Skip to content

Chapter 49

Chapter 49

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

da tunanin komai ba, Ta tuna sanda Samirah ke mata bayanin dalilin da yasa basu je gidansu da biki ba. "Mu fa bamu san da bikin ku da Yaya ba sai ana saura two weeks da aka haɗa lefe sannan Mami ke gaya mana, kuma ko ranar dinner ma munso mu kai muku cards din. Yaya Shukra ce ma ta bani ranar luncheon na saka a jakar Khadija (wata kawarta) ita kuma sai tazo da wata jakar kuma ta manta bata ɗebo ba. A ranar ni kuma I was so busy kamar me, shikenan ban samu time munje mu ɗauko ba. Da na kira Yaya kuma na gaya masa cewa yayi kar mu damu kawai." Amma duk da yadda ta fara sakewa a cikin nasu, tana kewar gida kamar ba gobe, abubuwa da yawa akwai su anan na duk wata buƙatar rayuwa, ga komai sabo koina ƙal-ƙal, gashi babu wanda ya taɓa ko haɗe mata rai har yanzu, idan ta shiga cikin gidan kowa haba-haba yake da ita, hatta su Salma amaren da akayi bikinsu tare dukksnsu sun gaisa a wayar Samirah, da Salman ma ba sau biyu suna gaisawa. Ga Hajiya Kilishi da take nan-nan da ita kullum fuskarta dauke da fara'a tana fadin ita ƴarta ce, Ranar da taje ta gaishe da Baffa ranar ta fahimci dalilin da yasa Baba ya bada aurenta a gabansa ba tare da wani tunani ba, dattijo ne kamili mai nutsuwar da a fuska kadai kowa zaiyi masa shaidar hali na gari, don haka babu wata matsala da ta guskanta a gurinsa shima. Sannan shi kansa uban gaiyar har yau ko haɗe rai bai taba yi mata ba, amma duk da haka, tafi son rayuwar cikin ƴanuwanta akan wannan, tunda har yanzu zuciyarta bata gama kwantawa da komai ba, tunaninta iri ɗaya ne da Amma dama kuma Fatima, dukkaninsu sun yarda cewa akwai wani abu dake tahowa wanda bai karaso ba, don ba'a ɗora turbar auren da cewar komai ya tafi daidai ba, sun sani cewa ba sun kawo ta cikinsu ne don su nuna mata kirkinsu ba dashi da ƴan gidan nasu, dole akwai wani abu da yake a ɓoye wanda har yanzu basu kai ga saninsa ba. Su Aminu da Baba ne kawai hankalinsu a kwance don duk sanda suka yi waya da Baban, zai yi ta zubo mata tarin addu'o'in da suke karya zuciyarta, shi har yanzu zuciyarsa guda ɗaya ce game da auren, ya riga ya aminta da Baffa da ma Hajiya Kilishi ta yadda baya taɓa iya hango komai. Ta lumshe idanunta a hankali tana jin yadda bacci ke shirin ɗaukarta a lokacin, ta shiga ƙokarin kore shi don aƙalla tana son jin lokacin da Ma'aruf zai dawo amma baccin mai nauyi ya ƙara karfinsa, don haka wata zuciyar ta gaya mata cewa zata iya ɗan runtsawa tunda tayi sallar isha kuma bata wani samu baccin safe ba sosai, da wannan lasisin da zuciyarta ta bata taji maganganun cikin rediyon nan suka zuƙe daga kanta a hankali, taji su suna yin nisa da kunnenta kafin a lokaci guda taga Aminu a tsaye daga bayan idonta. "Me yasa kika kasa Amina?" Kai tsaye ya tambaye ta yayin da idanunsa ke kallonta, kuma kalaman suka isa kanta amma suka kasa bada ma'ana saboda dukkan tunaninta ya tsaya cak tana kallonsa da dimbin mamaki, Yaushe yazo? Yaushe yazo ko kuma ita yaushe ta bar cikin gidan, don daga nesa tana hango duhuwar wasu dogwayen bishiyu, hakan yasa gabanta fadi da dukkan tsoron da zuciyarta zata iya dauka. Tayi ƙokarin ta kalli kanta amma sai ta fahimci bata iya ganin jikinta kwata-kwata, kamar idanunta ne kawai a wajen