Chapter 61
Chapter 61
huta ba wannan hargitsatsen gidan nasu shi da Ishaq ba. Kamar ya zauna yaci abincin sai kuma kawai yaji ba zai iya hakan ba alhallin bai ganta ba. Sai kawai ya zaro wayarsa ya kira lambar Samirah, bugu ɗaya biyu kuwa ta dauko, muryarta a ciki ta fara cewa 'To Mami.' kafin tayi sallama. "Yaya barka da dare." "Kun yini lafiya?" "Lafiya ƙalau." Ta amsa sannan tayi shiru tana jiran abinda zai faɗa a gaba, kuma hakan kaɗai ya bashi amsar da yake nema cewa Aminan bata ciki don haka kai tsaye yace. "Sai da safe." Ya kashe wayar ya zura ta a aljihunsa sannan ya koma cikin gidan, ɗakinta da bai shiga ba a yanzu shi ya nufa kuma bai jira komai ba ya buɗe shi, fitilar a kashe take kamar yadda ya gani sai dai babu duhu a ciki don hasken fitilar waje na shigowa ta windon ciki, kuma a lokaci guda idonsa ya hango masa ita, tana zaune daga gefen gadon ɗakin ta ɗora kanta akan gadon yayin da jikinta yake a dunƙule, kamar dai ranar daya fara ganinta, ranar da ya fara ganinta a matsayin matarsa. Wannan shine karonsa na biyu shigowa ɗakin kuma ya sake tarad da ita a irin wannan yanayin da ya san cewa tabbas akwai abinda ya faru. Hannyensa duka biyun suna cikin aljihu, sai ya fito da ɗaya daga aljihunsa ya sosa kan hancinsa yana kallon idanunta da suke a rufe. "Assalamu alaikum." Muryarsa ta ratsa ɗakin cikin amonta. Kamar wancan karon ta dago kanta da sauri ta kalle shi amma bata mike ba, kallonsa take yi cikin hasken ɗakin wucewar sakanni biyu kafin bakinta ya amsa sallamar tana ƙoƙarin dagowa daga kishingiden da take. Sai kawai ya juya ya koma ya kunna fitilar dakin, haske ya gauraye koina, yana nuna masa kumburarrun idanunta da tabbas kuka tasha dasu. "Me ya faru? Me ya same ki?" Tambayar ta fito sak kamar ranar da ya ganta cikin daren nan, amma wannan karon sai yaji abinda yake son tambayar yafi hakan, zai iya jero kusan guda goma don ya samu gamsashshiyar amsa. "Babu komai." Ta fada tana ƙoƙarin juya kanta gefe don naɗe sallayar da take kai, yana iya ganin dogon hancinta wanda da alama ta murza shi fiye da kima. "Kayi hakuri, ban ji lokacin da ka shigo ba, barka da dawowa..." Muryarta ta faɗa sanda ta gama ninke sallayar ta miƙe tsaye tazo zata wuce shi, amma sai kawai ya riko hannunta na hagu ta baya ya tsayar da ƙafafunta. Ba shiri Amina ta cije lebbenta tana kallon tiles ɗin dake ƙasan dakin, gayawa zuciyarta take yi cewa ta daurewa wani kukan dake shirin tasowa a ƙirjinta amma sakon baya tafiya sam, don lokacin da ya jawo ta baya ta dawo gabansa ƙwalla ta sake cika idanunta taf. A yau ɗaya rayuwarta ta canja, ta shiga tashin hankalin da bata san da me zata kwatanta shi ba, a cire mamakin halayen Hajiya Kilishi daya nade zuciyarta a gefe, tsoro da taraddadin hatsarin da ta kawo kanta cikinsa ya hargitsa kowanne abu mai kyau na tunaninta, tana tuna kalamanta, tana tuna ranar da ta yanke hukuncin karɓar auren nan, da wani zai gaya mata da wani abu ko da makamancin haka ne... da tabbas labarin zai canja daga yadda yake yanzu. Ita bata san ma me take ji ba, bata san yadda zata fassara halin da take ciki ba, kawai dai ta sa zuciyarta ta karye da kowanne abinda kalaman Hajiya Kilishin ke nufi, kuma shi kansa Ma'aruf ɗin ma a yanzu bata yarda dashi ba, don bata san me Hajiya Kilishi ke nufi