Skip to content

Chapter 31

Chapter 31

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

dake bin Ashraf (wanda yayi aure) ya hawo saman daga shi sai gajeren wando da riga. "Wai Maamah ki dawo ƙasar nan baki gaya mana ba. Sai da na shigo wajen 12 maigadi yake ce min ai kin dawo." Ya faɗa yana ƙarasowa kusa da ita ya zauna, kuma sai a lokacin idonsa ya kai kan Rukayya dake kuka. "Me ya faru?" Yayi tambayar ga dukkansu biyu. Hajiya Nafisa ta nisa sannan ta bashi amsa. "Hamida ce ba'a gani ba, ita da mai kula da ita." "What? Ta yaya? Tun yaushe?" "Itama bata gidan ai, sai da na dawo tukunna." Ransa a ɓace yace. "Me nake gaya mata a gidan nan Maamah, don me zata dauko wata ƙedara wai ita zata dinga kula da ƴarta, wai don ta iya turanci? Turancin banza su Hausawan ba su iya turancin bane?" Hajiya Nafisa ta girgiza kanta. "Ajiye wannan zancen Ahmad tunda komai ya faru, yanzu nemanta ne a gabanmu. Ya za'ayi?" Kafin ya bada amsa, Ibrahim ya shigo riƙe da wayarsa a hannu yana faɗin. "Is it true yarinyar nan ta ɓata? Umar just called me now wai ya ganki a waje ɗazu kuna tambayar Hamida." Hajiya Nafisa ta gyaɗa kanta don ita yake kallo sanda ya shigo yana tambayar. "Ƴansanda ɗin dake gadi a bakin titi muka tambaya suka ce mana tun shekaranjiya Maryn ta fita da Hamidan kuma basu dawo ba." "Ya salam! This is bad, yanzu me ake ciki?" Tambayar tasa Ruƙayya sake fashewa da kuka. Ahmad yace. "Akwai wani abokin Ashraf da ya taɓa zuwa nan yace min ya san ita mai aikin, ban ɗauko wayata daga ɗaki ba, Ibrahim kira shi." Ya kalle shi. "Wa zan kira?" "Ashraf ɗin zaka kira kace ya baka number B-man." Wayar Hajiya Nafisa tayi kara a lokacin, ta kalli number dake kiran nata, mahaifinsu ne don lokacin da Rukayyan ta dawo tace bata san inda Maryn take ba shi ta kira ta gaya masa halin da ake ciki. Ta ɗauki kiran ta kara a kunnenta, gaya mata yake yi cewa yasa an turo da ƴan sanda gidan zasu zo su nemi bayanai don su kamo Maryn. Kuma bayan ta sauke wayar kallon Rukayyan ta cigaba da yi a lokacin Amir ɗan autansu ya shigo rike da kofin shayinsa ya zauna a gefenta yana bata hakuri. Gayawa zuciyarta take yi cewa ba zata sake kuskuren rasa ƴarta ba a karo na biyu, bata son Ma'ruf amma idan har yanzu shine zaɓin Ruƙayya, shi abinda zai daidaita rayuwarta, to zata hakura kawai ta karɓi wannan ƙaddarar, zata dawo mata da Ma'aruf cikin rayuwarta ko ta wace hanya. *** "Allah yayi miki albarka, Allah ya haskaka rayuwarki, Allah yasa ki zama haske a cikin gidan aurenki, Allah yayi riƙo da hannayenki wajen kyautata zaman ibadarki, Allah yasa ki zama sanyin idaniyar mijinki, Allah yasa masa tausayinki a zuciyarsa, Allah ya bashi ikon sauke nauyin duk wani hakkinki, Allah yasa ku zamewa junaku inuwar salama har a ranar alƙiyama, Allah ya sanya albarka a zuri'ar da zaku samu, Allah ya tashi rayukanku cikin rahamar ibadarku a lokacin da zaku koma gare shi..." Duk wannan addu'ar tana fitowa ne yayin da ruwa ke sauka akan Amina daga bakin wata dattijuwa ƴaruwar Amma mai suna Gwaggo Balkisa da suka zo daga Nijar a lokacin da gidansu Amina ya cika da ɗimbin jama'ar dake shaida Kamu ko kuma wankan amarya da a ƙa'idar zuri'arsu Amma ake yinshi kwanaki kafin ɗaurin aure, al'amarin da yazo musu babu shiri don kwatsam suka samu baƙoncin ƴanuwan Amman tun daga Nijar mutane har motoci biyu. "Bikin ƴarki ta fari guda kice ba sai mun