Chapter 35
Chapter 35
hannaye ta yana ƙara haska farin. Hatta Amma tayi kyau cikin shigar wani lace da ya dace da maman Amarya, itama tana ta dariyar da har ta mantar da ita haushin da zuciyarta ke ciki game da kayan jere da suka kai aka ƙi karba. Ranar da su Tanti suka tafi za'a fara jeren nan, ranar zuciyarta ta sake yin baƙi game da al'amarin auren, don a waya Hajiya Kilishi ta kira tana gaya mata cewar ai su basu ce su kawo kaya ba, wai mahaifin yaron daya bada kudi ayi gyaran gida ya bayar har dana komai don haka su sun riga sun gama jeran su amarya kawai suke jira. Sai da ƙyar bayan Tanti ta dage cewar baza su kawo ƴarsu haka ba sai da abinda zata kalla itama ta san cewar iyayenta ne suka yi mata kamar kowacce ƴa, sannan Hajiya Kilishin tasa aka fitar da kayan gado guda daga wani ɗaki suka jera nasu, kayan Kitchen kuwa suka zube mata gabaɗaya don shi dama abubuwan da aka ajiye basu da yawa, sai a sannan ne zuciyar Amman ta ɗanyi sanyi, amma har a wayewar garin yau bata dawo dai-dai ba sai a yanzu da Aminu ya saka ta yin dariyar dole. Kuma duk yadda bikin ya kai ga zuwa a gaɓar da kowa ke ganin ba'a shirya ba, yayi mutuƙar yin daɗin da wataƙila ko da sun shekara ne suna tanadi haka komai zai kasance, banbancin kawai na farin cikin da za'a samu a zuciyoyinsu ne. Wajen yamma, Adam ya kawowa Amina saƙon wata sallaya mai kyau da kuma alƙur'ani daga Abdallah, a hannayenta Amina ta rungume ledar ba tare da tace komai ba, idanunsa kawai take hangowa a ranar da ta gaya masa aure zata yi, yana kallonta da yanayin da bata iya fassara shi ba. "Dama na gaya miki, ba wani son ki yake yi har cikin zuciyarsa ba." Haka Fatima tace lokacin da ta gaya mata yadda suka yi, amma sai ta girgiza kanta ta bata amsa. "Cewa yayi dama ya sani ba lallai ya iya aurena bane Fati, yace ya san ba lallai ni ko iyayena mu iya jurewa tazarar dake tsakani na dashi ba." Da yamma Fatima dasu Ummi suka sa ta canja zuwa wani material kalar ruwan madara, a lokacin kuma kusan duka ƙawayen nasu na nesa sun tafi sai mutum uku kawai da kuma wasu daga cikin ƙawayen su Ummi, kalar kayan ta ƙara fito da hasken fararen idanunta, suka saje sosai cikin wani ɗauri mai kyau da Momi ta sake yi mata. "Kece amarya ta farko a wannan lokacin da naga anyi bikinta bata yi make-up ba Amina, Allah ya shirya miki halinki." Cewar Momin sanda take ɗaura mata ɗankwalin, sai kawai tayi wani murmushi tana kallon ƙunshin hannunta yayin da wata ƙawarsu ta ke cewa. "Amma kuma tayi kyan da wasu amaren ma da yawa basu yi ba, kin san natural look ƙarshe ne." Da haka sai hirar ɗakin ta koma kan kwalliya, kowa na faɗin ko a kwalliya simple make-up tafi kyau, wasu kuma na lissafo masu kwalliyar da ko heavy make-up ɗin suka yi tana yin kyau. Ta sani itama da aurenta bai zo a karkace ba zata yi kwalliyar, amma babu kalar tanadin data shiryawa wannan, ƙunshin ma don su Momi sun takura ne kuma ta san shine abinda kowa zai fara lura dashi akanta. "Dama da kika haɗa kayanki baki ɗebi waɗancan litattafan ba?" Fatima ta tambaya daga gefenta sanda idonta ya kai kan wani kwali a can saman durowarsu na litattafan makarantar ta, litattafan da ta san ba zata taba rabo dasu ba, don kullum cikin bitarsu