Chapter 23
Chapter 23
Hafsa suna doki ke shiga kunnenta, tunda satin nan ya kama komai ƙara gaya mata yake yi cewar sauran wasu ƙaiyadaddun kwanaki rayuwarta ta fara daga gaɓar da zata ƙare. Musamman wannan haɗuwar ta ƴanuwan Amman a gidansu, wani abu ne daban da basu saba ba don Tanti itace babba a cikin su Amman, don haka mafi yawanci a gidanta ake yawan haɗuwa, ko da Sallah kowa can yake tafiya su haɗu har su, shi yasa ganin yadda gidan nasu ya zama wajen haɗuwa yanzu yana ƙara tabbatar mata cewa da gaske komai ke shirin faruwa, gashi Baba ma har ya fara aiko da tanadin abincin biki duk da Amma ta daɗe da kafa layin cewa ba wani taro za'ayi mai yawa ba, ko ƴanuwansu a can Niger tace duk a waya za'a shaida musu kawai, sai dai idan maza zasu zo ɗaurin aure don ya zama shaida a wajensu. Wani abu ya wuce ta maƙogwaronta lokacin da idonta ya kai kan tulin katinan ɗaurin auren nan, sunayen mutane takwas ne a jiki banda sauran bayanai, amma idan ta kalle shi ba abinda idonta ke gani sai nata sunan dake ƙasan rubutun Ma'aruf Mansur Bakori, sunan da ko sau nawa zata maimaita shi sai ta ji bugawar zuciyarta a cikin allon ƙirjinta. Ta rufe idanunta ta buɗe tana jin yadda har yanzu zuciyarta ta kasa yarda cewa tana shirin buɗe shafin kaddarata ne da hannayenta. Ba lallai ne ya kashe ta kamar yadda ya rubuto a takardar nan ba ta sani, ya rubuta ne kawai don ya tsoratar da ita, amma hakan ba zai hana ta ɗanɗani gwargwadon azabar da ya tsara mata ba, tunda ta tankwabe gargaɗin da yayi mata. Ta tuno shekaranjiya lokacin da Tanti ke tambayar Amma 'yaron kuwa yazo?' sai da ta ƙware da yawunta tsabar yadda tsoron hakan ya shige ta, ita har yanzu bata hango cewar in dai wannan Ma'aruf ɗin da ta sani ne zata ganshi a kusa da ita ma balle ƙaddara ta haɗa su. Gani take yi kamar za'ayi auren ne kawai a kaita wajen Hajiya Kilishin da sunanta ne kaɗai ke yawo a gidansu game da auren. Shi yasa bata fatan kowa ma ya ambace shi, tafi son ayi dukkan abinda za'ayi a kaita ɗin kawai, acan zata tsara matakan da watakila zasu iya siyar mata lokaci kafin dukkan abinda zai faru ya faru har Amma tazo tace. 'Dama na gaya miki Amina' Fatima ma tace. 'Me yasa kika yi tunanin zaki iya Amina?' Maryam zata dinga da binta da kallo kawai, Aminu kuma zai iya cewa. 'Ko ba komai kin ƙoƙorta Amina.' Baba ne kadai zai saka mata albarka ta sani, yayi mata addu'o'in da wataƙila zasu iya gyara rayuwarta a gaba, don ya san tayi komai ne don shi, don tallafar mutuncinsa. Ta kai ƙarshen tunaninta lokacin da sallamar su Ummi da Momi ta cika tsakar gidansu, taji su suna gaisawa dasu Amma har da muryoyin wasu daban don haka ta rufe wardrobe ɗin ta juyo tana korar yaran zuwa waje. A lokacin Ummi ta ɗage labulen ɗakin ta shigo. "To amaryar ƙulle, kina nan mu munje mun samawa kanmu mafita.." Suka shigo suna ajiye ledojin hannayensu yayin da Momy ke cewa. "Amina ruwa dan Allah, wallahi mun ɗebo rana." Da murmushi ta fita zuwa kitchen ta ɗauko jug ɗinsu na roba haɗe da kofinansa ta ɗebo musu ruwa sannan ta dawo. "Wai daga ina kuke?" Muryarta a hankali ta tambaya tana ajiye musu ruwan. Ummi ta miƙo mata ledar kusa da ita tace. "Buɗa ki ga." Ta