Chapter 30
Chapter 30
Ma'aruf, don haka bata zana cewar abubuwan da ya rasa a baya zasu waiwayo shi nan kusa ba. A tunaninta yadda yarinyar tayi masa nisa haka tayi a zuciyarsa ma, a tunaninta ko zai neme ta sai shekaru sun ja tukunna a lokacin da hakan ba zai shafi tsarinta ba, amma har me tayi a yanzu da duniyarta zata fara girgizawa? Ta ƙara girgiza nata kan a fili tana cigaba da kallon fuskar Hamidan da kuma yadda ɗan ƙaramin ƙirjinta ke ɗagawa wajen fitar da numfashi mai nauyi, a ɗaya gefen ƙwaƙwalwar ta tana hango idanun Ma'aruf da suka tafi ɗauke da tsananin damuwa da kuma ƙaunar yarinyar dake nunawa ƙarara. Ta kuma girgiza kanta wannan karon a hankali, ai alƙawari ne cewar ba zata taɓa iya raba zuciyar Ma'aruf tare da kowa ba, sau nawa zata zana cewar shi nata ne ita kaɗai? Ba har da tsoron wannan yasa ta haɗa aurensa da yarinyar data san ba zata taɓa tasiri akansa fiye da ita ba? Ko uwar data haife shi a yanzu ta isa ta raba soyayyar sa tare da ita ne balle kuma wannan sabuwar halittar? Ta ƙara gurgiza kanta, ba lokacinta bane yanzu, ba lokacin da zata shigo rayuwarsu bane yanzu, bata tsara mata waje ba sam. Numfashin yarinyar har yanzu take kallo tana so ta kai karshen lissafinta... Lissafin da ta fara tun a lokacin da wayarta ta suɓuce daga hannayenta a lokacin da Ma'aruf ɗin ke mata bayanin samun yarinyar. Kuma wucewar wasu sakanni kawai, tunanin nata ya kai kan gaɓar da kwakwalwarta tayi tanadinsa tun a gida... Gaɓar da take shirin faruwa da zaren wani makamancin tarihin da ta taɓa ja a baya, fuskar Jamal ta haska a cikin kanta a ranar da ya shiga har cikin ɗakinta ya gaya mata cewa bata isa ba, wani murmushin ya suɓuce a fuskarta cike da fatan ruhinsa ya iya ganin yadda lokaci ke bata tarin damar dake ƙaryata kalamansa, tana fatan ace kabarinsa zai buɗe don yaga sabon saƙon da zata aika masa a daren yau wanda zai ƙara ƙaryata kalamansa fiye da cikin masaki. Ta miƙe a hankali ta nufi wajen da ta ajiye jakarta, kan teburin da Ma'aruf ya ajiye hularsa, zata yi komai ne hankalinta a kwance don ɗakin asibitin shi zame mata mafaka mai kauri daga duk wani tunanin da zai iya taɓa farinta. Ta gama tsara hotunan komai a cikin kanta har tayi musu fenti ma, sannan hannunta ya jawo jakar da niyyar buɗe ta.... *** A cikin ɗakin, da misalin ƙarfe goma na safe, Ruƙƙaya ta kalli mahaifiyarta da fararen idanunta dake shaida tashin hankali da kuma fargaba ƙulli-ƙulli, ta girgiza kanta tana share hawaye. "Wallahi Maamah Hanan ƙawata ce ta haɗa ni da ita, tace ta taɓa yin aiki da wata ƴaruwarta suna da ƙoƙari sosai, shi yasa banyi tunanin komai ba na ɗauke ta a lokacin, kuma itama ta taɓa fada min inda take amma na manta." Kukanta ya ƙaru lokacin da ta sake cewa. "Na shiga uku Maamah, idan na rasa Hamida ya zanyi da rayuwata? Da me Ma'aruf zai sake kallona idan har babu ita?" Hajiya Nafisa, mahaifiyar Ruƙayya na zaune a cikin ƙaton falon gidan na ƙasa, sanye take da wata doguwar riga irinta larabawan dubai, kanta daure da ƙaramin mayafin rigar yayi da wayarta ke riƙe a hannu. Idanunta na kallon Ruƙayyan ne da tsananin takaici bayan tashin hankalin da suka tashi dashi na ɓatan Hamida, sai jiya da daddare jirginta ya sauka daga Paris, don haka ko da ta dawo ta hawo samanta bata nemi kowa ba tunda