Skip to content

Chapter 66

Chapter 66

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

nasa ba'a cikin garin Jigawan yake ba, a wani ƙauye ne dake gaba kadan mai suna Kuɗai, gida ne kato da iyalansa, amma kusan rabin dakunan gidan yana saukar marasa lafiya ne wanda ciwonsu yayi tsamari ya zama sai anyi kwanaki ukun da yake bayarwa kafin a bar wajensa, don haka inda suke ɗin dakuna ne a jere kamar asibiti, sai dai bayan su ɗin wani ɗaki ne kawai daga can gefe inda aka sauki wani yaro da nasa iyayen suma da suka zo daga Kaduna. A jiya su biyar Amma tace mata sun zo, bayan ita da Aminun da kuma Baba, sai kuma Fatiman da ta kawo su gidan da kuma wani ɗanuwanta Yusuf da a jiyan su suka koma, dama an taho dashi ne don yayi mata rakiya tunda ita ba kwana zata yi ba. Sai ta mike a hankali ta shiga neman inda ta ajiye mayafinta a dakin lokacin da Aminu yace. "Anjima su Baban Kurnan zasu tafi Amma?" "Eh, Babanku yace da sun dawo daga masallaci zasu kama hanya, su zasu tafi da waɗannan kayan da Amina ta kawo ma don mu sami sauƙi jibin." Kalmar 'waɗannan kayan' ita ta tsaida kafafun Amina cak a inda taje, don ta san waɗanne kaya take nufi, kayan abincin da suka fito daga hannun Hajiya Kilishi. "Wallahi matar nan tana ƙoƙari Amma, Allah dai ya saka mata da alkhairi." Taji Aminun ya sake faɗa kuma ga mamakinta sai taji Amman tayi shiru bata ce komai ba, zuciyarta ta buga a kirjinta, ta juya da sauri a lokaci guda ta kalle ta, kanta na kasa a yanzu tana ninke wasu kayan Aminun, fata take ta fadi wani abanin tunanin sauran mutanen ko ta sami kofar da zata iya tunkararta da zancen da bata san ita ina fara ba, amma ga mamakinta sai tayi ajiyar zuciya sannan tace. "Amin ta kyauta kam, haka Babanku ma yayi ta fada." Sai kawai tayi saurin sunkuyawa ta damƙo mayafinta dake ƙasa sannan ta haɗiye abinda ke bakinta da karfin da zata iya kafin ta muryarta ta fito wani iri. "Bari naje Amma." Da haka ta tura ƙofar net ɗin ɗakin ta fita, tana jin kamar tana ɗauke da nauyin duniya ne bakiɗaya a kafaɗunta, Amma ce kadai fatanta amma ko ita bata san ta yadda zata fara gaya mata komai ɗin ba. Abinda bata sani ba shine, idan ubangiji ya amsa addu'ar bawa, sai komai yazo masa a bazata, don wajen karfe ɗaya Aminu ya samu bacci, Baba kuma tun bayan tafiyarsu Baban kurna ya fita zuwa cikin gari. A lokacin ne Amma ta kira ta zuwa waje, kasan wata katuwar bishiya daga cikin gidan suka zauna inda aka shimfiɗa wata tsohuwar tabarma, kuma kalamanta na farko suka gutsirtsira duk wani saurin ƙarfin gwiwa da take jin cewa tana dashi na iya fuskantar wannan tashin hankalin. "Amina a wannan zamanin mafarki baya tabbata, kin sani ba zan taɓa yarda cewa lafiya kike zaune a gidan nan ba ko?" Lokacin da ta faɗi hakan kallonta take da ƙwallar data cika idanunta taf, amma sai ta girgiza mata kai ta cigaba da cewa. "Ni uwa ce ina kallon abinda ya shige wannan zahirin, dukkan kalamanki da kuma abinda ke faruwa basu isa su sa in kasa hango damuwarki ba... Watakila a kwanakin baya muryarki a waya taso ta ɓoye min wani abu tunda ba ganinki nake yi ba, amma a yau kallonki kawai na yi Amina, na zaƙulo tarin abubuwan da ban sanki dasu ba fal." Sautin muryar Amman ya fito da ɗimbin abubuwa masu yawa, masu yawan da a cikinsu babu wanda bai sake karya zuciyar Amina ba, yana tuna mata da rayuwarta ta baya data shuɗe