Skip to content

Chapter 71

Chapter 71

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

saman ta kowa, shi ya fara yarda da ita kafin ta buɗe zuciyar kowa ta fara aiwatar da manufarta, idan baki sani ba yau ki sani Amina cewar taƙamar kowacce mace a duniyar zuciyar mijinta ce, idan taci riba anan to wallahi duk girman wata matsala koda kuwa ta mahaifiyarsa ce ta tsallake ta. Yaron nan ya riga ya zama mijinki a yanzu ko munso ko bamu so ba, don haka kije ki ƙara dagewa, ki dage wajen kyautata masa har zuciyarsa ta ƙara yarda dake akan yanzu, sannan da zarar kun koma kije wajen Kilishi ki tsugunna ki gaya mata cewar kin yarda da sharaɗinta bama sai lokacin da ta gindaya miki yayi ba, ki ƙasƙantar da kanki a gabanta ta sigar da ba zata taba iya haska cikin zuciyarki har tayi wani hasashe ba, waɗannan sune matakan farko Amina, kuma ina tabbatar miki idan kika tsallake su, dukkan sauran zasu zo ne bi da bi kuma a sauƙake..." Waɗannan sune kalaman dake saka sa hannyenta rawa a ɗazu, sune kalaman Amman dake rikita lissafinta suna gaya mata cewar ba zata iya dorar da wani abu akan Ma'aruf ba tunda bata gama sanin tunaninsa akanta ba... Sai gashi tun ba'aje koina ba hanyar farko tazo mata da sauki. Allah ya amsa addu'ar ta, Ma'aruf ya cire dukkan wani kokwanton dake zuciyarta da waɗannan iya kalaman nasa, a yanzu ta yarda cewa shi da gaske zuciyarsa wankakkiya ce akansa, abinda take ta taraddadi daga bangaren Hajiya Kilishi yake dama. Taji yadda mamaki ke cinye zuciyarta tun daga ƙasa, ashe komai ba mai wuya bane kamar yadda Amman tace, kowacce mace tana da irin nata ikon a hannu, kawai burga da barazana ce ke saka wasu yin ƙasa su yarda cewa an fisu su baza su iya ba, gashi tun basu ko bar garin nan ba ta fara samun yardar Ma'aruf a hannunta, idan haka ne kuwa ta yarda da maganar Amma na cewar da gaske Kilishi ta kiyaye su, don ko ita a yanzu tana jin ƙarfin gwiwar cewa zata iya. Kuma cikin wata irin sa'a, sai ya ƙyale ta bai nemi amsarta ba har suka kammala cin abincin da komai. Wajen ƙarfe goma sha ɗaya saura Amina ta dunkunkune a karshe gadon ɗakin har a lokacin tana ta faman sake-sake a ranar, don ko ka kaɗan ba bacci take ji ba, abubuwan da ta fuskanta a yau suna da yawan da har yanzu basu gama narkewa a cikin ranta ba. Ta juya bayanta ne tana kallon ɗaya gefen ɗakin yayin da hannunta ke wasa da ƙarshen bakin mayafin nan data yafa a akanta. A yanzu fitulun ɗakin duka a kashe suke, Ma'aruf ya kashe su kafin ya shiga toilet don ta riga shi kwanciya, sai da ya gama aikinsa tana kwance tana sake-sakenta sannan ya tashi ya kashe fitulun duka ya shiga toilet din. A yanzu babu wani haske sai na waje da yake shigowa cikin ɗakin, kuma wucewar minti biyar kawai sai kofar toilet din ta buɗe, hasken fitilar ciki ya ratsa duhun ɗakin kuma duk da ta juya bayanta sai da hasken ya shiga idonta kafin taji ya rufe ƙofar duhun na sake dawowa. Taji gadon ya motsa yana shaida mata hawowarsa zuwa daya gefen da sanda yaje jan sauran bargon da ta rufe ƙafafunta dashi zuwa nasa jikin. Sakan ɗaya, biyu, suka wuce tana cigaba da wasa da mayafinta kafin taji muryarsa, can ƙasa a hankali kamar duhun daren. "Amina..." Ya kira sunanta kamar wannan ne karo na farko daya fara faɗa, yadda tunaninta ya tsaya cak haka ma daren ya tsaya, kamar shima yana jiran amsar