Chapter 69
Chapter 69
komai banda kyawunta don ita ɗin kyakkyawa ce, amma a yanzu ya samu wannan amsar da ya daɗe yana nema, don yadda zuciyarsa ke sake ɗaukan hoton ƙafafun Amina tana masa kyakkyawar ajiya, a wani yanayi ne da wataƙila ko bayan ransa ba zai manta ba. Ta ƙaraso kamar mara gaskiya ta wuce shi ta nufi wajen wani ɗan ƙaramin table da ma'aikatan wajen suka kawo musu abinci kamar yadda ya basu umarni. Kuma sai a sannan tayi magana, tun bayan da suka idar da sallar isha da ya bata wayarsa ta sake kiran mahaifiyarta ta shaida mata cewa basu bar garin ba sai gobe tukunna. "Wanne abincin zan zubo maka?" Yaji ta tambaya daga bayansa inda taje ta tsaya, sai kawai ya ture komai a ransa ya taso ya taho inda take, ta juya bayan nata kamar yadda ya zata tana ƙoƙarin buɗe plates ɗin masu wasu irin manyan-manyan murafe kamar na abincin sarakai, a hankali ƙafafunsa suka tako ta kan carpet ɗin dake shimfide a wajen ya ƙaraso ya tsaya dab da bayan nata idanunsa na nazarin ɗan karamin jikinta dama siraran hannunta, bayan haka tsawonta ma gabadaya iya kafaɗarsa ne, ya san yana da tsawo don shi da Jamal ana cewa duk tsawon Hajiya Maimuna suka yi, amma bai taɓa tsayawa yayi nazarin yadda yafi wani tsawo irin haka ba sai akanta, don ko Ruƙayya ya sani ne cewa da kaɗan yafi ta. Kuma wataƙila shirun da yayi ne yasa ta juyowa a hankali hannunta rike da murfin da ta ɗauko guda ɗaya, idonsa ya sake kaiwa kan kafafunta a yanzu data juyo, sai yanzu ya lura cewa akan farcen kafafun nata akwai kalar baki alamun lallen da bai gama fita ba, kuma yadda farcen ya rabu kala biyu fari da baki yasa shi kasa daina kallonsu. Amina ta sunkuya kalli ƙafafunta da yake kallo tana son ta nemo abinda ke wajen amma bata ga komai ba, yadda yake tsaye dab da ita kaɗai ya isa yasa zuciyarta rabewa gida biyu, amma tunda bata rabe tun a lokacin data fahimci cewa yau zata kwana daya daki daya dashi ba, bata jin a yanzun ma zata yi. Ta sake haɗiye wani abu karo na ba adadi a maƙogwaronta tana son kore ɗimbin tunanin dake kanta kafin ta sake yin magana. "Zaka ci abincin?" Muryarta ta fito ne kamar tana son tuna masa cewa ba'a kafarta fuskarta take ba, kuma hakan yayi aiki don a lokaci guda ya ɗago da idonsa ya kalle ta. "Naci abincinki, kin manta?" Ta yaya zata manta, da wannan busashshiyar doya da ƙwan data soya tun safe yayi buɗa baki, tea ɗin wajen kawai yasha ya cinye doyar gabaɗaya, a lokacin tana waya dasu Amma, tana daga karshen ɗakin kallon yadda yake buɗe-bude a cikin labtop ɗinsa yana cin doyar, wani abu da ya kara nutsar da zuciyarta a cikin kirjinta tana jin dama abinda tayi yafi doyar kaɗai, sannan kuma wani abu da ya fara buɗewa kalaman Amma dake sa hannunta rawa kofa a zuciyarta. Sai ta girgiza kanta a yanzu tana ƙoƙarin cigaba da kallonsa. "Ai wannan ba zai isa ba, idan mutum yayi azumi gwara yaci abinci da yawa." Ya gyaɗa kansa shima yana kallonta. "Na sani, amma raina ne ya fara ɓaci yanzu, bana jin zan iya cin abincin." Kawai sai ta samu kanta da tambayar. "Me ya faru?" Kuma fitowar tambayar yasa taji kamar ta fara yin nisa da taraddadin dake zuciyarta. Hannunsa ɗaya taga ya zura cikin gashin kansa kamar abinda zai faɗa zai yi masa wahala kafin wucewar sakan biyu yace. "Ina da abubuwa da yawa a gabana, so mutane na using wannan