suke ganin komai amma babu gangar jikinta, ta ɗago ta sake kallon Aminun da har yanzu ke tsaye a gabanta. A lokacin ta kula cewa idanunsa sun canja, kalolinsu ba iri ɗaya ne daga yadda ta sansu ba, sun koma baƙiƙ-ƙirin dauke da kyallin kwalla yayin da fuskarsa ke nuna dukkan wasu kalolin tashin hankalin da bata taɓa gani a fuskar Aminun ba, Aminun mai raha da fara'a, Aminun data sani mai ɓoye damuwarsa a kodayaushe. "Me yasa kika kasa Amina?" Muryarsa ta sake tambaya da amon da ya kara hargitsa ta, kuma bata san lokacin da ya matso gabanta ba sai kawai taji ya riƙo hannunta na dama. Ta kalli inda hannun nata ya kamata ya kasance, babu komai sai yadda yatsunsa suka riƙe ta, lokacin da ta ɗago da idonta sai taga ashe ya jawo ta ne har sun iso wajen duhuwar bishiyun nan, tashin hankalin ta ya ƙaru don tana jin yadda ƙafafunta da basa nan suke tafiya, da kuma yadda hannayenta ke rawa a cikin nasa. Hankalinta ya kasu wajen nazarin bishiyun sanda suka tsaya a wani waje, ta juyo tana kallon yadda yanayinsa ke haskawa da dukkan raunin da bata taɓa hange ba, taji ta ƙara rikicewa, taji abubuwa da yawa suna tasowa cikin kanta, tambayoyi fal suna ihu da kokawar fitowa daga bakinta da ta san babu shi balle har ta iya furta su, kowanne lungu da saƙo na tunaninta ya cika da hanƙoro, kamar tana jiran wani abun da bata san meye ba. Kuma kwatsam sai ta nemi bishiyun nan dake kewaye dasu duka ta rasa, warin ƙonewarsu ya cika hancinta amma babu su ɗin balle kuma alamun wutar, kuma babu wani ɓata lokaci kunnenta ya fara jiyo mata muryoyinsu, Maryam ta fara ji, tana ihu mai haɗe da salati, sai ta jiyo ta Hafsa da Adam ma, kowanne yana kuka mai nuna tsananin azaba, bata san ya akayi ta iya tsinto muryoyin su Fatima, Ummi har ma da ta wasu daga cikin ƴaƴan kawu Malam ba. Kuma kafin wani abu ya sake giftawa a cikin kanta ta jiyo muryar Baba yana faman kiran sunayen su Maryam ɗin har ma da sauran mutanen da bata iya tantance muryoyinsu ba, hankalinta ya kara tashi duniyarta ta rikice, ihu da hargowar suka cika kanta kota'ina, kuma a lokacin da ta juya zata kalli Aminun sai taga babu shi, a yanzu Amma ce tsaye tana kallonta, fuskarta ɗauke da wani irin murmushi mai ciwo yayin da take kallonta da dukkan wani fata na duniya. "Me yasa kika yarda ba zaki iya ba Amina?" Tayi tambayar a lokaci guda da itama ta neme ta ta rasa, wajen ya koma babu komai sai tashin ihun ƴanuwanta da kuma hargowarsu yayin da warin ƙonewar nan ya cigaba da cika wajen. Ta kasa gane komai ko kuma abinda yake shirin faruwa, abinda kawai zata ita tunawa kafin ta farka shine daga cikin muryoyin dake ihu, ta jiyo wata murya da ta kasa gane wacece ko kuma inda ta santa, muryar tana ƙyalƙyala wata irin dariyar da bata taɓa jin irinta ba! Dariyar ta shiga amsa kuwwa a kowanne ɓangsre na wajen yayin da ihun mutanen dake amsa sunan rayuwarta ke cigaba da tashi.... A lokacin ne kuma ta farka a firgice, kafafunta suka mike tsaye akan gadon bakinta na biyo kalaman Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, a cikin ɗakinta take har yanzu, akan gadon da bacci ya ɗauke ta, amma tun yaushe? Don rediyon wayarta da ta bari a kunne yanzu ƙarar shuuuu kawai take fitarwa. Tasa hannu ta jawo ta da sauri, ta kashe

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73