Skip to content

Chapter 48

Chapter 48

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

ban ƙarasa kallo ba." Sai ta sake ɗagowa ta kalle shi. "Na zata novel ne." Ta fada kamar tana tsoron labarin nasu zai banbanta, amma sai yayi saurin daga mata kai. "Novel ne, amma lokacin da Munaya ta takura min da zancen labarin bani da time ɗin karatu, so sai kawai na siyo film din na kalla instead." Ta gyada kanta sau daya sannan ta sake maida shi ƙasa ba tare da tace komai, yaji wani abu na shiga zuciyarsa yadda ta fara sakewa dashi a yanzu, don haka kai tsaye ya sake tambayarta. "Baki kalli film din ba?" ya tambaya yana nazarin abinda bata faɗa ba akan furkar ta, kuma sai ta bashi amsar da ya riga ya sani ɗin ta hanyar daga kanta. "Insha Allah zan kawo miki ki gani." Sai ta ɗago ta kalle shi, yayin da hannunta ya tsaya da wasa da mayafin nata. "Allah ya yarda." Ta furta a hankali tana kallonsa, kuma a cikin idanun nata Ma'aruf yaga daren ya tsaya cak kafin ta sake sunkuyar da kanta a hankali, yaji wani abu yaji kamar tausayinta na bi ta kan zuciyarsa. Tana da rayuwarta ya sani, watakila har ma da mafarkai na abubuwan da take son cimma, amma yanayin yadda auren yazo ya sani cewa yabi ta kan abubuwa da yawa a rayuwar tata, wanda da shine baya taɓa jin zai jurewa hakan, amma ita gata a zaune har tana kokarin yi masa hidima, yaji wani abu ya zarce cikin maƙogwaron sa a lokaci guda, a baya yana jin zai iya bin kowacce hanya don sanin meye haɗinta da Jamal amma tun a yanzu ya fara jin cewa ba zai iya yin abinda zata yi dana sanin haɗuwa dashi a rayuwarta ba. *** Washegari da safe Hajiya Kilishi ta buɗe kofar ɓangarenta, fuskarta ta faɗaɗa da wannan murmushin nata mai armashi a duk lokacin da ta ganshi duk kuwa da cewar a jiya tayi ta kallon agogo cikin lissafin zuwansa amma bata ganshi din ba, dalilin da yasa a yau ta tashi da sassafe kenan don ta san yana da karbar magani a yau, don haka ta buɗe kofar zuciyarta na fatan ya kasance Ma'aruf ɗin ne, kuma fatan nata ya karɓu don yana tsaye a gabanta yana murmushin da take jinsa kamar ashanar dake ƙyasta zuciyarta wajen kamawa da wuta. "Tun jiya muke kallon hanya Ma'aruf..." Ta fada tana kallon idanunsa da kullum suke gaya mata shi daban ne a lissafinta ba sai ta rantse ba, zuciyarta tana yin fiffike ne ta tashi sama ta zagaya a duk lokacin da ta ganshi a gabanta irin haka. "Mami I'm sorry, jiya aiki ne yayi min yawa kuma a gida naci abinci shi yasa baki ganni ba." Maganar ta taho kamar wani gingimeman dutsen da ya faɗo daga kolulowar sama ya dira a tsakiyar kanta, a lokaci guda murmushin fuskarta ya ɗauke, idanunta suka tsaya akansa cak a sanda ya kara wayar hannunsa a kunne ya shiga yiwa wani Benjamin magana cewa yayi wa Legal Department ɗinsu bayani su ƙarasa shiryawa kafin ya ƙaraso. Ya katse wayar ya juyo ya kalle ta a lokaci guda da yanayin nata ya baje, fuskarta ta cakuɗe da murmushin da yasa shi gyaɗa mata kai kafin ya wuce zuwa ciki, Abinda bai sani ba shine wannan karon murmushin ba nasa bane, na halittar da take hangowa a cikin idanunta ce... Amina! A yau an ƙaraso gaɓar da take jira, a yau tsarinta zai fara ba sai gobe ba, bata wasa da lokaci balle har tayi sake da koda ƴar mitsitsiyar dama ce... A yau Amina