Chapter 40
Chapter 40
ƙofofin hancinsa, me ya zata dama ga yarinyar da yayi wa wannan barazanar, don haka ya sani cewar yanzu a farko dole ne yayi kokarin kore wannan tsoron nata game dashi, yasa ta fahimci cewa a yanzu ba abinda ke gabansa game da ita kenan ba. "Ki kwantar da hankalinki, na shigo ne don kawai mu gaisa ki san cewar ba ke kaɗai ce a gidan ba, idan akwai wani abu da kike bukata kuma zaki iya gaya min..." Kalaman suka daki zuciyar Amina ta yadda numfashinta ya tsaya cak! Wani abu a cikin kanta ya gaya mata cewar hatta lokaci sai da yayi shawara sau biyu kafin ya motsa. Kallonsa kawai take yi da tsananin mamakin da ta kasa auna shi a mizanin hankalinta. Ya fahimci ba zata yi magana ba don haka ta ga ya sake riƙe hannun kofar sannan ya furta mata. "Sai da safe." Ya rufe ƙofar daidai lokacin da kafafunta suka kasa ɗaukarta gabaɗaya. ** Hasken safiyar dake shigowa ta liner labulen ne ya tada ita, ta kifta idanunta tana kallon yadda wajen yayi mata kyau a ido, yadda hasken ya haɗe da kalar labulen dama liner yana ratsowa ta cikinsu, amma duk da kyan nasa sai taji kewar gida ta kamata, taji tana kewar ɗakinsu har ma da katifarta don ba zata iya tuna rana ta ƙarshe da taje wani wajen ta kwana ba tun bayan data gama makarantar Boarding fin da tayi. Ta rufe idanunta ta buɗe tana sake kallon windon wanda tsawon yadda take ganinsa yasa ta tuna cewa a ƙasa take, akan carpet din nan, don anan bacci ya dauke ta bayan zuciyarta ta cika da sake-saken al'amarin da ta kasa ganewa. Ba irin tunanin da bata yi ba da abinda bai zo kanta ba a jiyan nan, amma daga ƙarshe da ta tattara duk lissafinta da kuma abubuwan da aka gaya mata dama abinda ta shirya, sai taga cewar bata da wani zaɓi illa ta fara fahimtar manufarsa akanta kafin ta yanke hukuncin da zata iya kare kanta dashi. Ta miƙe zaune a hankali tana son daidaita ganinta, a sannan ne ƙwaƙwalwarta ta tuna mata cewar bata yi sallar asuba har gari ya waye haka, ƴar wayarta dake gefe ta jawo tana tunanin yadda akayi alarm ɗinta bai tashe ta ba amma sai ta tarar ta mutu saboda ba caji, don haka ta mike da sauri ta nufi bandakin a lokacin da idanunta suka sake kallon ƙofar dakin ta tabbatar muƙullin data kulle ta dashi yana jiki har yanzu kafin ta shiga ciki. Bayan ta idar da sallar ta daɗe tana addu'ar neman gafara da kuma ƙwarin gwiwar tunkarar duk abinda ke gabanta kafin ta mike, a cikin akwatin kayan kwalliyar nan ta samo sabulu, ta shiga tayi wanka, kuma duk da cewar komai sabo ne a wajenta bata sha wahalar gane kan fanfunan dake ciki ba tayi wankan ta fito. Ta dawo cikin ɗakin dake ƙara tuna mata cewar rayuwarta ta canja da gaske, don har yanzu yanayin da take ciki ba zata iya fassarashi ba, aayƙin da take ji daya ne kawai na cewar ƴan gidansu zasu zo, don haka da ƙyar ta ture duk wani tunani dake ranta ta shirya cikin wata doguwar rigar da hannunta ya fara kaiwa a cikin kayan dasu Ummi suka jera mata jiya, bata ɗaura ɗankwalin ba sai kawai ta yafa shi akanta. Ta kalli kanta a mudubin ɗakin tana ganin yadda idanunta suka fara washewa da kukan da tasha a jiya kafin tasa duka hannayenta tana gyara zaman ɗankwalin akanta, siraran awarwarayen da har yanzu ke hannunta suka shiga rawa suna tuna mata da zamansu, don