Skip to content

Chapter 57

Chapter 57

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

ko in takurawa rayuwarki ba insha Allah." Ya furta hakan yayin da hannunsa ya kai kan zip ɗin, sauran yatsunsa na ɗaya hannun suna taba fatar bayanta, sai kawai ta rufe idanun gabadaya tana ƙoƙarin saita numfashinta, kuma da ja ɗaya kawai hannunsa yayi ya sauke zip ɗin sai dai bai kai shi har ƙasa ba, daga daidai tsakiya ya barshi, taji sanda yatsunsa suka dauke daga saman fatar ta, da kuma sanda yake matsawa, sai ta buɗe idonta lokacin da ya zagayo daidai saitin ta. "Nagode." Ba zata ba taɓa iya tantance yanayin yadda muryar tata ta fito ba, ya gyaɗa kansa. "You are welcome, sai da safe." Da haka ya juya ya nufi kofar ɗakin yana rufo mata ita. Sakan ɗaya, biyu, uku, suka wuce Amina tana ƙoƙarin saita numfashinta kafin a hankali ta ɗauko rigar baccin nan ta karasa abinda zata yi, wanda har ta gama komai ta kashe fitilar ɗakin kalamansa na yawo a cikin kanta. ...ba zan taba cutar dake ko in takurawa rayuwarki ba insha Allah. Sai kawai ta rufe idanunta sannan ta dunkule jikinta akan gadon, kuma bata bawa zuciyarta wani damar tunani ba don bata san buhu nawa zata kwance na tambayoyin da bata da amsar su a zahiri dama cikin kanta ba. Ya rabbi lakaal hamdu kam yanbaghi li jalaali wajhika wa adheemu sulɗaanik. Bakinta ya furta addu'ar hankali yayin da take jin ma'anar ta na tafiya har ƙasan zuciyarta. *** Washegari... Ƙarfe goma na safiyar Litinin, a irin wannan lokacin Amina ta saba da wani irin shiru don ko'ina tsit yake, duk wani mai fitar safe ya daɗe da yin gaba, ƴan makaranta da masu aiki da mafi yawanci sun fi yawa a kowanne gida. Tana daga kitchen a lokacin tana ƙoƙarin fara aikinta ta tsinkayi ƙarar ƙwanƙwasa kofar, mamaki ya ɗan kamata don ta san babu wanda zata yi tunanin zuwansa a wannan lokacin, ta gyara zaman ɗankwalinta yadda ta yafa shi sannan ta fito daga kitchen ɗin ta iso ƙofar falon kuma ba tare da tunanin komai ba ta buɗe ta,a lokaci guda siffar Hajiya Kilishi dake tsaye ta shiga idonta tun kafin sakon saninta ya ƙarasa ƙwaƙwalwar ta. Tana sanye da wata haɗaddiyar lafaya ruwan makuba (maroon) da ta nannaɗe ta tsaf a jikinta, fuskarta kamar kullum ɗauke da wannan murmushin nata, murmushin dake haska annurin fuskarta a kodayaushe yana ƙawata kammaninta. Babu dalili Amina taji gabanta ya faɗi amma tayi saurin kore hakan wajen yin nata murmushin itama. "Sannu da zuwa Mami, barka da zuwa." "Barkanmu dai Amarya. Yau dai na ajiye kyuiyata a gefe nazo ganin ɗakin amarya." Wani murmushin mai haɗe da kunya Amina ta sake yi kafin tayi baya don bata hanya tana kara fadin 'Barka da zuwa', kuma kai tsaye kuwa ta shigo haɗe da sallama yayin da ƙamshin daddaɗan turarenta ke rufo mata baya. "Wa'alaikum salam." Ta amsa sallamar tana rufe ƙofar har a lokacin da murmushi a fuskarta, murmushin da a lokaci guda ya ɗauke sakamakon juyowar da Hajiya Kilishi tayi tun kafin ta kai tsakiyar falon tace. "Idan akwai muƙulli rufe ƙofar dashi Amina, akwai maganar da zamu yi ne." Zuciyarta ce ta fara bugawa a kirjinta kafin ta juyo ta kalle ta, amma ganin murmushin dake kan fuskarta har yanzu, yasa itama ta dawo da wani dan guntu kan leɓɓenta sannan tace. "Toh Mami." Da haka ta rufe kofar tana ƙoƙarin gayawa zuciyarta cewa gabanta ba faɗuwa yake ba sannan ta juyo ta ƙaraso ciki. A lokacin ta zauna daga tsakiyar kujera mai cin mutum