da zata bayar ne. Tayi kokarin haɗiye wata busashshiyar iska a makogwaronta sannan tayi dauriyar amsawa a hankali. "Can I hold you.. ?" (Zan iya riƙe ki?) Bata san me take tunanin a wannan lokacin ba, bata san ma me taje yi va ko kuma abinda yake faruwa a cikin kanta, ta san dai kawai zuciyarta ta ƙirga wucewar wasu sakanni ne data san cewa jiranta yake yi kafin duk wata dauriyarta ta rinjaye ta wajen ɗaga kanta a hankali. Kuma bata san ya akayi yaji ta ba, don a lokaci guda yasa hannunsa daya ya janyo ta zuwa jikinsa, ya juyo ta tana fuskantar sa yayin da hannunsa ɗaya ya zagaye waist ɗinta, sannan ɗan kaɗan ya ratsa ƙafafunsa a tsakanin nata. Ya hade ta da jikinsa har tana jin kara bugawar zuciyarsa kamar kaɗawar igiyar ruwa a bakin teku wanda sautinsa ya haɗe da amon tata zuciyar, ya zama idanunta basa ganin duhun daren sai wanda ke tsakaninsu kawai, numfashinsu ya hade waje guda yayin da ƙamshin turare da kuma sabuntar kayansu ya cika hancinta. Kuma bai isa Ma'aruf ya gama rikita zuciyarta ba sai da ya sunkuyo da fuskarsa daidai cikin wuyanta ba shiri kuwa jikinta ya shiga girgizawa gabaɗaya a cikin nasa, kuma ga mamakinta sai taji yayi wani abu kamar murmushi sannan a cikin kunnenta ya furta maganar data rikito da duniyarta bakiɗaya ta rugurguje. "Kar ki damu, not now, not here." (Ba yanzu ba, ba anan ba.) Shikenan! Ma'aruf ya gama da rayuwarta! *** Kano. 09:30Am No. 58 Mafara Street, NNDC Sharaɗa Quaters. "Wai har kun dawo?" Surayya ta faɗa a lokacin da ta fito dafa daki tana kallon Amina daje zaune a tsakiyar falon nasu tare da Sameerah wadda ta cika gabanta da kayan breakfast. "Tun wajen ƙarfe takwas fa suka dawo. Yayan har ya tafi aiki ma." Sameerah ta bata amsa lokacin da take hada nata tea din. "Auren ma'aikacin kamfani na da wuya ko?" Surayyan ta fada tana kallon Amina lokacin da tazo ta zauna a kusa da ita tana ɗaukan pillow ɗin kujerar zuwa cinyarta. Da murmushi a fuskar Amina tace. "Gashi nan dai, ni ban saba ba har yanzu." "Gaya min zaki yi idan da wuya tun wuri in kori Tahir." Kafin ta amsa Sameerah tace. "Ki kore shi ma, don Wallahi Baffa yace ba wanda zai sake yiwa aure a gidan nan sai man da shekara biyar. Su Salma sun karya tattalin arzikinsa." Dariya kawai Amina tayi tana kallonsu lokacin da musun da suka saba a kullum ya kaure tsakaninsu, don ma wai Munaya na can ɓangarensu ne. Sai dai duk yadda dariyar tata ta kai akan lebbenta kawai take, don daga can kasan zuciyarta taraddadi ne fal da kuma tunanin abinda ke shirin faruwa. Don kamar yadda Samirah ta fadawa Surayya ne, tun wajen karfe takwas da ƴan mintuna na safe suka iso garin Kano, don Ma'aruf ya gaya mata cewar yana da tarin aikin dake jiransa a office, kuma ya sauke ta a gida ne ya tafi bayan ya rungume ta yayi kissing saman kanta lokacin da suka shigo ciki ya buɗe mata gidan da muƙullin dake jikin na motarsa, sannan ya juya ya barta tana kokarin hada zuciyarta waje guda ya koma wajen motar tasa da ya bari a waje. Kuma shigarta gidan ya sake tsayar da zuciyarta waje guda, yana tuna mata da kalaman Amma. "...da zarar kun koma kije wajen Kilishi ki tsugunna ki gaya mata cewar kin yarda da sharaɗinta bama sai lokacin da ta gindaya miki yayi ba, ki ƙasƙantar da kanki a gabanta ta sigar da ba zata taba

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73