Skip to content

Chapter 70

Chapter 70

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

ne. "Ina son chocolate, sannan zan sha lemon zoɓo a koina kuma a kodayaushe." Ta fada lokacin da yake tambayarta abinda take so na kayan kwaɗayi. Ya gyada kansa. "Naga alama, cox naga zoɓo da yawa a fridge dinki." Ta gyada kanta a hankali itama. "Ina ga ba zan taɓa iya dadewa babu shi ba a koina." "Wow, I like the enthusiasm."(ina son kwarin gwiwar nan.) Muryarsa ta gito da slamun cewa shima ya fara jin dadin sakewarta. Sai tayi wani guntun murmushi da bata san daga ina ya fito ba tana kallon abinda take zubawa. "Wane kalar chocolate kika fi so?" Da alama so yake hirar ta cigaba da yin nisa. "Kowanne." Wannan karon muryarta ta sake fitowa kamar silin gashin dake faɗowa ƙasa a hankali ba tare da ta dago ba. "Chocolate bai dame ni ba amma I always enjoy Ferraro Rocher." (Ina jin dadin Ferraro Rocher.) Bata taɓa jin ko sunan ba, kuma sai Allah ya taimake ta kafin tayi tunanin abinda zata faɗa, wayarsa dake can kan table ɗin daya baro ta ta shiga ƙara, don haka ya karbi plate din da gama zubawa ya tafi wajen, ya ajiye plate shi akan table din sannan ya kara wayar a kunnensa ya shiga magana da wani cikin Pidgin english, irin tsantsar Pidgin din da ita bata taba ji ba ma, amma kuma sai yayi mata dadi, yadda sautin muryarsa yake haɗewa cikin accent ɗin da kana ji ka san ya fito ne daga Jinsin Hausa/Fulani. 'Matar ƴan gayu.' Haka Aminu yayi ta tsokanarta ɗazu, kuma ita kanta duk da hargitsin yanayin da take ciki ta sani cewa kamar yadda Hajiya Kilishi ta faɗa ne, idan banda kaddara ko zata mutu sau ɗari ta dawo Ma'aruf yafi karfinta, don a yanzu da kowacce wucewar rana tana ƙara gane cewa yafi ƙarfin hangen da take masa a lokacin da ta yarda da auren nan. Shi yasa ko a yanzu kawai ƙwaƙwalwarta ta kasa auna mata adadin kuɗin da ya kashe wajen kama ɗakin nan don kwana ɗaya kawai. Ta ɗebo farfesun kifi na ƙarshe a cikin wani ɗan bowl sannan ta juyo tana hango shi daga can inda ya zauna a jikin table din yana magana, kuma kayan jikinsa na T-shirt da gajeran wandon nan suka sake tuna mata da wanda ke jikinta itama, ba shiri ta hadiye wani yawu a maƙogwaronta tana jinjinawa kaddara, don in ba ƙaddarar ba ba zata taba hango kanta a irin wannan yanayin tare da wani namiji kuma dadin daɗawa a Hotel ba. Ƙafafunta duka karasa a hankali har gabansa, ta tsaya daga gefensa sanda ya dago daga rubuta wani abu da yayi a jikin wata ƴar jotter yana kallonta, ya taimaka ya ture mata kayansa dake kan table din kafin ta ajiye plate din a hankali kusa da dayan sannan ta juya niyyar dauko ruwa wanda tun dazu ta ganshi a fridge din dake can gefe, amma sai kawai taji ya riƙo hannunta na hagu, dogwayen yatsunsa suka ratsa cikin nata yana riko ta, a lokaci guda numfashinta ya katse a ƙirjinta yayin da yatsunta suka yi sanyi kalau! Ya sake riƙo hannun nata sosai sannan ya jawo ta baya ta dawo gabansa, shi yana zaune ita kuma tana tsaye a gabansa da kafafunta duk a waje, ba shiri ta dunƙule tafin kafarta akan sassanyan marbles din ɗakin, sannan ta rufe idanunta a hankali tana jin yadda yake motsa yatsunsa a cikin nata. Ta buɗe su daidai sanda ya gama wayar, idonsa yana kan kafafunta ne da har yanzu ta rasa me yake gani a jikinsu, kuma kafin ta gama