cikin wani kankanin lokaci, lokacin da Hajiya Kilishi bata yiwa Baba wannan kiran ba balle har a fara ƙulla zaren ƙaddarar ta, lokacin da bata kirga damuwa a cikin lissafinta tana kwana tana tashi ne kawai da mafarkin abinda gobe zata haifar. "Me suke yi miki Amina? Ki faɗa min abinda yake ƙasan wannan kyautatawar..." Ba shiri leɓɓenta ya tale cikin kokarin yin kuka yayin da take cakuɗa yatsunta cikin juna, kuma kaf a cikin bayanin da bakinta ya fara, layi biyu ne kawai ya sa fuskar Amma haskawa da tsananin mamakin da ko na nesa zai ganshi karara, amma bayan wannan layi biyun, saurarar bayanin ƴarta tata take yi da dukkan wata nutsuwar da take da ita a duniya... Nutsuwar da take da ita ta Halimatus- Sadiyar ta, sannan nutsuwar da a cikinta ta shafe shekaru ashirin da ɗoriya a gidan aurenta ba tare da wani mahaluki a duniyar nan ya taɓa jin kanta game da mijinta ba. Nutsuwar da a cikinta ne idan za'a taro duk mutanen da suka santa a rayuwa, ƙaryane a samu mutum guda da zai tabbatar da wani aibinta baiyananne... Nutsuwar da a cikinta wasu tarin abubuwa suka faru da idan da za'a buɗewa Hajiya Kilishi su, zata yi dana sani sau dubu na inda ta kawo kanta, zata raina duk wani tunaninta dama wayonta, zata san cewa tayi kuskure wajen amfani da ƙwaƙwalwarta wajen cimma munafunci, mugunta, yaudara har ma da zalunci. Zata gane cewa ba an halicci ƙwaƙwalwar mace ne don ta fitar da da kaidi kamar yadda take taƙama ba, zata san cewa Allah ya halicci ƙwaƙwalwar mace ne don ta samarwa kanta duniya da kuma lahirarta a tafin hannunta kamar yadda ita tayi. Kuma a karo na farko tun bayan tsawo lokaci wani murmushi ya suɓuce a fuskar Amman, ita ta sani ba'a banza jikinta ya bata cewar bata son kai ƴarta cikin wannan gidan ba, ashe wata halittar ce mai ɗauke da irin ƙwaƙwalwar ta a wajen, banbancin kawai shine ita waccan ƙwaƙwalwar cike take da duhu tata kuma fara ce kal! Idan kissa da dabara Kilishi ke taƙama dashi, tazo wajen da yake daidai ita, hausawa sunce karen bana maganin zomon bana! wasan nasu ne yanzu, kowa zai yi nasa cizon da sunan ceto! Kuma Amina da Ma'aruf ɗin data zaɓa dasu za'ayi wasan! Wasan da a karshensa Sarki ɗaya zai tsaya a wani matsayi da ita ta riga ta saba dashi. Don mutane ukun da ta ga ƙarshen makircinsu a rayuwarta, bata jin Kilishi ta ko kamo yatsan ƙafarsu, kuma kamar yadda ta nuna musu, haka zata tabbatarwa da Kilishi itama yadda cikakkiyar macen data amsa suna da matsayinta ke amfani da ƙwaƙwalwarta a bigiren da ubangiji ya halitta mata ba bigiren shaidan ba, zata nuna mata irin yadda tayi asarar nata tunanin a duniyar nan! A hankali ta gyara zamanta sannan ta furta. "Daga yau kar na ƙara ganin hawaye a fuskarki kamar yadda baki taɓa ganinsa a tawa ba...!" Waɗannan kalaman su suka zama na farko da ta shiga sauke ƴarta daga raunin da ta hau kai zuwa dakakkiyar Aminarta da ta san ta baro hannunta da ƙwarin gwiwar cewa zata iya tunkarar yaƙin dake gabanta saboda mahaifinta. Banbancin shine wannan karon zata sa ta fuskanci yaƙin ne saboda kyautatawar rayuwarta... a tafin hannunta zata ɗora mata rayuwar gidanta sannan a ɗaya tafin, zata ɗora mata Kilishi bayan sun sa ta biyo ta kan matattakalar... 'Ɗan hakin da ka raina...! *** Haseenah Guest Inn, Jigawa. 04:30pm "Gidan da ka dauko Hamidan zaka koma

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73