Chapter 65
Chapter 65
ke baza ki so in fara tafiya in gano me akeyi ba? Idan yaso ko ta email sai na rubuto muku abubuwan da zaku tanada?" Aminu ya fada yana kallon Amina da ta gama gaya masa irin tashin hakalin da ta shiga jiya, tana zaune a gabansa tana ƙoƙarin zuba sukari a kofin tea ɗin data take hada masa. Abinda ya faɗa yasa ta yin murmushin da bata shirya masa ba tana kallonsa, kafin tace. "Allah ya shirye ka Aminu, ai wallahi ina jin mutuwar ce kaɗai ma zata iya kashe bakin ka." "Daga fadar gaskiya, yanzu ke tsakani da Allah baza ku so ku sami wata ƴar expo ba? Wannan harkar fa harka ce ta dindin idan an tafi an tafi kenan." Tissue din dake gefenta Amina ta dauko ta jefe shi dashi a fuska. "Aminu wannan fa ba zancen wasa bane." Ya ɗaga duka hannayensa sama. "To shikenan, ai ke yanzu naga alama dama baki shirya mata ba, gashi nan har kin canja sai washewa kike yi wai ke amarya, dan Allah Amma bata yi haske ba?" Ya tambaya yana kallon Amman da ta idar da sallar walha a lokacin, bata amsa ba sai jawai ta juyar da kanta gefe kawai ta cigaba da laziminta. Kuma sai akayi sa'a kafin shima ya kara cew komai wayarsa a gefe tayi kara, ya ɗauka ya shiga sake amsa gaisuwar tarin mutanen da duk bayan ƴan mintuna ake kiransa. Amina ta sake kallon Amma data juyar da kanta tana lazimi, kafin itama ta sunkuyar da nata ƙasa a hankali ta shiga wasa da wani zobe a yatsanta, wani abu take ji yana tokarewa a cikin zuciyarta duk sanda ta kalli Amman. Kusan awar su guda kenan da sauka, awa guda da zuciyarta ta narke lokacin da Ma'aruf ya tsugunna a gaban su Baba harma dasu Baban Kurna da suka yi sa'ar ganinsu don a safiyar ranar suma suka zo, yadda ya tsugunna a gabansu kansa a ƙasa suna amsa gaisuwarsa wani abu ne da girmansa yasa har yanzu ta rasa inda zata ajiye shi a cikin ranta, don har ciki ya shigo ya gaishe da Amma da kuma Aminun, sannan har yanzu idanunta suna hango mata damin kudin daya ajiye a gefen shimfiɗar Aminun lokacin da zai fita. "Guess what?" (Kin san me?) Ta tuna yadda muryarsa ta furta hakan daga bayanta lokacin da ta sake binsa wajen mota tare da wasu yara don su ɗauko kayan nan ita kuma ta dauko jakarta da lokacin da suka tsabar zumuɗi tsaya bata ko tuna da ita ba ta buɗe kofar motar ta fita. Yadda ya tsaya a kusa da ita bayan ta juyo yasa ta kallon gefe ta hango yaran suna tafiya cikin gidan kafin girgiza kanta a hankali idanunta a kasa tana kallon jakar data dauko. "Naga yadda zaki koma idan kin ƙara girma." Hakan yasa tayi saurin ɗagowa ta kalle shi, ya harde hannayensa duka biyi a kirji riƙe da wayoyinsa, kuma a take sai ya bata amsar tambayar da idanun nata ne suka yi masa. "Kamar ki ɗaya da Mamanki, na daɗe ban ga masu kama haka irinku ba." Ruɗani idon nata ne ya tafi lokacin da ta sake sunkuyar da kanta kafin ta iya lalubo muryarta. "Haka kowa yake cewa." Ta faɗa a hankali. "Haka kowa yake gani that's why." Bata ce komai ya sake cewa. "Naji dadin ganinsu sosai Amina, yanzu naga inda kika samo wannan kirkin naki." Bata san lokacin da wani guntun murmushi ya suɓuce a lebbenta ba duk da halin da take ciki. Ta sake ɗagowa ta kalle shi, har a lokacin kallonta yake da yanayin da bata iya fassara shi, yanayin