Chapter 51
Chapter 51
mudubi, ya nuna abinda zahirin ke iya haifarwa! *** Ƙarfe bakwai na safe. Idan akwai wani abu daya rage a rayuwar Ma'ruf ta baya, shine ƙaunarsa da football (ƙwallon kafa) shi kaɗai ne abu guda ɗaya bayan sunansa da kuma kamanninsa da zai ce basu canja daga Ma'aruf ɗin da yake a baya ba, Ma'aruf ɗin da yake kafin rasuwar Jamal, amma duk wani abu bayan hakan komai da yake yi ba rayuwarsa bace. Son football ɗin ne kawai yayi yawa a zuciyarsa da ba zai iya barinsa ba, shi yasa yawanci duk weekend da safe yana stadium ɗin Sani Abacha, team ne dasu guda da suke da ranakun yin wasa da kuma ranakun training, sannan yana ɗaya daga cikin members ɗin dake kula da wajen ma, duk wani taimakon harkar kudi da ake yi a wajen su suke badawa, idan ya gama ya fito haka zaka ga samarin nan ma'aikatan wajen sun biyo bayansa har wajen mota don ya sallame su, don haka babu wanda bai sanshi ba a wajen. Yau asabar can yayi niyyar zuwa don tun da ya dawo daga sallar asuba ya shirya, amma yayi-yayi da motarsa taƙi tashi, jiya lafiya lau ya ajiye ta kuma a saninsa bata da wata matsala amma sharrin karfe ance ba abinda ba zai iya ba, haka ya hakura ya rabu da ita, sai kawai ya fito da ball ɗin sa daga booth ɗin motar ya shiga training ɗin da ya saba a compound ɗin gidan. Kusan ƙarfe bakwai da rabi lokacin da wayarsa tayi ƙara daga can saman motar inda ya ajiye ta, kuma sai da ya kai ball din sama sau biyu sannan yazo ya ɗauka, Martha ce. "Barka da safiya sir, RTL sun bugo waya cewa yau zasu sauka a Kano, don haka meeting din zai zama karfe huɗu na yamma." Ta zayyano dukkan bayanin da harshen turanci, hannunsa ya zura cikin kansa don kwata-kwata ya manta da zancen cewa zasu iya yin meeting din a yau, yayi niyyar babu inda zai fita zai zauna ya huta ne don Allah ya sani ya aikatau a cikin satin nan gashi jiya ma bai wani samu bacci mai yawa ba. A hankali ya cije leɓɓensa yayin da ta cigaba da yi masa bayanin cewar sunyi waya da Faruq da sauran board members ɗin nasu ta shaida musu komai, shi gabadaya ya manta ma da nasa takardun da ya kamata ya karanta kafin a shiga meeting din jiya a Office. "Sannan kuma Sir ka manta papers na background Information din a Office, dole zaka buƙace su kafin a shiga meeting ɗin." Ya sake motsa hannunsa a cikin gashin kansa. "Na sani Martha, yanzu kuma ban san ya za'ayi ba gashi motata taƙi tashi, amma bari na kira Ishaq sai a ɗauko min tasa." "Okay sir." Ta amsa muryarta a ƙasa. Da haka suka gama wayar sannan ya shiga laluben nambar Ishaq ɗin da har yanzu bai dawo ba, bugu ɗaya biyu kuwa ya ɗaga. "A ina ka ajiye muƙullin motarka?" "Me za'ayi?" Ishaq ɗin ya amsa daga cikin wayar. "Motata ta samu matsala ne kuma ina da meeting anjima." "Ka kira Jamilun?" (Makanikensu.) "Ban kira shi ba, tunani nake sai anjima tukunna saboda gabaɗaya na manta da meeting ɗin ne." Dariya Ishaq ɗin yayi daga ciki yace. "Wallahi tayar motar nan a sace na tafi na barta, I don't know ma ya take take yanzu." Ya girgiza kansa kafin yace. "Baka da amfani." Da haka ya kashe wayarsa, ya kira Malam Sani. "Yallaɓai Barka da safiya." "Barka dai Malam Sani, nace dan Allah akwai mota a cikin gida ne?" "Ai kuwa Babu ranka ya daɗe, don su Baffa sun tafi gona