tunanin hakan taji ya jawo ta zuwa kasa a hankali, ya durƙusar da ita a gabansa, dab dashi sosai wanda hakan yasa ta sunkuyar da idanunta ƙasa tana cije gefen lebbenta. "Wata magana nake son muyi Please..." Yadda muuryarsa a fito a hankali da kuma zurfi ya haddasa faduwa da saukar numfashinta. "Zamu iya yi yanzu?" Ya ƙara tambaya a lokacin da take kokarin tsayar da iska a kirjinta, da kyar ta daure ta daga kanta sau biyu babu kari. Shina ya gyada nasa kan a hankali yana cigaba da kallon fuskarta. "Na sani a yadda komai ya fara a tsakaninmu akwai tarin irin tunanin da kike yi akaina, na san an gaya miki tarin abubuwan da ba lallai ne na iya ƙaryata miki su ba, kinji wanene ni ta bangare da yawa na sani Amina, kuma har nima na bada gudunmawa wajen saka miki wani tunanin akaina tun a wancan lokacin, wani abu da nayi shi ne ba don komai ba sai don in hana faruwar auren a tsakanin mu." Yayi shiru ya cigaba da kallon fuskarta, kuma ganin yanayinta bai canja ba yasa shi cigaba. "I'm a mess Amina, akwai tarin abubuwan dake gabana kuma a tsakiyarsu ne na tsinci zancen aurenmu wanda ni tun bayan lokacin dana rabu da Ruƙayya ban kara tunanin cewa zan sake aure ba, abubuwa sunyi min yawan da bana son nauyin komai ya sake ƙaruwa akaina, saboda haka wannan wasiƙar da na baki nayi ne don in tsorata ki ta hanyar da zai sa ki ƙi yarda sabida su Baffa baza su saurare ni ba a lokacin, abinda na manta a wannan lokacin shine ban isa in canja ƙaddarar da Allah ya hukunta ba tunda hakan babu abinda ya canja." A wannan lokacin numfashin dake ƙirjin Amina ya kasa tsayawa waje guda, sai kokari take dashi kamar kifin da ya fito daga rywa yana wutsil-wutsil, hasken fitukub dakin ya karu a idanunta yayin da wata iska ta shiga busuwa daga maka-makan windunan dskin kasancewar a sama suke. "Daga ranar da na fara ganinki Amina, nayi nadamar abinda nayi, na san cewa ban kyauta ba da har na saka wannan tsoron da na gani a cikin idanunki, wanda duk da hakan kuma bai hana ki kyautata min ba, bai hana ki nuna min kirkin ki da kuma halayenki na gari ba, kuma yanzu wannan kirkin naki nake kwaɗayin cigaba da samu Amina, ina son nutsuwar da nake samu a wajenki don itace babban abinda nake bukata wajen tafiyar da rayuwata a yanzu, shi yasa nake rokonki da ki manta duk wani hasashe da kike yi kaina Please, ki bani damar da zamu yi normal life kamar yadda kowa yake yi, wallahi nayi alkawarin ba zan taɓa cutar dake ba insha Allah." "....Kamar yadda na faɗa miki mafitar ta riga tazo hannunki Amina, Kilishi ta bude miki kofar samun nasarar da ita kanta bata sani ba, so nake ki dauki dukkan maganganunta kiyi wa taki zuciyar ado dasu Amina, don takunta zaki bi, dukkan abinda ta fada kema shi zaki yi, banbancin da za'a samu tsakanin ke da ita shine, ke ita zaki yiwa Amina, ita zaki lulluɓe da rigar amincinki ba kowa ba, ita zaki zamewa farar wutar da ba zata taɓa sanin cewa ƙonata kike yi ba. Kuma hanyar farko da hakan zata kasance shine idan kika sami soyayyar mijinki..." Kalaman da Amma na ɗazu su suka biyo bayan dukkanin bayanin Ma'aruf a cikin kan Amina, ta tuna yadda take kallon Amman cike da ƙarin bayanin da bata furta ba Amman ta cigaba. "Kilishi ta gaya miki cewa soyayyar mijinta ta fara samu a

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73