maigidan ma baya ƙasar. Sai a safiyar yau da ta tashi ne sannan ta san Ruƙayya bata gidan saboda haka ta nemi Hamida da mai aikinta Mary amma sai su Jamila da Aisha masu share-share na gidan suka shaida mata cewar ai kwana biyu kenan Mary ta fita da Hamidan kuma bata dawo ba. Saboda haka kai tsaye ta kira Ruƙayyan ta shaida mata cewar ba'a san inda Hamida da Mary suke ba, kuma wucewar minti talatin sai gata ta ƙaraso cikin tashin hankalin da yafi nata, kuma a zaton ta da tazo kai tsaye zata kira Maryn ko kuma ta bita zuwa address ɗin gidansu ta karɓo yarinyar amma sai gashi tana gaya mata wai lambar Maryn bata shiga kuma ita bata san inda take ba. Allah ya sani idan har tana da wata matsala a rayuwarta to akan Ruƙayya ne, don babu abinda ta nema ta rasa a duniyar nan illa haɗin kan ƴar tata, ita kaɗai ce mace kuma babba a cikin maza huɗu amma a abubuwa da yawa ta kan gwammace mu'amalarta da mazan akan ita. Ta sani cewa tun daga lokacin da Ruƙayya ta fara hankali a duniya ta rasa ta, don daga lokacin da ta ɗauki zuciyarta ta danƙa a hannun Ma'aruf shikenan take zaune da ƙirjinta fanko, don bata kara marmarin saka wani a zuciyarta har ta kalle shi da daraja ba kamar shi, tun yana cikakkensa na mutum har ciwon da zata iya kira na hauka yazo ya same shi, haka akayi auren tana murna su suna jiye mata baƙin ciki, kuma ko kafin ta haihu takaici iri-iri sun sha shi, sai da ya juye ƙwaƙwalwar ta tsaf ya goge wannan Ruƙayyan da take a baya, ƴar gayu mai cike da izzar da ko a cikin ƴaƴan manya ake samun masu kwaikwayon ta. Ya canja mata yarinya zuwa bagidajiya irin matan da basu san komai ba sai zaman aure, ɗaya daga cikin abubuwan da ba zata manta ba shine lokacin aurenta har Lagos tasa aka nemo mata wasu ƙwararrun chefs(masu girki) mata bama maza ba don sanin halin Ma'aruf ɗin, amma wucewar sati guda Ruƙayyan ta bugo mata waya cewa ya sallame su yace shi girkinta yake so, kuma duk ƙin Rukayyan da girki haka ta ajiye ra'ayinta pa gefe ta shiga makarantar koyon girki tsawon watanni don kawai farin cikinsa, abubuwan da ta canja a rayuwarta don Ma'aruf baza su lissafu ba, don a abubuwa ne da ko na nesa zai hango su balle na kusa. Don haka a lokacin da ta fahimci cewa da gaske tana shirin rasa ƴar tata, a lokacin ta miƙe tsaye tayi wani yunƙuri da bai bawa Rukayyan zaɓin komai ba illa bin umarninta, kuma sa'arta ta zarce har bayan rabuwar tasu ta cigaba da jin maganganunta zuwa yardar da tayi ta auri Alhaji Ahmad, amma zata rantse cewar zamanta baiyi nisa a gidan Alhajin ba fitinanniyar zuciyarta ta sake karkatowa zuwa shafin da take zaton sun barshi kenan har abada wato Ma'aruf, don haka auren bai je koina ba ta fito. Ƴarta Hamida bata taɓa damunta ba don a tunaninta ita ba tasu bace, da tayi wayo ne mahaifinta zai karɓe ta koma wajensa, don haka bata ko waiwayarta a al'amuranta ta Ruƙayyan take yi. Ashe duk ub*n shirin da suke yi mata ita da ƙawarta akan alaƙarta da yaron nan Jawad a banza suke kashe ƴan kudadensu, ashe har yanzu zuciyarta bata dawo daga inda ta juya ba, Tunani take zata sake komawa wajen wannan yaron da a wajenta kudin da yake dashi ne kawai banbacinsa da wani mahaukacin. Har ta buɗe baki zata yi magana, Ahmad, ƙanin Ruƙayyan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73