a tasa shi da Baba Usman, ta Hajiya kuma a tsaye take tun wancan watan don haka na baro za'a kaita asibiti da ta Mami, school bus din kuma ka ganni da ita a ƴankaba." Sai kawai ya gyaɗa kansa alamun ya fahimta kafin suyi sallama ya kashe wayar, Martha ya sake kira yace ta kira direban kamfanin nasu kawai ya kawo ta kawo masa takardun. Da haka ya mayar da ball ɗin cikin booth ɗin motar sannan yayi hanyar cikin gidan, ya shiga cikin falon ya shiga cikin a lokaci guda da ƙamshin wani air freshener mai sanyi ya shiga hancinsa, yana tabbatar masa da cewar matar gidan ta tashi kenan, ya nufi hanyar dakinsa don yayi wanka ya shirya yayin da yanayin fuskarta a jiya da daddare ke haskawa a idonsa da kuma waɗannan siraran ƙafafun nata. *** Ƙarar kwankwasa kofar gidan ta shiga kunnen Amina a lokacin da take kammala aikinta na karshe a kitchen, ta san ba Ma'aruf bane, don a yanzu ƙwaƙwalwarta ta haddace yanayin nasa bugun kofar duk da ba kullum yake manta mukullinsa ba. Ta kashe gas ɗin da sauri sannan ta goge hannunta kafin ta fito, har yanzu wani iri take jin jikinta, mafarkin jiyan nan dana abinda ya faru bai gama barin tunaninta ba sam, don bayan ta koma ɗaki a jiyan bata iya komawa bacci ba, sallah tayi sannan ta zauna tunane-tunane har lokacin asuba, kuma sai bayan asubar sannan bacci ya ɗauke ta, baccin da baiyi nisa ba ƙarar wani abu ta tashe ta. Kuma ba'a dade ba wata yunwa ta dame ta, don haka a gurguje ta karasa karatun Azkar ɗinta sannan tayi wanka kafin ta fito zuwa kitchen, inda anan ta hango Ma'aruf ta cikin sliding windows ɗin dake wajen sink yana ball, ta fahimci ƙarar data tashe ta kenan. Yana sanye da wata loose-fitted riga fara kal, da bakin wando irin na sports, (track pants) da kuma takalmin ball, rigar ta fito da ƙirar jikinsa sosai, sannan yadda yake juya ball din a kafafunsa cikin kwarewa ya tabbatar mata cewar da a cikin filin ball yake tabbas zai iya yin kokarin ture kowa ya ci. Ta daɗe tsaye tana kallonsa cike da mamaki, don bata taɓa tunanin mutum so committed kamar shi zai samu irin wannan lokacin ba, ta fahimci a kullum ƙara sanin wasu halayensa dake bata mamaki take kuma har yanzu ba'a zo kan wani abu guda da tayi hasashensa game dashi a baya ya zama gaskiya ba. Komai zuwa yake saɓanin tunaninta, ita har yanzu bata ga wata alama ta ciwon nan nasa da ta riga ta gama tsorota dashi ba, shi yasa zuciyarta ke ta tantama ma akan idan shi ya rubuto mata wannan saƙon, har Fatima ta gayawa cewa in dai ba warkewa yayi ba, to ba koyaushe ciwon ke tashi ba. Shi yasa tare suka yarda da tsarinta na kyautata zamansu, da tunanin idan ya san bata da niyyar cutar dashi, ba lallai yayi mata wani abun ba duk lokacin da ciwon nasa ya tashi. Sai dai ita bata tsara da yadda zuciyarta ke jin dadi tun lokacin da ya fara cin abincin nata ba, jiya duk da rikicewar mafarkin nan da take ciki sai da zuciyarta ta faɗa ganin kwanukan abincinta a gefensa... Tunanin hakan ya tuna mata da yadda ya riƙe hannunta a lokacin, har yanzu tana jin kamar shatin yatsun sa akan fatar ta, tana jin kamar akwai wani abu dake ƙonewa a jikinta saboda tasirin yadda yatsun nasa suka zagaye duka hannun nata gabaɗaya. Da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73