Chapter 1
Chapter 1
SHIMFIDA. A lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai...! Me zai faru a lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai? A lokacin da ka shiga shiga cikin wata duniya da zaka ji baka son barinta? ka bi ahalin cikinta kuna nutsewa cikin ramin da baku san dashi ba? ka shagala da kallon FARAR WUTAR da ta juye tunaninsu, ta wanke kwakwalwar su har kowa a duniyarsu ya manta cewar wuta, WUTA ce! Duk kuwa irin FARINTA. #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. BABI NA ƊAYA. ~~~~~ Wajen karfe goma sha biyu na rana, matar dake cikin kitchen ɗin da aka zagaye da langa-langa daga ɗan madaidaicin tsakar gidan ta kwance wani ɗaurin itace dake gefe ta ƙara a cikin murhun gabanta sannan ta shiga firfita wutar da wani karyayyen mafici dake gefe. Dattijuwa ce mai kyawun jikin da idan ba fuskarta ka kalla ba zaka zabge shekarunta ƙiyasi. Kayan jikinta riga da zani ne masu kyau da har karin guga zaka hango a jiki, gashin kanta mai laushi ya sirka da kananun furfura da ta fara yiwa kan nata rumfa. Sai da ta tabbatar wutar ta kama sannan ta mike ta fito, a tsakar gidan ta tarad da babbar ƴarta mai suna Amina zaune tana tsintar wake a wani katon farantin silver, shekaru ne kawai suka banbanta kamannin fuskokinsu amma kammaninsu daya sak! Har yanayin jikinsu da komai. Ƴar siririya ce mai yalwar gashi irin na mahaifiyar tata, komai a fuskarta maidaidaci ne mai sanyin kwatance, idanunta ne kadai abinda mai ɗaukar hankali don duk da ba girma ne dasu ba, amma suna da wani kyalli kamar an ɗiga wani abu a cikinsu. "Yi sauri ki gama Amina, sha biyu tayi gwara muyi sauri a ɗora don yanzu zaki ji su sun dawo." Amina ta buɗa labule ɗakin dake bayanta, ta kalli agogon dake kafe a cikin dakin sannan tace. "Ashe lokaci ya tafi har haka, ban kula ba sam wallahi." "Garin ne ba zafi ai shi yasa kika kwanta kika yi ta baccinki." Da murmushi tace. "Ni ai na gaji da tashi da wurin ne wallahi, da sun tafi makaranta sai inga gwara kawai na kwanta." Mahaifiyar tasu da suke kira da Amma ta dauki wata tukunya dake gefe, ta nufi wajen ruwa da ita tana fadin. "Ki cigaba da addu'a kawai, idan da rabon ki a cigaba da karatun nan zaki yi insha Allah." Amina bata ce komai ba, don Allah ya sani ta fara karaya, shekararta guda kenan da kammala karatun sakandire dinta, kuma sakamokonta yayi kyau duk da cewar an taimaka musu wajen yin jarabawar, amma duk da haka ta san tana da kokarinta daidai gwargwado, shi yasa ko kadan ƙulafucin son cigaba da karatun bai bar ranta ba. Kuma ba dole sai wani babban karatu ba, don ta daɗe da soke Jami'a a lissafinta, ta sani cewa mahaifinta bashi da halin wannan wajen, yana iya bakin kokarin sa wajen kula dasu da ɗan abinda yake dashi kuma duk da haka kullum cikin damuwa yake yana ganin kamar baya basu abinda ya kamata, don yasha fadin cewa yayi burin cewar ƴaƴan sa zasu huta da duk wani gata na duniya. Don haka tunanin ta a kullum na ta samu makaranta ne ƙarama inda zata dan koyi aikin lafiya... Don mahaifiyarta tasha faɗa mata cewa ko allura ta iya yiwa mutane, idan tayi aure hakan zai taimake ta sosai fiye da ace ta zauna bata yin komai. Zancen auren ya tuno mata da saurayin ta Abdallah, ta san shirye-shiryen komawa makaranta yake yi shi yasa bata ji shi ba kwana biyu, a matakinsa na ƙarshe yake a can wata jami'ar Sakkwato. Abdallah mutum ne mai kirki da kuma