zata shigo cikin ukunta! A yau duk wani mahalukin da yake da kusanci da Amina zai shigo cikin lissafinta! ** #Aysha shafi'ee. #fikrawriters #FararWuta. BABI NA SHA DAYA. ~~~~~~~ I've never fallen from quite this high Fallin' into your ocean eyes Those ocean eyes. -Billie Ellish A wannan ranar Amina na kwance daga kan gadon ɗakin tana sauraren wani shiri mai taken 'Allah ɗaya gari banban' da baya taɓa wuce ta daga cikin rediyon wayarta. Idanunta kusan a rufe suke yayin da take sauraren maganganun mutanen dake gabatar da shirin, yau hira ake akan daya daga cikin garuruwan da take son zuwa a rayuwarta, Paris... Don haka sosai take jin daɗin duk wani bayani da baƙin da aka gaiyato suke yi na yadda garin yake da kuma tsare-tsaren su. Sai dai duk yadda hankalinta ke kan shirin zuciyarta kuma nata zarya a can falon gidan inda ta kammala komai na abincin Ma'aruf ta ajiye masa kaar jiya, a yau ta riga ta tsarawa kanta cewa ba zata fita ba don Allah ya sani bata so yaga kamar tana kokarin shige masa ne ko kaɗan, ƙundubalar da tayi wajen yi masa abincin ta wadatar tunda har yanzu bata san manufarsa akanta ba. Ko a jiya umarnin da ya bata ne kawai yasa ta zauna ba wani abu ba, yadda muryarsa ta furta 'Ki zauna' da kuma yadda ya kalle ta da idanunsa bai bata damar zabi ba ko kadan. Duk da cewa kuwa taji dadin hirar, tsaya... Ba hirar tasu ce ta mata daɗi ba, zancen cewa wannan labarin yana da film ne, don Allah ya sani zata so ganin yadda dukkan tunaninta game da komai na labarin zai fito zahiri. "... Wato ina gaya maka samun gida a garin nan shine babban abu mai wahala, gidaje ba karamin tsada ne dasu acan ba..." Hirar rediyon ta cigaba da fitowa yayin da zuciyarta ta fara lissafin kamar yau ya daɗe da yawa, don ko da safe bata ganshi ba kuma yau ita kadai ta yini a gidan, su Sahla da Zahran da suka yi mata alkawarin zasu sake shigo mata yau sun manta da zuwansu makarantar Haddar da suke zuwa shi yasa bata gansu ba. Tun da tazo gidan basu shigo mata ba sai jiyan, kuma sai a jiyan ta gane ashe su ma suna da magana kamar su Samirah, a cikin gidan idan ta gansu da littafinsu kawai gaishe ta suke yi su cigaba da harkokinsu, amma jiyan da suka shigo tasha labarai kala-kala wanda mafi yawanci ba komai ta gane ba. Don a baiyane yake yanayin rayuwarsu da tata ba iri ɗaya bane, abubuwan da suka taso suka sansu ita har yanzu saninta bai ƙaraso nan ba, yanayin makarantar su dama ƴaƴan masu kuɗin da suke mu'amala dasu ba iri daya bane da abinda ita ta taso ta sani. Ta tuno wata magana da Aminu ya taɓa gayawa Maryam ranar da yake tsokanarta bayan ta gama kurin cewa ai ita babu inda zata je a raina ta. "... Nan bayan layin nan idan aka ƙarasa ba sai anje da nisa ba za'ayi iya ɗebo sa'anninki biyar da in suna hira ba zaki taba iya magana ba wallahi sai dai kiyi ta binsu da kallo kina wage baki." Itama dai kuwan ta wage jiya, don murmushi kawai tayi ta binsu dashi kamar yadda take yi a wajensu Samirah, don har gwara su Zahran ma, su idan suka fadi wani abu sai ta biya shi sau biyu akanta kafin ta fahimta musamman Surayya da ta fahimci tafi su iyayi gabaɗaya. Suna da daɗin mu'amala sosai, da gaske suke sun karbe ta a cikinsu ba tare

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73