Skip to content

Chapter 21

Chapter 21

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

masa sauki, don haka da guntun murmushi a fuskarta ta kai laziminta na sallamar sallah sannan tace. "Idan ranar na koma bautawa Muhammadu, iyayenku ai su zasu fara biyo ni kafin ku." Murmushi yayi a hankali sannan ya buɗe idanunsa ya juyo ya kalle ta dasu a lumshe. "Allah yasa da kika dama furar kin rage min, tun da na shigo nake jin ƙamshinta." Maimakon ta bashi amsa sai tace. "Yanzu Allah baza ka ji magana ta ka aske gashin nan ba ko? Ko iska ba ka so kaji tana ratsa ka Muhammadu?" Ba shiri murmushinsa ya karu. "Saboda me zan so iska ta ratsa ni? Wadda ke shiga hancina ma ta ishe ni Inna... Ki tashi ki ɗauko min furar dan Allah." Ai kuwa kamar ya ziga ta ne akan irin mitar da tayi a duk lokutan da baya nan a gidan, ta faro ta tunda daga farko daki-daki har tana faɗin idan ma ba zaiyi askin ba wai ya tsaya ta wanke masa da sabulun salo ta tabbata ranar sai yayi bacci mai daɗi, murmushinsa kawai yake yi yana jinta tunda dama ya riga ya shiryawa hakan. A haka har Ishaq ya shigo ya same su, shima aka zuba masa furar sannan ta tasa su a gaba su duka biyun kuma da zancen aure. A lokacin Ishaq ke gaya mata hukuncin da Baffa ya yanke game da Ma'aruf, don haka bayan ta gama hamdala da mitar cewa Baffan bai zo ya same ta ya gaya mata ba, sai faɗan kuma ya koma kan Ishaq shi kaɗai, tana yi tana zayyano masa jikokin ƴanuwanta na ƙauye, kowacce ta faɗo Ishaq sai ya gyada kai yace "Kuma da alamun tana da hankali." Ma'aruf na jinsu bai ce komai ba, tunani da yawa ke yawo a cikin kansa game da abubuwan dake gabansa, sai dai ko kaɗan babu batun auren nan a cikinsu, don tunaninsa ya gaya masa cewa ko iyayen yarinyar nan mahaukata ne idan ta nuna musu wannan takardar dole ne auren ba zai yiwu ba. A hankali ya sake rufe idanunsa yana tuno dukkan irin matakan dake rubuce a jikin takardun asibitinsa, Allah ya sani a baya baya taba damuwa da ciwonsa, yana ajiye shi ne a can ƙarshen lissafinsa, amma a yanzu... yanzu bai san me yake ji ba, tsoro ko kuma taraddadin cewa abubuwa zasu iya ƙwace masa kafin ya kai ga cimma manufarsa? A cikin duhun idanun nasa ya hango a inda yake manufar tasa, abinda shi kaɗai ne abu guda a duniyar nan da baya taɓa haɗawa da kowa, ɗakin bincikensa yake hangowa, tunda ya dawo bai buɗe shi ba don haka a yadda ya tafi ya barshi yake hango shi... Yadda yayi kaca-kaca da takardu cikin takaicin da shine linzamin dukan da yayi wa Daniel. "... Kaga Rabi ma ƴar wajen Baɗɗejo, yarinya ce mai hankali, ga kyau..." Muryar Inna ta shiga kansa da wani irin tasirin da ya doka a ƙirjinsa, tasirin da yasa ba shiri ya buɗe idanunsa yana kallon Innar da kuma Ishaq din dake cigaba da gyada kai yana shan furarsa, sai dai ba saurarar abinda suka cigaba da cewa yake ba, muryar Inna ta shekaru goma da suka wuce ce ta shiga haskawa a cikinsa, shekaru goma cikin wannan ɗakin. Kuma bayan muryar sai hoton ma ya canja a idanunsa, yaga yadda tsufan Inna ke raguwa da shekaru goma da yadda komai na ɗakin ke canjawa da abubuwan da suke a mazauninsu a shekaru goman da suka wuce, sannan a lokaci guda Ishaq ɗin ma ya bace, siffar Jamal ta maye gurbinsa yayin da yake zaune a gaban Innar yana dariya. "Ga Halima ma ƴar gidan Baffayo, yarinya