da 'matakan da take ɗora shi akai don tsarinta ya tafi daidai ba.' Zuciyarta tayi rauni da yawa ta yadda fuskar Aminu ce kawai ke yawo a kanta da tunanin halin da yake ciki, shi yasa a karo na farko tun bayan ranar da aka kawota gidan, hawaye ya kasa tsayawa a idanunta, don a wannan lokacin tana jin cewa kukan shine kawai sauƙin abinda take ji a kirjinta. "Ki gaya min abinda ya faru da kuma dalili da yasa kike kuka." Ma'aruf dake riƙe da hannunta ya fada da muryarsa cike da ikon dake nuna mata cewa da gaske yake yi, sai tayi ƙokarin maida kukanta ta hanyar share idanunta da ɗaya bayan hannunta sannan ta shiga gyara tsayuwarta don ji take kamar zata fadi. "Me ya same ki Amina?" Bai gaji ba ya sake tambaya a lokacin da take jin kamar ƙamshin turarenta na kassara kasusuwanta ne, bata da wani zaɓi da ya wuce ta lalubo wani sauti daga can ƙasa maƙoshinta idanunta har yanzu suna ƙasa tace. "Aminu ne ya gamu da hatsari, yana asibiti tun jiya." "Ya salam, Ya salam, wane asibiti ne?" Bai san waye Aminun ba, amma ya fahimci ɗanuwanta ne. Ta girgiza kanta wani kukan na shirin ƙwace mata. "Ban sani ba, muna waya da Amma sai... Sai wayar ta ɗauke." Zancen ya fito daga can ƙasan maƙoshinta ba tare da ta tsara shi ba. Sai kawai yasa ɗaya hannunsa da baya rike da ita ya zaro wayarsa daga aljihu, santsinta ya biyo hannyensa yayin da ya kunna password ɗin da yatsansa sannan ya shiga wajen dial log kafin ya miƙo mata. "Ki kira ta sai muji wane asibiti ne?" Sai a yanzu ta ɗago ta kalle shi kuma kafin tayi saurin sake maida idanunta ƙasa, ya gani cewa har yanzu kwalla ce taf a cikinsu, a hankali nata hannun suka karbi wayar don babban abinda take bukata a lokacin kenan, kuma ga mamakinsa bata matsa ba ta shiga danna nambar wayar Amman. "Assalamu alaikum." Sautin muryar mahaifiyarta da ya fito ta ciki yasa a yanzu ƙwallar idanunta ta gangaro... Karo na farko a duniya taji so take ta ganta a gabanta wannan lokacin ta rungume ta, so take ta cusa kanta a jikinta ta rera kukan da har yanzu take jin nauyi ta a ƙirjinsa, ta gaya mata cewa tayi nadamar ƙin gasgata maganganunta, don abinda ya shigo cikin rayuwar tasu yanzu wani abu ne da duk ƙarfin hangensu basu gano ko rabinsa ba, wani tashin hankali ne da ya tsallake dukkan tunaninsu. A yau ta ƙara yarda da zancen Amma na cewar babu wani auren gaske tsakanin mai kuɗi da talaka a wannan zamanin, indai ya faru to tabbas akwai wani boyayyen abu dake ƙasa, Amma tace rayuwarki zaki sadaukar musu Amina, ashe su duka basu sani ba cewar bayan tata rayuwar suma tasu ta shigo ciki wataƙila har da sunan duk wani da ya rabe su ma. "Amma, Amina ce." Muryarta ta fito tana kakkarwa kamar yadda hannunta keyi acikin nasa. "Amina... Amina." yadda muryar Amman ta kira ta a jere da wani irin sautin ajiyar zuciya yasa lebbenta talewa cikin kokarin wani kukan. "Me ya faru ɗazu wayar ta dauke? Mun gwada yafi sau hamsin kuma bata shiga ba. Har Hajiya Kilishi na kira ita kuma ba'a dauka ba?" Sai da ta hadiye wani abu a ƙirjinta jin sunan Hajiya Kilishin sannan ta iya cewa. "Amma wayar mutuwa tayi kawai, kuna ina yanzu? Ya jikin Aminun?" "Gamu nan mun dawo gida don Baba yace bai yarda yayi zaman asibitin ba, yanzu dai sunyi masa abinda zasu yi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73