Skip to content

Chapter 72

Chapter 72

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

iya haska cikin zuciyarki har tayi wani hasashe ba, waɗannan sune matakan farko Amina, kuma ina tabbatar miki idan kika tsallake su, dukkan sauran zasu zo ne bi da bi kuma a sauƙake..." Zuciyarta ta gaya mata cewa wannan lokacin shine zaiyi daidai da zuwanta wajen Hajiya Kilishin, don a yanzu ne zata yarda cewa da gaske zuciyarta ta wanku wajen yarda da ita. Shi yasa ta tattaro dukkan dauriyarta ta taho cikin gidan inda Sameerah ta shaida mata cewa Mamin tana wanka. "Kin gama? Mamin tace tana jiranki a ciki." Muryar Sameerah ta dawo da ita zahiri, ta ɗago tana kallonta daga can jikin hanyar koridon dakin Mamin, ta san lokacin da Surayya ta tashi ta shiga ciki amma ita bata san lokacin da ita ta tashi ba, taji zuciyarta ta buga a cikin ƙirjinta amma kuma sai fuskar Amma ta gifta a idanunta ta kore hakan, ta gyara yafen mayafinta sannan ta mike a hankali tana zagaye table din da Sameerah ta cika da kayan breakfast din, kafafunta suka taja cikin korido din lokacin da Sameerah ke gaya mata cewa ta tafi ta shiga wanka, kanta kawai ta gyada mata kafin ta rike handle din kofar dakin. Da dukkan addu'o'in da zata iya karantowa a zuciyarta ta tura kofar dakin, kuma kamshin turaren wutar da taji tunda ta shigo dakin shi ya fara shiga hancinta, ta hango shi kuwa yana ci daga can kan bedside drawer dakin daga cikin wata haɗaddiyar burner irin wadda Sameerah ta taba kai mata. Sai taji ta shaki wata busashshiyar iska a makogwaronta lokacin da ta hango Mamin, tayi wankan kamar yadda aka fada ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa da aka baza mata stones tana ta kyalli, kamar ƙyallin dake son nunawa duniya cewa ita kadai ce Kilishi irinta. Ƙafafunta suka karaso ciki da sallama, sallamar da Mamin ta amsa da murmushi a fuskarta, murmushin nan nata mai nauyin da sai a yanzu Amina ke jinsa a saman kafadunta. "Ashe ƴan jigawan har sun dawo, yaya kuka tarar dashi Amina?" Takaicin da ya taho ya taru a kirjinta wani abu ne da ba zata iya misalta shi ba, amma haka ta daurewa masa ta amsa. "Jikinsa da sauki Mami." Kuma sai da ta jira ta nemi bakin gadonta ta zauna sannan kai tsaye muryarta ta sake fitowa. "Mami na yarda da dukkan zancenki, na yarda zanyi dukkan abinda zaki sani ba tare da wani ya san komai ba, dan Allah kar ki sa a sake taɓa kowa a cikin ƴanuwana, raunin dake jikin Aminu yayi yawa, dukkan kafafunsa biyu sun karye... Zanyi dukkan abinda kika ce da yanzu Mami don ni kaina ina son rayuwata ta inganta, na miƙo miki hannayena kamar yadda kika umarta don ba zan taɓa yin katoɓarar yin ganganci da rayuwar iyayena da ƴanuwana ba, darajarsu tafi komai a wajena." Muryarta tayi shiru na wani lokaci sannan ta sake ratsa shirun ɗakin amonta na rawa. "Na rantse da ubangijin daya halicce ni Mami, zan yi miki biyayya kamar yadda kika umarta, baza ki taɓa dana sanin bayyana miki sirrina ba insha Allah." A cikin ɗakin wani irin shiru ya sake giftawa, irin shirun nan mai tsantsar zurfi, zurfin da a cikinsa zukata ke saƙa abubuwa da yawa, kamar yadda zuciyar Kilishi ke saka mata dubunnan abubuwa a wannan lokacin yayin kallon Amina take da dukkan irin nazarin da ƙwaƙwalwarta ke iyawa, tana jin yadda a bayan kanta wasu kofofi ke buɗewa kuma tunaninta na nutsewa cikinsu na son gano wani abu daban saɓanin