haka tayi saurin cire su gabaɗaya ta ajiye akan mudubin sannan ta juya ta kalli kofar dakin. Kai tsaye ta ture komai a ranta ta nufi kofar ta buɗe ta, korido ne mai dan tsawo dake dauke da ƙofofin ɗakuna guda uku, ta sani cewa dole a daya daga cikin dakunan ya kwana tunda yace mata yana nan, don haka bata ko yi gigin bude kowacce ba kafafunta suka taka suka fita zuwa falo, anan ne, zuciyarta ta narke da kowanne abu na cikinsa dake shaida haɗuwarsu tun daga nesan da take, komai yana haɗewa cikin kalar ɗanuwansa cikin wani simple ado daya dace da wurin. Ta jinjina kai a hankali kafin ƙafarta ta tafi zuwa daya korido ɗin anan, tana jin yadda fatarta ke sulalewa akan santsin wajen duk da ƙurar data lura akwai, kofar wani katon kitchen anan da komai na cikinsa ash ne da kuma fari, akwai store mai ɗan girma data buɗa ta tarar da kayanta fal a ciki, wasu ma duk a cikin buhu suke ba'a buɗe ba. Ta dade tsaye tana kallon kayan da kuma tsarin drawers din kitchen din kafin ta hango wats kofa a can gefen fridge, taje ta bude ta, hanya ce mai dan fadi dake zagayawa kowanne bangare na gidan, inda daga can jikin katangar kuma ta hango wata kofa data tabbatar ta nan ne ake shiga cikin gidansu. Ta rufe kofar ta dawo tana sake komawa store din nan don ganin kayanta, tsji wani abu kamar magana amma bata tabbatar ba ta cigaba da duba kayan. A lokacin ne kuma ta jiyo muryarsa, kamar irin ruwan saman dake sauka a lokaci guda tana ƙarasowa hanyar kitchen ɗin, ba shiri hannayenta suka nemi hannun kifar store ɗin amma kafin ta iya rufe ta gabadaya, ya karaso don hannun nata ya tsaya cak tare da numfashinta, idanunta suka hango mata shi ta zirin ƙofar da bai gama rufuwa ba, kuma a lokaci guda taji zuciyarta tayi kuli-kulin kubra ta faɗo daga wata sama mai nisa. Ashe jiya bata lura da tsawonsa sosai ba, a yanzu daya canja cikin wani yadi kalar sararin samaniya da irin ɗinkin rigar da bai kai gwiwa ba, bata jin a cikin abokan Aminu gabadaya data sani akwai wanda zata iya kwatanta shi tare dashi. Ta hadiye yawu tana kallon yadda idanunsa ke lumshewa da sauraren abinda ake gaya masa ta cikin wayar kafin yayi magana. "Me kace?" Muryarsa a hankali ta fito, da wani irin amon da yasa jikinta girgizawa, numfashinta yana katsewa ba gaira ba dalili. Me yazo yi ne ma a kitchen din? Ta ga ya girgiza kansa sannan ya zura hannayensa cikin gashin kansa yana motsa su, a lokacin ne kuma iska ta buso mata da ƙamshin turarensa, wani abu kamar ƙamshin musk ko mint, ko kuma meye hancin nata ya jiyo mata, sai kawai ta juyar da kanta gefe yayin da muryarsa ta sake fitowa. "That issue aside Faruk, ba yanzu zamu neme shi ba, let's give him atleast two weeks to settle down, (mu bashi kamar sati biyu da zai huta) babu wuya zamu kama shi a sannan. Yanzu let's just focus akan waɗannan mutanen, I have somewhere to be now amma zan kira Martha ta min sending duk wani back-up da muke dashi akansu, zuwa yamma we decide where to meet sai ka kawo naka mu ga me zamu fitar." Murza ƴan yatsunta kawai Amina ke yi tana fatan ya juya ya fita, amma ga mamakinta sai kawai taji wata muryar mace ta taho tana faɗin. "Yaya baka ganta bane?" Kuma kafin ƙwaƙwalwar ta ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73