Skip to content

Chapter 32

Chapter 32

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

ranar da ta taɓa ganinsa, yana dariya a tsakanin mutanen dake taya shi murnar aurensa, babu shiri wani kukan mai ƙarfi ya sake suɓucewa a bakinta. A haka sai da duk wani babba na danginsu da kuma dangin Baba suka zo suka yi sannan aka rufa mata wani farin saƙin, aka lulluɓeta dashi har ƙasa sannan kuma sauran ƴanuwan Amman da basu kai irinsu Gwaggo Balkisa ba suka shiga fesa mata turare ana guɗa. Al'ada ce sabuwa ga duk wanda ya halarci wajen, irin dangin Baba da kuma sauran ƴan unguwa don haka abin ya birge kuma ya ƙayatar ga duk wanda ya gani, kuma duk da cewar ba wani abinci aka raba ba, amma kowa ya tafi yana yaba abinda akayi. "Na gaya miki su Nusaiba duk cewa suka yi baza su zo ba wai tunda ba ke kika fada musu ba, ba'a gaiyace su ba kenan." Fatima ta faɗa da daddare bayan an gama komai mutanen duk sun tafi, wadanda suka rage iya na cikin gidan ne kawai. "To ba shikenan ba, su sha zamansu. Dasu da masu karyatawa suna cewa karyane duk su ƙarata can, ranar da suka zo nemanki akace musu kina gidanki sai su san cewar da gaske ne." Ummi ta faɗa tana kallon Aminar wadda a yanzu ta canja zuwa wata doguwar riga daga cikin ɗinkin kayan sallarta, har yanzu bata fara amfani da kayan lefen nan ba duk kuwa da an karbo daga dinki, gani take kawai kamar basu gama tabbata nata ba har yanzu. Dukkaninsu suna zaune ne a cikin dakinsu tare da ƙawayen su Ummin da kuma ƙawayen Amina da basu fi biyar ba, don kamar yadda Ummin ta faɗa ne da yawansu da Fatima ta gaya musu cewa suka yi ƙarya ne basu yarda ba. Amina bata ce komai ba saurarensu kawai take yayin da take riƙe da ƙaramar ƴar Aunty Safiyya da tayi bacci a cinyarta, daga tsakar gida hayaniya ce kawai ke tashi cikin hausa da kuma zabarmanci daga ƴanuwan Amma, ƴaƴan Baban kurn dana Kawu Malam da kuma yayyensu Ummi duk suna nan, tabarmarsu daban ana ta hirar yaushe gamo, don ma ƴaƴan su Kawu Ibrahim dana Kawu Hamza basu ƙaraso daga Abuja bane, wanda su dama ba sa'anninsu bane, su hudu ne duk sunyi aure a can Abujan ɗaya ce kawai a Kaduna, don haka ko zasu zo tabbas sai ana i gobe ɗaurin auren ne tare da iyayensu, Kawu Hamza ne kawai yake da ƴa sa'ar su Aminar amma tana Ghana ta samu scholarship tana karatu. Amina ta sani cewar ƴanuwan mahaifinta suna da arziƙin da tun lokacin da ta gama karatu zasu iya daukar nauyin cigabanta, amma basu yi ɗin ba, don duk yadda zumuncinsu yake da karfi akwai raunin taimako a tsakaninsu, kowa yafi maida hankali kan iyalansa kawai, kuma Baba mutum ne mai son dogaro da kansa a komai shi yasa shima bai cika tambayarsu abu ba idan har ba wanda hannunsu ya miƙo masa ba. Ta lumshe idanunta tana sauraren hirar dasu Fatima ke yi a gefenta, Baba bai ƙara yi mata maganar auren ba har yau tun daga ranar da ta shaida masa amincewarta, amma a kodayaushe ta kalli fuskarsa sai taji ƙarfin gwiwarta na ƙaruwa, taji zata iya yin abinda yafi wannan ma idan har zai umarce ta. A hankali maganganun da ta gayawa Fatima ranar da tazo mata da labarin Ma'aruf suka shiga dawowa kunnenta. "Fatima, Baba yasha wahala akanmu a rayuwarsa, yaga tashin hankalin da ba zan iya lissafa miki ba duk saboda mu. Lokacin da nake shekara hudu, Amma tayi fama da wata irin rashin lafiya