da yake ƙara tuna mata cewa har yanzu bata san inda zata ajiye shi a zuciyarta ba. "Nagode sosai." Sai a lokacin tayi masa godiyar da tunda suka taho a hanya take fama da ita a bakinta tana tunanin yadda zata fade ta, kuma murmushin da yayi a wannan lokacin sai da ya kusan tsinka zuciyarta ba don kalaman Hajiya kilishi dake daure da zuciyar tata tamau ba. A wannan lokacin Ma'aruf na kallonta ne tunanin mai yawa a zuciyarsa, Allah ya sani wani abu ya motsa a zuciyarsa game da ita tun daga ranar da ya fara ganinta. Ya cewa zuciyarsa tausayinta ne da kuma mamakin ganin ƙankantar ta, don a lokacin da Mami tayi masa zancenta da kuma lokacin da ya tsinci sunanta a kayan Jamal, zuciyarsa bata kawo masa ko kadan cewar zai ganta karama irin haka ba. Kuma duk sanda ya sanda yake tare da ita a yanzu yana mantawa da dalilin da yasa ya yarda da aurenta ko kuma yadda na auren nasu ya kasance, yana ji ne kawai kamar zamansu wani abu ne da ya daɗe daga cikin tsarinsa, don abubuwa da yawa ya banbanta da irin zaman da yayi da Rukayya. Tare da Ruƙayya gani yake kamar duk abinda yake yi dole ne, don ita tana da tarin expectation ɗinta akansa, ta daɗe tsara wata irin rayuwa tare dashi a cikin kanta da a wancan lokacin shi ba abinda ke gabansa kenan ba, shi yasa abubuwa da yawa kai tsaye zata gaya masa tace yayi kaza ko ya kamata yayi kaza wanda duk da ba saurarata yake yi ba, hakan baya masa daɗi, amma ko fuskar Amina ya kalla, innocent kammaninta kaɗai yana sashi jin wani cikakken iko irin wanda kowanne namiji ke ji akan iyalinsa. Don haka yadda take kallonsa a wannan lokacin, yasa shi ture abubuwa da yawa a cikin kansa ya tako ya karaso gabanta, ya tsaya dab da ita sosai lokacin da kallon cikin idanun nata ya koma kalar mamaki da kuma ruɗani, irin ruɗanin da ya kula dashi tun ranar da ya dawo ya same ta tana kuka, zuciyarsa ta gaya masa cewa so yake ya rungume ta har sai kayanta sun koma ƙamshin turarensa gabaɗaya, amma yayi kokarin ture zuciyar dake gaya masa hakan yace. "Kin manta baki ɗauko basket ɗinki ba." Ta kuwa juya ta kalli basket din dake ajiye akan kujera kamar bata san dashi ba sannan ta dawo da fuskarta wanda hakan yasa ta ƙara matsowa dab da jikinsa amma sai tayi saurin yin taku baya kaɗan kafin tace. "Abinci ne a ciki, ban sani ba ko zamu yi magariba a hanya, kace kana azumi." Bayan ta faɗi hakan, bata san me yake tunani ba don sai da wasu sakanni suka wuce kafin yayi magana. "Ban san ta yaya zance miki nagode ba, amma I'm really grateful, Allah ya saka miki da alkhairi dear." Dear, dear, dear.... Sunan da ya kasa barin zuciyarta kenan har yanzu, yake rikita zuciyarta duk sanda ta tuno duk kuwa da irin zagayen tashin hankalin da take ciki ba cewar shi kansa a yanzu bai kamata ta yarda dashi ba duk kuwa da yadda komai nasa ke nuna mata akasin haka. "Amina..." Muryar Amma ta dawo da ita zahiri, ta ɗago da sauri ta kalle ta, har Aminu ya gama wayar yana shan tea din data hada masa. "Ko zaki karɓo mana maganin da za'a saka masa yau a cikin gidan, kina shiga ɗaki na farko ne wajen Malam Ibrahim ɗin." Malam Ibrahim Mijinyawa shine ɗanuwansu Fatima mai dorin, kuma gidan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73