba. Ita kanta ta fara sabawa da gidan a yanzu, ranar da su Fatima suka zo sun taya ta sake kimtsa komai nata, sauran kayan kwalliyar nan da jakunkuna da takalman dake cikin Ghana must go ɗin nan duk an samar musu wajen daya dace dasu, ta basu kayan kwalliyar ma da yawa da kuma wasu daga cikin undies din. Sannan a kitchen ma sun jera komai a muhallinsa, store din ya zama babu komai sai iya abubuwan da ba lallai amfaninsu yazo a kusa ba, bata san adadin mamakin da tayi ba na yawan ganin kayan, don bayan wanda aka siya mata kusan duk wanda zai

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73