take yi. "Maryam ce ma ta haɗa kayan ai, ni ban san me da me ta haɗaba, kawai dai tace min ta hada su ne tare da sauran kayan akwatunan." "Allah yasa dai bata haɗa miki da kayan sawa da yawa ba, don yawa zasu yi miki idan aka hada da sababbin, gwara ita a ta ɗan ƙara akan nata. Ina ledar su sallayar da aka kawo, bari na haɗa na kaisu kusa da akwatunan, kar a manta." Fatiman ta faɗa tana ƙokarin miƙewa, sai dai kafin ta kai ga miƙewar Amina ta jawo hannunta da sauri, ta juyo ta kalle ta, idanunta sun kaɗa daga farinsu ta girgiza mata kai. "Ki zauna kawai Fatee, ki bari ko anjima sai ki ɗauko su." Muryarta da kaɗan tafi kuka, kukan dake kwance a ƙirjinta tun bayan ɗaurin auren da su Kawu Mallam suka kirata soro bayan dawowarsu, Kawu mallam ɗin ya danƙa mata sadakinta dubu ɗari a hannunta, da kuma bayan tafiyarsu da ƴanuwansu na Niger suka ƙaraso suna faɗin angon bai je ba... Kalaman da suka sata tambayar me yasa take yaudarar kanta ne? da kansa yazo har nan ya gargaɗe ta tun kafin komai yayi nisa don haka don ya fara nuna mata bala'in da ta kawo kanta cikinsa hakan ba komai bane. Har bayan sallar magariba gidan nasu a cike yake, koina yayi kaca-kaca da ruwa da kuma abincin da aka zuzzubar, sannan ga tarin wanke-wanke fal a gefe, don haka ana idar da sallar magaribar ƴanuwansu na Niger suka fara aiki kotaina, Allah ya taimaka da wutar Nepa don haka akwai haske koina. A lokacin ne kuma motocin ɗaukar amarya suka hallara! *** A cikin motar dake tafiya kan titin Lamido cresent, ɗan karamin mayafin da Ruƙayya ta yafa akan doguwar rigarta ya zame ya sauka kan kafaɗunta, gashin kanta baƙi sidik da ya haɗu dana ƙarin data nannaɗe cikin bun ya fito ta cikin hasken street lights da kuma na fitilar motar ƴan sandan dake jiniya a bayansu, amma bata damu ba, hannayenta na rawa ne yayin da take kokarin sake kiran layin mahaifiyarta daya katse saboda rashin service yanzu da suke magana. Ta samu kiran ya shiga a lokacin da muryar Ashraf dake tuƙa motar da kuma ta abokinsa Bilal da suke kira da B-man ta shiga kunnenta. Ashraf ɗin ne ke tambayar abokin nasa idan har lambar wayar da suke jira an turo masa, amma a gajarce kawai ya bashi amsa yana girgiza kai. "Ina jin ki Ruƙayya kuna ina?" Muryar mahaifiyar tata ta shiga kunnenta daga cikin wayar. Sai a lokacin ta jawo mayafin ta sake rufe kanta sannan tace. "Maamah muna hanya, mun ɗauko Bilal ɗin yanzu zamu tafi can sabon garin, su Ibrahim ma sun je sun taho da police ɗin suna bin mu a baya, muna jira ne yanzu a turo masa da number wanda ya sani a gidan don a tabbatar idan tana nan." Daga cikin wayar Hajiya Nafisa tace. "Ko bata nan ku ƙarasa ku sami iyayenta ko kuma duk wani wanda zai iya baku bayani akanta, duk abinda ake ciki da kun isa you let me know, yanzu zan kira Daddy in gaya masa." Ta gyaɗa kanta kafin kiran ya katse, idanunta na tafiya kan abokin Ashraf ɗin dake danna wayarsa hankali a kwance, tsawon kwanaki kenan suna nemansa amma ba'a same shi ko a waya ba sai a yau da da wanin abokin Ashraf ɗin ya kira cewar gashi nan ya dawo daga Ondo, don haka ba shiri suka taho har wajen da aka kwatanta musu yana nan, kuma cikin sa'a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73