uku a falon don haka ita tameni waje daga ɗaya karshen ƙaton carpet ɗin ta zauna tana fuskantar ta. "Barka da Asuba Mami, fatan kun tashi lafiya?" Ba kallonta take ba amma daga yanayin yadda muryarta ta fito wajen amsawa ta fahimci har yanzu murmushin take yi. "Mun tashi lafiya, Ya bakunta kuma? Ko da yake ai naga su Samirah sun saka kin saba tuni." Bata ce komai ba illa wasa da karshen skirt dinta da take yi tana cigaba da murmushin da zata kira na dole, don bata san me yasa zuciyarta ta kasa zama waje ɗaya ba. Hajiya Kilishi ta kalli ƙaton screen din Tvn dake tsakiyar falon dama sauran kayan kallon da aka jera akan hadadden stand ɗin Tvn da dubu tamanin da biyar ta bayar aka siyo shi sannan tace. "Gidan shiru ke kaɗai baki ko kunna Tv ba?" Da wani murmushin a fuskarta tace. "Ai ba'a hada Tvn ba har yanzu Mami." Muryarta ta fito ƴar ƙarama a cikin shirun dakin, kamar tana son ta shaidawa Hajiya Kilishin ƙanƙanta da kuma rauninta. "Baku gaya min ba ai, gashi jiya kuwa yaro mai gyaran satelite ya shigo har cikin gida, da ya karaso ya hada muku, amma a bar ki a gida haka shiru, shi ya fice ya tafi hadaniyar gabansa ba zai tuna da wani sha'anin Tv ba. Sai ta sake girgiza kanta tana cigaba da murmushin. "Ba komai Mami, duk sanda aka sa baza'a makara ba ai." Ta fadin hakan lokacin da take kokarin mikewa, amma a lokaci guda Hajiya Kilishin ta tsayar da ita. "Ina ziki je kuma?" "Mami, kayan breakfast zan kawo miki." Ta faɗa taka kallonta, sai ta girgiza kanta. "Barsu nagode, dawo ki zauna." Umarnin dake cikin muryar ya kaɗa hantar ta, taji wani abu yana ƙoƙarin ɓallewa daga cikin zuciyarta, amma sai tayi saurin ture hakan ta dawo ta zauna ɗin, hannunta na taɓa hannun kujerar gefenta kamar tana neman taimakon ta. Kuma zaman nata sai ya zama kamar shine farawar wani shafi na farko a rayuwata, don watakila idan zata bada labari, zata fara ne ta kansa, daga lokacin da kafafunta suka sake komawa kan carpet ɗin nan da kuma lokacin da muryar Hajiya Kilishi ta sake ratsa shirun ɗakin da cewar. "Amina kunyi waya da mutanen gida kuwa jiya?" Sai da ta haɗiye wani dunƙulen abu da bata san sunansa ba a kirjinta sannan ta girgiza kai. "A'a Mami, na kira su dai jiyan amma bai shiga ba." "Ina wayarki?" Kai tsaye ta sake wata tambayar da ta fito kamar tsawa. Kan Tv's stand ɗin nan ta nuna inda bayan fitowarta da safen ta saka ta a caji. "To matso ki kira su." Wannan karon sai da ta kalle ta tsawon wasu sakanni fuskarta na haskawa da mamaki sannan ta matso a hankali zuwa wajen wayar, lokacin da ta cire ta daga caji taji kamar hannunta na rawa amma tayi saurin fara dannawa ta lalubo nambar Amma. Sai da ta sake kallon Hajiya Kilishin da murmushin fuskarta ya rage tasiri kafin ta kara wayar a kunnenta, kuma cikin wata iriyar sa'a, bugu ɗaya biyu sai Amman ta dauka, sautin muryarta kadai ya doka wani abu a ƙirjinta tun kafin ta fahimci abinda take faɗa. "Amina yi haƙuri, tun jiya bamu kira ki ba, muna asibiti ne sai da safen nan muka fara samun nutsuwa..." "Asibiti? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!... Me ya faru Amma? Me ya faru?" A yanzu ta tabbatar hannun nata rawa yake, don tana jin yadda yake tafiya tare da bugun zuciyarta. Daga cikin wayar Amma tayi ƙokarin gyara muryarta kaɗan sannan tace. "Aminu ne mai mashin ya taka shi jiya da daddare a wajen aiki, amma sun

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73