hankali, har islamiyyar dare yake da ita a bayan layinsu wanda yasa kowa ke ganin mutuncinsa kamar yadda itama take girmama shi a kodayaushe, tana ganinsa kamar yayanta shima kuma yana taimakon ta a komai kamar ƙanwarsa. Mu'amalarsu daban take da yadda take ganin tsakanin ƙawarta Fatima da nata saurayin, abubuwa da yawa idan Fatiman ta gaya mata ta kanyi mamakin yadda suke iya kasancewa, don ita ko ɗaga ido ta kalli Abdallah bata iyawa sosai, sau da yawa ma ta kan manta cewa mu'amalarsu aure zata kai. "Salamu alaikum, wai a bada gullisuwa." Sallamar wani yaro ta katse tunaninta sanda ya tsaya daga jikin hanyar soro yana miko naira hamsin. "Ta nawa?" Ta tambaya. "Ta naira Ashirin." Sai ta ajiye farantin waken ta miƙe ta karbi kudin, watanni hudu kenan da fara sana'arta ta saida alawar madara, gullisuwa da kuma albishir, kuma ciniki take yi sosai don a kwana uku kawai take sake yin kowannensu na dubu biyu. Wannan shine babban abinda ke ɗebe mata kewa da kuma faranta ranta ganin yadda take iya yin wasu bukatunta da kanta har ma ta taimakawa ƙannenta da ɗan kuɗin kashewa, saɓanin a watannin baya da bata komai. Lokaci shine rayuwarka ta duniya da kuma lahira, babu amfani ka barshi yana tafiya haka sakaka... Kalaman Ammansu kenan a kullum idan tana bayanin abubuwan da suka dace da rayuwar mutum. Ta ɗebowa yaron gullisuwar hade da canjinsa, ta fito daga falon nasu da babu komai sai shimfidadden carpet daidai lokacin da Fatima tayi sallama ta shigo. "Amma ina wuni." Ta gaishe da Ammar dake wanke bayan tukunyar data dauka. "Lafiya kalau Fatima, Hajiyan ta fita ko tana nan?" Hajiya mahaifiyar Fatiman ce, kuma tana zuwa jinyar kakar Fatiman ne da aka kwantar a asibiti kullum. "A'a bata fita ba, girki take yi tukunna." "To bari in gani nima idan na gama nawa ko zan iya bin ta, tun jiya nake waƙar ya kamata in koma wallahi." "Ai jikin nata ma da sauki." Cewar Fatiman tana nufar hanyar ɗakin su Amina rike da ledar hannunta, ganin hakan yasa Amina ta dauko farantin waken da ta gama gyarawa, ta nufi wajen rijiya ta zago ruwa ta wanke shi sannan taje ta zuba a tukunyar dake gab da tafasa. "Kaya Ahmad ya kawo min jiya da yazo." Tana bude labulen ɗakin Fatiman ta fada, da fara'arta kuwa ta goge ruwan hannunta a jikin doguwar rigar da ta saka sannan ta ƙarasa gefen katifarta inda Fatiman ke fito da kayan, atamfa ce har guda biyu da kuma farin mayafi ɗaya sai kayan kwalliya. "Gaskiya ne Fati, wallahi ki gode Allah, Ahmad na ji dake." Fatima ta juya idanunta alamun dadi tana murmushi. Fara ce ita sosai, farin da take alfahari dashi a kodayaushe, tana ganinshine silar samuwar abubuwa da yawa a rayuwarta, don iyayenta masu ƙaramin ƙarfi ne sosai. "Ni kaina wallahi na sani Amina, shi yasa nake gode masa kullum." "Allah kuwa yana da kyauta, Allah ya saka masa da alkhairi... Kai wannan tafi kyau wallahi." Ta fada tana daga wata. "Kamar kin san nima nafi ganin kyanta, har cewa nayi ko in barta sai Sallah kawai muyi ankonta ni dake." Amina ta bude kwalin wata hoda sannan tace. "Sallah fa da nisa, ki ɗinka abarki kawai. Ma yi wani ankon idan lokacin yazo." "To shikenan." Fatima ta gyara zama tana kallon yadda take kallon kayan, sai kawai tace. "Wai yaushe rabon Abdallah da ya miki kyauta ne Amina?" Amina bata bar kallon kayan kwalliyan ba tace. "Shi da yake dan makaranta ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73