opportunity ɗin suna cuta ta, Annual report din MMB- 6 aka aiko min yanzu, kuɗin da suka ce sun kashe a shekarar nan Amina ko ni bani dasu yanzu." Ba maganganun ne suka daki zuciyar Amina ba, sautin muryarsa ne yadda ya fito cike da wani rauni da idan za'ayi musu da ɗimbin mutane zasu kwana suna rantsewa cewa ba daga muryar Ma'aruf wannan raunin yake ba, ba shiri taji ta hadiye wani abu a makogwaronta kafin tace. "Meye MMB-6?" Wataƙila idan ta fara sani meye shi din zata fahimci abinda maganar tasa take nufi. "Asibiti na ne da yake Abuja." Sai ta sake gyaɗa kanta tana jin kamar maganar tafi karfinta, amma kuma kai tsaye sai tace. "Ance idan hankali ya ɓata hankali ake sawa ya nemo shi, yanzu ko ranka ya ɓaci babu abinda zai canja, kamata yayi ka samu nutsuwa mai kyau, sai kayi amfani da hakan ka gano koma wane irin akasi ne aka samu." Maganganun suka tafi har ƙarshen zuciyar Ma'aruf, suna fito da irin kwanciyar hankalin da yake ji a duk lokacin da ya gayawa Mami damuwarsa kuma ta bashi ɗaya daga cikin shawarwarin ta, Amina bata sani bane amma itace mutum ta farko daya dangance shi bayan Ishaq da suka san da zancen asibitin nan. Abu ne da ko Mamin bata sani ba, kuma shi yasa dama yake damuwa duk sanda aka samu matsala akansa don ya san babu wanda zai iya bashi shawara mai kyau akan hakan tunda ko Ishaq baya yiwa zancensa. Kuma haka kurum ya zaɓi boyewa kowa sanin da zaman asibitin don so yake yi da gaske ya binne duk wata halayyarsa ta baya tare dasu kamar yadda yayi wa kansa alƙawari. Zama likita yana daya daga cikin burinsa na farko a duniya, don haka nacin da zuciyarsa ke masa shi yasa shi tsallakewa zuwa garin Abuja ya gina ƙaton asibitin guda inda ya danka amanarsa a hannun wani likita mai suna Sadiq, shi yake jagorantar komai na asinitin don hatta tarin likitocin dake musu aiki shi yake biyansu, shekaru biyar kenan da kafa asibitin, kuma tun bayan shekaru biyun farko aka fara samun matsala a annual report din da suke bashi duk ƙarshen shekara, ya zama kudin da suke cewa duna amfani dashi duk shekara ya fara fin karfin tunaninsa. Sai gashi yanzu minti ɗaya kawai gaban Amina duk dauriyarsa ya kasa riƙe wannan sirrin ya fallasa mata komai, amma kuma da ta bashi sai tasa bai ji yayi nadamar sanar da itan ba, hasalima zuciyarsa gode masa ta dinga yi don aƙalla abinda ta faɗa ɗin ya sama mata wani sauƙin. Sai kawai ya gyaɗa kansa yace. "Thank you." Sannan ya zagayo ta gefen table ɗin yace. "Me zaki zuba mana?" Tambayar tasa ta juyowa itama tana jin nauyin abinda ya faɗa, plates din ya shiga budewa gabadaya yana tara murafansu a hannusa ɗaya. "Wanne kafi so a ciki?" Ta samu kanta da tambaya babu wani dalili. Ya girgiza kansa shima. "Ni zan ci ko meye kika zuba, favourite abinda nake so baya cikin wadannan." Ya fada yana kokarin ajiye murafan a gefe, sannan kai tsaye ya shiga gaya mata irin abincin da yake so wanda kusan duka na gargajiya ne, sanda yace mata har da ɗanwake sai da ta tsaya tana kallonsa, don ita a tunaninta mutane kamarsa basa ɗaukar abincin gargajiya da muhimmanci. Ya tambaye ta abinda take so itama kuma sai ta samu kanta da ture komai a ranta ta shiga gaya masa, kuma da kowacce kalma data faɗa tana ji kamar tana karkaɗe ragowar taraddadin dake ranta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73