bayan haihuwar Aminu, Baba shi yayi ɗawainiyar konai damu har tsawon shekara guda kafin ta warware. Lokacin da ina aji ɗaya a sakandire nayi wata rashin lafiyar ciwon ƙafafu har bana iya tafiya, wani abokinsa ya kwantanta masa wajen wani mai magani a garin Benue, ni dashi kawai muka tafi, daren farko a hanya mota ta lalace mana gashi motocin dake wucewa basa tsayawa saboda gudun ƴan fashi, a bayansa ya goya ni Fatima, muka dinga bi ta daji tare da sauran mutanen motar har washegari kafin Allah ya taimaka mu isa wani ƙauye. Lokacin da zanyi jarabawar shiga sakandire, Baba ya sadaukar da lokacinsa da komai wajen koya min karatu ba dare ba rana, idan ya dawo daga kasuwa yana gyangyadi yana hamma zamu yi karatun nan, ranar da sakamakon jarabawar ya fito kuma naci, ranar na fara ganin hawaye a idanun Baffa, hawayen farin ciki. Sanda Maryam bata da lafiya kuma karayar arziƙi ta same shi, kin sani Fatima, kin san yadda Baba ya koma kamar mai roƙo yana bi kusufa-kusafa don tara adadin kudin da ake buƙata. Kullum so yake mu girma, mu zama wasu mutane da al'umma zasu amfana suyi alfahari dasu, don haka ba lallai ne mu hango fa'idar wannan hukuncin nasa a yanzu ba, amma na tabbatar miki Baba ba zai yarda da zancen auren ne haka kawai ba, yace ya amsa musu ne saboda nauyin idanunsu da yaji, amma ni na sani cewar akwai wani abu daban da yasa ya amsa wanda ba lallai ne dukkanmu mu fahimce shi yanzu ba. Kema na yarda da maganarki kamar yadda na yarda da ta Amma, sai dai bana jin zuciyata zata dauki taku sama da tasa, don ban san wane irin butulci zanyi ba idan har na kunyata mahaifina a idon duniya, gwara ko meye ya same ni da inyi sanadin hakan." Kuma tun daga lokacin, shikenan ta kashe bakin Fatiman, bata kara cewa komai ba, bata ƙara ƙalubalantar ta da komai ba, ta fauwalawa ubangiji al'amarin kamar yadda itama tayi, har ta saki jikinta cikin su Ummi itama ta siya atamfar nan ta kai ɗinki. "Gobe zanje in karbo ɗinkina, kuma zamu je ni da Maryam wajen masu sarƙar nan mu ƙara yi musu tuni." Fatiman ta faɗa tana katse tunaninta. Sai ta gyada kai kawai sannan tace. "Ɗazu Maryam take gaya min, wai ta samo me zuwa ta mana ƙunshi ma." "Ƙunshi a ina? Me zuwa gidan ce zata miki? Ai kar ma ku fara wannan zancen, kuɗi zaki karɓo zoo road zamu tafi jibi-jibin nan, idan aka gyara miki gashin nan naki da hannayenki, ba wanda za'a sake yiwa bayanin cewa ke amarya ce." Ummi ta faɗa, kuma tana ƙarashewa wata ƙawarsu ma ta ɗauka da faɗin. "Ni wallahi naga ta kara haske ma akan ranar da muka zo daga kasuwa." "To kina raba amare da gyare-gyaren jiki ne? Kawai ki tambaye ta sirrin tunda kema kin kusa fara naki." Momi ta faɗa suna ƙyalƙyalewa da dariya, Amina kuwa ta haɗiye yawu, don ita bata san wani abu gyaran jiki ba, vasiline ɗin da take shafawa kullum shine dai, robar ko ƙarewa bata yi ba balle ta canja ko kuma ta waiwayi mayukan cikin lefen nan, abinda ta sani kawai shine idan har da gaske tayi fari to kuwa tabbas na tsora ne. Don Allah ya sani idanunsa kaɗai idan ta tuno zuciyarta na bugawa da sautin dake barazanar saka ta kuka duk da ƙwarin gwiwar da take ji, tsoron daban ne don bata san me shi da kuma zuciyarsa suka tanadar mata ba... Ta rufe nata idanun a hankali tana jiyo

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73