zo ba Halima? Idan kince ku komai yazo muku cikin gaggawa an gaya miki mu yanzu muka fara tanadi ne? Har a aika da katinan ɗaurin aure amma ace wai iya maza ne kawai zasu taho? Yau ko Amina ba ƴarki ta sunna bace kina tunanin zamu ƙi halartar bikinta ko da kuwa tsakaninmu daku nisan bangon duniya ne? Amina tana tuna yadda Amman ta sunkuyar da kanta tana saurare kafin tayi musu bayanin yadda al'amarin auren yazo, kuma fahimtar al'amarin ya kawo cece-kuce a tsakaninsu, waɗanda suke tsofaffi a ciki basu ga aibin komai ba don sun yarda cewa dama uba ke da ikon bada ƴarsa budurwa zamani ne kawai ya canja komai, amma sauran suma sai tunaninsu ya zama irin na Amma cewar tasirin taimakon da Hajiya Kilishi ke yiwa Baba shi ya rufe idanunsa saboda auren bai kamata ba. Sai da aka kira Aminan ta tabbatar musu cewa ita ta amsa auren da bakinta sannan kowannensu yayi shiru. Ta faɗi hakan a lokacin da take kallon idanun Amma dake ɗauke da sauran labarin da bata ƙarasa musu ba, sauran labarin da ko ƴanuwan Baban basu sanshi ba, tana jin yadda zuciyarta ke bugu akai-akai cike da fatan kar nauyin kalaman su rinjayi zuciyar Amma a wannan lokacin, amma bata yi maganar ba, bata ce komai ba. Kuma hakan yana tuna mata da matsayinta na Ammar su, matar da tunda suka taso a rayuwarsu babu wata rana da zasu iya ɗorar da saɓanin cewa faɗa ya shiga tsakaninta da mahaifinsu, kuma ba wai ba'ayi ba, ta tabbata ana yi ma fiye da tarin wasu gidajen auren, kawai babu ƙofar da zasu gane ne. Ta tuna watarana da taji ta tana yiwa Aunty Safiyya nasiha bayan wani saɓani da ya shiga tsakaninta da mijinta. "Sirrin mijinki sirrinki ne Safiya, idan kika buɗe kamar kin tonawa kanki asiri ne, ko wa kika budewa littafin da wannan karatun zaiyi ta kallonki koda kuwa kin cigaba da zama ko kuma kin rabu dashi, mafitar matsaloli da yawa a hannunki suke, da wuya ake kaiwa gaɓar da wani ne zai iya magance miki damuwarki..." Zata lissafa Ammanta cikin manya-manyan jajirtattun mata a gidajensu, zata lissafa ta cikin irin mutanen da mata da yawa ya kamata su kalla suyi koyi dasu, don ita kanta babban makamin da take taƙama dashi na shirin tunakarar sabuwar rayuwar da zata yi, halayen Amman ne. Sai dai duk yadda ta kai ga dake zuciyarta, a wannan lokacin da Gwaggo Balkisa ke mata wannan addu'ar tana zuba ruwan ɗumi daga saman kanta, kuka take sosai, kuka mai nauyi, kuka mara sauti, kuka da zata iya cewa ya zarce na amare da yawa, don nata kalolin taraddain dake cikinsa basu da adadi, ba na barin gida ne kawai ba, bana shirin fuskantar wata sabuwar rayuwa bane, wataƙila idan tace na shirin mutuwa alhali tana numfashi ne, hakan zai iya fassara rabin abinda take ji. Tana sanye da wani farin saƙi dasu Gwaggon suka taho dashi, anyi mata ɗaurin ƙirji dashi kawai, yayin da gashinta mai laushi da yawa ke mannewa a fatar kanta da kuma wuyanta saboda ruwan dake bi ta cikinsa, tana zaune akan wani sabon turmi dasu Aunty Safiya suka siyo a cikin kayanta, yayin da sauran jama'ar bikin ke tsaitsaye zagaye da, gidan ya cika danƙam don har ƴan unguwa sun shishigo. Taga lokacin da Tanti ta shigo cikin masu zuba ruwan ta ɗebo nata itama tana kwara mata tare da nata addu'oin dake ƙara karya zuciyarta suna saka kukanta ƙaruwa. A lokacin ne kuma fuskar Ma'aruf ta haska Idanunta, ranar da ta fara ganinsa,

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73