Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

ni da ita game da wani al'amari a gidan nan, duk abinda na fada ko nayi daidai ne a wajenta, amma a karo na farko jiya mahaifiyarki ta bijire min akan wannan hukuncin, tace bata yarda ba, tace ba ni kadai na haife ki ba itama tana da nata haƙƙin akanki don haka ba zan siyar dake ga wasu mutane ba kamar yadda ta fassara al'amarin. Kuma bayan zuwan su Kawu Ibrahim a yau sai suma duk suka goyi bayanta, da ni da Kawu mallam da Baban kurna Amina mune kadai muka hango wannan al'amarin ta fuskar alkhairi da kuma cigaban ki wanda su basa gani. Don haka na san a shekarunki da kuma hankalin yabzu zaki iya banbance daidai da akasinta, don haka muka yanke cewar matsayar tana gare ki yanzu, duk ɓangaren da kika zaɓa shi zai fi rinjaye kuma maganar ta zauna kenan har abada, kar ki ga cewar na amsa musu acan, ki faɗi ra'ayinki Amina babu wanda zai taɓa ganin laifinki don rayuwar ki ce, mu duk ƴan kallo ne kawai. Don haka kije kiyi tunani daga yau zuwa gobe, saboda idan har ɓangaren mahaifiyarki kika ɗauka, ina so ne muje mu sami mutanen tare da su Kawu Ibrahim kafin su koma kuma kafin wani abu ma daga ɓangarensu yayi nisa. Kije kiyi tunani Amina." Shikenan! Shikenan sai duk bayanin ya ƙare da wannan jimlar, lokaci kuma ya fara bugawa da adadin awannin da zasu tadda goben, goben da Baba ta furta kamar tsawonta na shekara guda ne. Taji lokacin da ya miƙe ya zo ya wuce ta, taji shi ya zura takalmansa daga waje sannan taji ƙarar takunsa na nufar hanyar soro, sai kawai ta rufe idanunta gabaɗaya tana hadiye wani abu da bata sanshi ba a maƙogwaron ta. "Duk abinda mahaifinki ya fada haka ne ya faru Amina, kuma ba komai yasa nayi hakan ba sai don nemar miki ƴancinki..." Da wani sassanyan amo muryar Amma ta maye gurbin ta Baban tun kafin ta bude idanunta "... Ƴancinki nake nemar miki Amina, don ni na hango abinda mahaifinki ya kasa ganowa, mutanen nan masu kudi ne da gaske, kuma duk tsananin kirkin mai kuɗi a zaune yake cewar baya taba son mu'amalar rayuwarsa da talaka kamar mu, zasu taimaka, zasu yi zumunci kamar yadda ita wannan Hajiya Kilishin ke yi amma aure Amina, aure babban abu ne da shine linzamin rayuwarka ta duniya har zuwa lahira, don haka kowa ya sani cewa hakan ba ƙaramin abu bane ga rayuwar mutum da zai haɗa shi da kowa. Da ke muka je auren wani ɗansu a shekarun baya da suka wuce, kinga matar daya aura ai, kinga irin tarin dukiyar ubanta da danginsu, don ba a banza bahaushe ke cewa 'ƙwarya tabu ƙwarya ba... Kowa daidai dashi yake nema. Saboda haka Amina ko makaho yaji wannan zancen ya sani cewa mu ba daidai da mutanen nan muke ba, sun nemi aurenki ne kawai don son zuciyarsu..." Sai tayi shiru kamar tana kokarin haɗewa wani abu da ya taso mata ƙirji yayi sanadiyar canjawar muryarta. "Amina, ciwon yaron nan na 'Hauka' ne na tabbata suka yi masa ado da matsalar ƙwaƙwalwa kawai, kuma kin san wannan ba ƙaramar magana bace, kowa ya sani, su ma sun sani shi yasa basu tunkari kowa da wannan zancen ba sai mu, mu talakawa da aka mayar kamar ba mutane ba, mahaifinki dasu Kawu mallam suna ta danganta al'amari da ƙaddara, alhalin basu ƙara binciken komai akan yaron nan ba, amma ni nace idan har ƙaddarar ce me yasa basu kai ta ga irin ƴaƴan masu