ce mai hankali, ga kyau, ga kyau..." Ya ga yadda Jamal ke girgiza kansa yana dariya kafin yace. "Akwai abubuwa da yawa a gabana yanzu Inna, ki ajiye maganar yaran nan... Akwai abubuwan da nake son daidaitawa a gidan nan kafin ma in fuskanci aikina..." Kuma a lokaci guda ƙwaƙwalwar Ma'aruf ta tsinto kalamai biyu a cikin zancen... Abubuwan da nake son daidaitawa a cikin gidan nan... Abubuwan da nake son daidaitawa a gidan nan... Tabbas! Ya akayi bai taɓa tunawa da wannan lokacin ba? Me yasa ƙwaƙwalwarsa bata taɓa hasaso masa wannan ranar ba? Babu shiri idanunsa suka shiga hasko masa tarin abubuwan dake ɓullewa ga wannan maganar, yaji su suna sauka a cikin kansa kamar zubar ruwan da aka tunkuɗo da ƙarfi. "B, Yaushe zaka fita?" Muryar Ishaq ta janyo shi daga tunaninsa, sai kawai ya lalubo wayoyinsa a gefe da mukullin motarsa ya mike tsaye. "Yanzu." Ya bashi amsa idanunsa na muna tsantsar nazarin abubuwan da shi kaɗai yake hangowa. Kuma da haka bai jira komai ba yayi waje, yana ji Inna Danejo na ƙokarin tsaida dashi amma bai tsaya ɗin ba, ya fita yana jin tasirin idanun Ishaq da ya biyo da kallo. A harabar gidan ya gano Munaya tsaye tana waya, duk ta rikice kamar yadda take kullum sai faman gyara glasses ɗinta take alamun bayani ake mata ta cikin wayar, don haka bata ma ganshi ba har ya buɗe motarsa ya jata ya bar cikin gidan, kuma zai iya rantsewa zuciyarsa na lissafa kowanne wucewar lokaci kafin ya isa gida. A ƙofar gidan ya ajiye motar don ƙwaƙwalwar sa ta gaya masa cewa ba zai iya jira har maigadi ya buɗe masa gate ɗin ba. Ya shiga har ciki zuwa ɗakinsa, ya buɗe ƙofar da ko waye ya shigo ɗakin zai ce wardrobe ce. A ciki komai yana nan kamar yadda yake hango shi kafin tafiyarsa. Tebura ne da duruwoyi masu cike da files ɗin takardu da kuma hotuna, ga tarin printers da photocopier a gefe, sannan bayan kayan rubutu akwai allo har kala uku ɗaya na rubutu biyun kuma ya manne su da takardu da kuma hotuna. Ɗaki ne da ko makaho ya shafa zai danganta shi da kalmar binceke balle kuma ga mai ganin da kallo ɗaya da zai yi masa zai bashi amsar da ba sai ya tambaya ba. A jikin allon nan bayanai ne da kuma hotunan mutanen da Jamal yayi mu'amala dasu tun daga lokacin da ya dawo daga karatu har zuwa ranar mutuwarsa, kuma a jikin kowacce takarda da hoto Ma'aruf ya zana tambarin × da jar marker alamun abinda yake nema bai ɓulle ga wannan hanyar ba, kusan hakan ne ma a jikin kowacce takarda dake barbaje a ɗakin har kuwa da waɗanda aka yayyaga. A wata durowa daga can ƙarshen ɗakin ya shiga fito da duk takardun cikinta har hannunsa ya kai kan wani file daga can ƙasa. A cikin file ɗin tarin takardun Jamal ne wanda suka haɗa da duk certificate dinsa na gama makaranta da kuma takardun ɗaukarsa aiki a matsayin sabon ma'aikaci a kamfanin Baffa, takardun ɗaukar aikin ya shiga buɗawa ɗaya bayan ɗaya idanunsa na nazarin komai sai dai har yaje ƙarshensu bai ga komai ɗin da yake nema ba, ya zauna daga tsugunnen da yake, ya sake bin komai dalla-dalla, amma har a lokacin babu komai ɗin. Hannayensa duka biyu ya cusa cikin gashinsa yana fitar da iska ta hancinsa... Tunani da yawa ke tsere a cikin kansa, yana ji yadda yanayinsa ke ƙoƙarin canjawa, ciwo na harbawa a cikin kansa

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73