abinda bakinta ke furtawa. Sai dai duk iya kokarinta, ta kasa gano abinda yake saman fuskar Aminan, a wannan lokacin, don tsoro da kuma rudanin da take gani karara suna fitowa tare da kalamanta, kuma takaicin yadda ubangiji ya biye sirrin kowacce zuciya ya kamata, don baza ta taɓa yarda kai tsaye cewa yarinyar nan ta karbi tayin ta kai tsaye haka ba, amma da yake ita Kilishi ce, sai tayi gyaran murya a hankali sannan ta faɗaɗa murmushin dake kan fuskarta, a kusa zata gane komai ba sai anje da nisa ba ta yiwa kanta wannan alƙawarin. "Shi yasa na barku kuyi tafiyar nan dama Amina, don so nake kije ki ga ɗanuwanki ki san cewa babu wasa a al'amarina kamar yadda na jaddada miki komai, kuma Alhamdlilah naji dadi sosai da idonki ya buɗe kika fahimci gaskiya tun a yanzu, tun kafin mu shigo da wasu cikin lissafin." Muryarta ta fito ne da wani irin sanyi kamar ƙanƙarar dake narkewa a cikin ruwa, Kuma da faɗin hakan bata jira komai ba sai ta taso, ta wuce ta ta nufi wardrobe ɗin dake dakin. Wajen da ta bude na farko ya nuna mata ajiyar da tayi na wata bakar jaka, ta dauko ta sannan ta sake buɗe wani wajen inda jakunkunan ta suke a jere, kuma a cikin aljihun guda ɗaya ta ɗauko Sachet mai yawa na wani magani sannan ta rufe komai ta juyo, da takunta a hankali ta sake dawowa wajen da Aminan ke zaune akan carpet, inda daga gabanta akwai wani stool da aka bari a wajen, ta ajiye wannan jakar da kuma magungunan a gaban Amina sannan ta nemi kan stool din ta zauna kafin muryarta ta sake ratsa dakin. "Komai mai sauƙi ne Amina, umarni na kawai zaki dinga bi shikenan sai duniyarki ta koma kamar aljanna, don zan cika miki dukkan wadannan alkawuran dana dsukar miki har ma da karin wasu da bamu lissafa ba, Kin fahimce ni ko?" Kuma kamar yadda ta zata, sai ta ɗago ta kalle ta idanunta na shaida sauran tsoron da a lokacin dama ya kamata ace yana barin fuskar tata, ta gyaɗa kanta sau biyu sannan ta sake maida shi kasa, kuma abinda Hajiya Kilishi ta gani a idanun nata ya shiga barazanar goge kokwanton da take yi akanta, amna tayi wulli dashi a lokaci guda. "Yayi kyau, yanzu ki saurareni sosai kiji abinda nake so dake." Amina ta sake gyaɗa kanta tana ƙara gyara zamanta lokacin da Muryar Hajiya Kilishin ta cigaba da shiga kunnenta. "Akwai abinda zanyi a kamfanin su Ma'aruf cikin satin nan, kuma zan yi shi ne ba tare da yana nan ba, don haka yanzu za ki taya ni abinda ya kamata ace ni zanyi don dama lokaci yayi da hakan zai koma hannunki. Abinda ke cikin jakar nan magunguna ne, na san an gaya miki cewa Ma'aruf yana da wata rashin lafiya ta ƙwaƙwalwa, sunanta 'Bipolar Disorder' ya same ta ne a shekarun baya lokacin da rayuwarsa ta canja bayan rasuwar ɗanuwansa, cuta ce dake canja tunaninsa a duk lokacin da ta tashi, abubuwa suna cakuɗewa a cikin kansa har baya sanin abinda yake yi. A London ake yi masa magani tun daga wancan lokacin kuma suna ɗora shi akan ingantattun magunguna tun daga sannan, amma da farko Ma'aruf bai karbi ciwonsa hannu biyu ba balle har ya dinga kula da kansa, baya taba shan magungunan sa akan kari wanda hakan ke ƙara bawa ciwonsa bigiren yaɗuwa, tun kafin yayi aure nake yi miki wannan zancen Amina kuma tun a sannan na karɓi magungunansa na ajiye a wajena. Ma'aruf kamar ɗan dana haifa na dauke shi, kin sani tun a wancan labarin dana baki, don

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73