Skip to content

Chapter 5

Chapter 5

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

taso masa, amma a yanzu sati guda cur, har suka zo ƙasar nan Ma'aruf ba'a hankali sa yake ba, hakan yasa dole aka kwantar dashi a asibitin da alluran bacci wanda suka taimaka, ya farka cikin hayyacinsa yanzu. Don duk da cewar a police station suka je suka same shi, idanunsa kawai ya kalla ya san cewar ya dawo hayyacinsa tun kafin likitocin ma su gane, shi yasa ya matsu da fitowarsu a yanzu don yaje ya same shi, ya sauke maganganun dake zuciyarsa tun daga ranar da Mami ta kira shi muryar ta na rawa taje ya taho gida Ma'aruf ya shigo musu da gawar wani. Likitocin duka fito a daidai wannan lokacin, kuma bai tsaya jiran komai ba ya zagaya ta ɗaya hanyar da wandanda ba ma'aikata ba ke wucewa ya nufi wajen gadon. "Minti biyar! minti biyar kawai na fita Ma'aruf amma kayi tsalle daga asibitin nan zuwa police station!" Ya faɗi hakan da harshen hausa daidai sanda ya bankaɗa labulen da aka zagaye gadon. Dama abinda Ma'aruf ɗin yake jira kenan, ya riga ya sani cewar ya daɗe a waje yana kaɗa ƙafa yana jira likitocin su fita ya shigo da tarin ƙorafinsa, don haka hankalinsa a kwance ya ɗago da idanunsa ya kalle shi. "Kaima sani bana iya rike yunwa, na tafi in samu abinda zanci ne and you left me with nothing, ba dole su kaini police station ba." Ishaq ya girgiza kansa. "Ma'aruf ba a Nigeria muke ba, ko baka gane bane da ka farka? me kake tunani idan suka kama ka a ƙasar nan?" Maimakon ya bashi amsa kai tsaye, sai ya koma da baya a jikin gadon, ya zura hannayensa duka biyu cikin gashin kansa sannan yace. "Na sha gaya maka kana damuwa da yawa Ishaq, kana damuwa akan abubuwan da suke faruwa dama wanda basu zo ba." "Kuma matsalar kenan, kai da baka damuwar, baka damuwa da kanka balle kuma na kusa da kai, shi yasa har muka zo wannan matakin Ma'aruf! Mania!" Ya faɗi sunan mataki na karshe a cutar da Ma'aruf ɗin ke fuskanta, kuma ga mamakinsa, a lokaci guda Ma'aruf ɗin ya juyo ya kalle shi, sannan a cikin sakan biyu idanunsa suka haska da wani abu da Ishaq ɗin zai rantse da ubangijin dake busa musu numfashi cewar bai taba gani a idanunsa ba. Tsoro da kuma fargaba! Sai kawai ya girgiza kansa sannan ya cigaba da faɗin. "Shekara biyu da suka wuce a asibitin nan ko HypoMania test ɗinka basu kai ba, baka da lafiya amma babu wanda ya sani babu mai ganewa, muna ɓoye komai daki-daki don rayuwarka ta tafi daidai. Amma yanzu ka gaya min me kayi kafin mu taho nan Ma'aruf? Daniel ka yiwa dukan da har ya suma akan baiyi maka submitting takardu a office ba, ka dake shi har ya suma Ma'aruf sannan ka sako shi a mota ka kaishi gida, ka shiga dashi har falon Baffa kana gaya masa wai ka kawo shi ya kore shi daga aiki!" (Mahaifinsa.) Yanzu ka gaya min a duk kamfanin Bakori da ɗaukacin jama'ar da suka sanka, waye bai san kana fama da ciwon ƙwaƙwalwa ba Ma'aruf? Yanzu ka gaya min a duk kamfanin Bakori da duk ɗaukacin kewayen da mutane suka sanka, waye a yanzu bai san cewa kana fama da matsala a ƙwaƙwalwa ba? Waye bai san cewa kana da wannan nakasar ba Ma'aruf?" Muryar Ishaq ɗagawa take a lokacin da yake fadar hakan, sautin ta na fitowa cike da wani irin daci da takaicin duk abubuwan da yake faɗa din, kuma har a lokacin yana ganin adadin kifta idanun da Ma'aruf ke yi alamun cewa kowacce kalma tana