kudin da ɗaya ɗan nasu ya aura ba? me yasa sai a yanzu ne irinmu zasu yi musu amfani... Na sha gaya miki masu kuɗi basa kallon kowa sai kansu, suna ganin talaka kamar shi ya zaɓawa kansa rayuwar sa, kamar dama Allah ya halitto shi ne kawai don ya kawar musu da matsalolinsu. Rayuwarki zaki sadaukar musu idan har kika zaɓi tafiya Amina, don aure ba karamar gwagwarmaya bace ko da mutum mai hankali kuma wanda kake so balle babu duk biyun a naki, rayuwarki zaki sadaukar musu a banza, dukkan wani mafarki da burinki sai ya mutu wajen yi musu bautar da baza su san kina yi ba, don wannan sigar auren a wajensu, bata da banbanci da cewar siyen ki suka yi..." Ta sake yin shiru sakamakon yadda Aminar ta runtse ido da tasirin maganar, amma duk da haka sai ta cigaba. "...Annabi yayi gaskiya da yace kudi sune masifar ƙarshen duniya, a karo na ba adadi wallahi na sake yarda da hakan, don ban taɓa tunanin cewa mutum kamar mahaifinki zai iya faɗawa cikin tarkonsu ba..." Wannan karon kalaman suka daki zuciyar Amina da tasirin da yasa a lokaci guda ta ɗago ta kalle mahaifiyar tata tana girgiza kai. Ta sani dukkan abinda ta faɗa gaskiya ne, amma ba ta yarda da wannan hasashen nata na ƙarshe ba, ba zata taɓa yarda cewa kuɗi zasu rufewa Baba ido har ya mika ta ga inda zata cutu ba, haba mana! ta manta ne? Ta manta duk wannan tarin ƙaunar tasu dake tare dashi? Ta mata tarin sadaukarwar da yayi a rayuwarsa saboda su kawai? Sai dai kallon da Amman ke mata yasa ta sake sunkuyar da kanta a hakali tana rufe idanunta da ƙwalla ta taru a cikinsu, dukkan maganganun da Amma ta fada gaskiya ne ta sani amma har a lokacin ta kasa gasgata zancenta na karshe don ta sani cewa ko da numfashinta na ƙarshe a duniya ne zata yarda cewa ba zai taɓa mika ɗayansu ga inda zasu cutu ba... A kullum shi mai son gyara rayuwarsu ne. Ta kai hannu tana share idanunta lokacin da Amman itama tace. "Kije kiyi tunani zuwa goben Amina, ki auna kowanne ɓangare ki ga wanda yafi rinjaye, ni dai a matsayina na mahaifiyarki kuma mace kamar ki na gaya miki abinda nake ganin shine daidai" Ta rufe bakinta daidai lokacin sallamar su Adam daga makarantar dare ta kwararo a tsakar gidan. Shi da Hafsa ne suka karaso har cikin dakin bayan sun duba falon da babu kowa, da sauri Amina ta saka bayan hannunta ta share hawayenta kafin su ƙaraso da hayaniyarsu. "Amma kaina ciwo yake yi." Muryar Hafsan ta ambata tun kafin ta shigo ɗakin da kalar ƙorafinta na kullum yayin da Adam shima ya shiga ƙaryata ta. "Amma wallahi makaranta ce bata son zuwa gobe ƙarya take yi, yanzun nan fa har kusan faɗa fa suka yi ita da wasu a wajen ƴar tsohuwa, ba don nazo da wuri ba da ko kafi-kazan data siya ma baza ta samu ba." Babu wanda ya lura da yanayin dakin a cikinsu sai bayan da suka ga Amman bata basu amsa ba, tayi shiru kawai tana kallonsu, wanda hakan yasa Adam yasha jinin jikinsa, ya sake kallon fuskar Amman da kuma ta Amina ya tabbatarwa kansa cewa basu yi daidai da lokacin da ya kamata ba, don haka ya nufi kofa, sai dai har yasa ƙafarsa ɗaya a waje ya tuna da saƙon da aka bashi. "Au na manta wallahi, Yaya in kin fito ana kiranki a waje." Da haka ya juya yayi hanyar Kitchen ayana fadin zai sake zuwa yaci abinci.

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73