karɓa kuwa ta shiga zaro wasu atamfofi masu kyau kalar ruwan hoda, (pink). Wani abu ya zarce ta maƙogwaronta, tun lokacin da aka kawo kayan lefen nan su Ummi suka san zancen auren, tunda suma sun san Hajiya Kilishin a matsayin ƴar uwarsu kawai dai tafi shiri da Baba ne duk a cikin si Kawu Mallam ɗin, don haka sai rawar ƙafarsu ta ƙaru kamar me sanin cewar bikin irin wanda suke so ne. "Kowacce dubu ɗaya kenan da ɗari biyar, jikinsu mai kyau ne baza ki taɓa cewa roba bace." "Wai na meye?" Momi tace. "Har tambaya kike? To anko ne muka fito dashi tunda ke baki da niyya, kin san mu ƴan ayi sha'ani ne babu ta yadda za'ayi muyi biki lami ko amaryar bata so." Amina bata ce komai ba, Momi ta sake cewa. "Ina Fatima? Ga guda ɗaya nan ta Maryam mun siyo sai ta nunawa ƙawayenku ita, wanda yake da hali yayi tunda dai saura ƴan kwanaki, waɗannan kuma ƙawayen mu ne su ma gashi sun siyo tasu." Sai a lokacin ta ɗago ta kalli ƙawayen nasu da murmushi a fuskarta tace. "Allah ya saka da alkhairi, nagode." Ummi ta kalle ta tace. "Su da kuɗinsu kike musu godiya? Zo muje ni kiga wani abu." Da haka ta ja ta suka fita daga ɗakin, a tsakar gida su Amma duk sun shige can ɗakinta suna cigaba da haɗa kayan dake ciki, sai Aminu kawai dake ta ɗaga yaran nan sama suna dariya. A ƙofar ɗakin Baffa suka tsaya Ummin tace. "Amina duk shiru-shirunki na san ba haka halaiyarki take ba, akwai wani abu game da auren nan da kike ɓoye mana, kin sani ni da Momi ƴanuwanki ne kuma sa'aninki da zamu iya jin irin ciwonki, idan akwai matsala ki gaya mana, wallahi in zamu iya zamu taimake ki." Amina ta haɗiye wani abu, duk kauɗin su Ummi ta sani cewa suna da zuciya mai kyau a can ƙasa, kuma ta sani cewa suna sonta fiye da yawanci daga cikin ƴan uwansu don haka zasu iya taimaka matan da komai, sai dai bata yi tunanin cewa Ummin zata iya ganin damuwarta sama da ɗokin bikin da suke yi ba. Amma duk da haka ta san babu amfani sanin nasu kamar yadda Baba ya shar'anta tun farko, musamman su biyun nan da ta san idan suka ji kamar ta saka lasifika ne a tsakar gidan Kawu mallam ta faɗawa kowa. Don haka sai kawai ta girgiza kanta. "Wallahi ba wani abu bane Ummi, kin san ban taɓa kawowa kaina aure a yanzu ba ne kawai, kuma sai komai yazo a lokaci guda shi yasa kawai nake jin wani iri." Kamar Ummin bata yarda ba, amma bayan ta kalle ta na wasu sakanni sai ta gyaɗa kanta tace. "To ai shikenan, idan wannan ne da an kai ki sati ɗaya na san zai tafi, don duk da haɗa ku akayi ke bata wasa bace Amina, kuma duk yadda yake jin kansa na san zaki iya dashi....Wai yaushe zamu ganshi ne ma? Ya bamu kuɗin walima..." Wai me yasa kowa yake son ganin sa? Me yasa kowa yake son jawo shi da baki? Basu san a lisafin tashin hankalinta wannan shi ne a sama ba? Jin bata ce komai ba yasa ta sake cewa. "Ko da yake da alama kema ba wani ganinsa kike ba, masu kudin nan sai a hankali, amma dai na san zaku haɗu kafin wani satin sai ki karɓo a madadinmu, idan ba haka ba kuma ni zan karɓi lambar wayarsa na tambaya da kaina." Jin haka yasa tayi saurin girgiza kanta tace. "Kar ki damu baza'a kai hakan ba ma." Ina zata kai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73