bada ma'anar da yake son ya gane a ƙwaƙwalwar sa. Bai ce komai ba ya cigaba. "Ka san me ya fitar dani ɗazu? Ka san abinda yasa na bar ɗakin har kaje ka aikata abinda kayi?..." Ya tambaya kamar yana jiran ya bashi amsa. "... Office din likitan ka naje, shi ya kira ni personally Ma'aruf! Yayi min dukkan bayanin halin da kake ciki, kuma albishirin ka abinda kake so zai faru, idan komai ya cigaba da kasancewa yadda yake tafiya kana gab da rasa hankalinka gabaɗaya Ma'aruf! Kana gab da rasa komai gabaɗaya..." "And so what idan na rasa?!" Yadda Ma'aruf ɗin ya katse shi a lokaci guda da tasa sautin muryar ya bashi mamakin da har sai da ya haska a idanunsa. Kallonsa yake har a lokacin da nasa idanun da suka canja, yanayinsu na kara lumshewa kamar kodayaushe idan yana cikin ɓacin rai. "Nace sai me idan na rasa komai? Idan dai har ragowar lokacin da nake dashi zai bani dama na iya cimma abinda ke gabana sai me idan na rasa hankalina?" Sai ya girgiza kansa kawai yana cigaba da kallonsa. "Nasha gaya maka Ma'aruf ya mutu shekaru goma da suka wuce Ishaq, kaƙi ka yarda dani ne, amma Ma'aruf ya riga mutu, babu shi anan." Ya ƙarasa yana nuna ƙirjinsa, daidai lokacin da labulen dakin ya buɗe, wani bature ya leƙo fuskarsa a murtuƙe yace. "What the in the world are you two talking abou..." Bai karasa ba sakamakon kallon da su duka biyun suka juyo suna yi masa kowanne ransa a ɓace, sai kawai yayi sauri ya maida labulen ya juya, dukkaninsu suka yi ajiyar zuciya alokaci guda. Shiru ya ratsa wucewar sakan ɗaya, biyu, uku... kafin Ishaq ya ƙaraso a hankali ya zauna a gefen sa. "Kwana na nawa a asibitin nan?" Ma'aruf ya katse shirun da sautin muryarsa da ya koma daidai, mai zurfi dake fitowa can kasa. "Huɗu, you were unconscious for three days a Nigeria kafin mu taho." A hankali ya haɗiye yawu cikin maƙogwaronsa sannan ya ƙara tambaya. "Me Baffa yace?" "Ransa ya ɓaci sosai, ransa ya ɓaci fiye da duk yadda kake tunani, kullum sai ya kira waya ya tambaya idan ka farka, kuma yace da zarar ka dawo hayyacinka mu koma gida." Yaji lokacin da ya zuƙi numfashi ya fitar sannan ya koma da baya ya jingina da gadon bai ce komai ba, don haka shi ya cigaba da cewa. "Mami kusan duk bayan awa guda take kira Ma'aruf, suna can ne amma hankalinsu anan yake, kowa ya damu, Hajiya tace hatta Abdurrahim jiya gidanka ya tafi ya kwana, dan Allah Ma'aruf, dan Allah ka taimaka ko don waɗannan mutanen ka tallafi rayuwarka, dan Allah." Kai tsaye maganganun suka shiga har wani waje dake can ƙasan zuciyar Ma'aruf, kuma yana jin yadda tasirin su ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinsa yana tafiya tare da gudun jinin cikinsu, sai kawai ya sake cusa yatsunsa cikin gashin kansa sannan ya runtse idanunsa. Ishaq yana kallonsa, yana jin yadda tausayinsa ke bin zuciyarsa kamar kullum, ba sauki bane rayuwa da irin wannan cutar ya sani, ba sauki bane daurewa irin abinda ke zuciyar Ma'aruf din, ba sauki bane yadda yake iya daurewa abubuwa tsawon shekarun nan, ba sauki bane ba zama Ma'aruf din da yake gabaɗaya ya sani... Shi yasa fatansa a kodayaushe bai wuce Allah ya tallafi rayuwarsa ta wata hanya daban da take sabuwa ba, domin Allahn ya sani cewa su sun gwada duk wata hanyar da take a tunaninsu amma babu wani sauki. Ya haɗiye yawu a hankali

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73