Skip to content

Chapter 22

Chapter 22

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

yana gaya masa cewa zai koma halin da baidade da fitowa ba. A lokacin ne kuma idanunsa suka hango masa wata ƴar mitsitsiyar takarda da alamun ta faɗo daga cikin file ɗin ne ba tare da ya kula ba, ya miƙa hannu da sauri ya ɗauko ta... Rubutun Jamal ne, hanwriting ɗin sa... Mamaki ya kama shi tun kafin yafahimci me aka rubuta, don yasha buɗe file ɗin nan ya zazzage shi amma bai taba ganin takardar ba. Kuma mamakinsa bai karu ba sai da hankalinsa ya gane masa me Jamal ɗin ya rubuta a jiki. Amina Sulaiman. Gadon ƙaya. *** Me kuke tunani ya haɗa marigayi Jamal da Amina? Me Hajiya Kilishi ke yi da magungunan Ma'aruf? Me yasa Ma'aruf baya son hayaniyar yara? Me Ma'aruf yake son cimma ne game da bincikensa? Waye ya saka kansa a takalmin Amina?😅 #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. BABI NA SHIDA. ~~~~~~ Wani mai adaidaita sahu ya shigo layin har zuwa ƙofar wani gida mai baranda, kuma da tsayuwarsa Aminu ya fito daga ciki yana dariya alamun sun daɗe suna hira da saurayin dake jan adaidaita sahun wanda shima ya fito bayan ya kashe mashin ɗin, kuma a tare suka kamo wani buhun shinkafa ƙato guda suka shiga kiciniyar shiga dashi cikin gidan, inda tin daga soro ƴar hayaniyar mutanen ciki zata shaida maka cewar an samu baki fiye da mutanen gidan. A tsakar gidan Amma ce tare da ƴanuwanta su uku da suke uwa ɗaya uba ɗaya suke ta kiciniyar hada wasu kayayyaki a cikin kwalaye. Yayarta mai suna Zahra'u da suke kira da Tanti wadda ke zaune a goron dutse ta kalli Amman da ta fito daga kitchen riƙe da ƙaton tire ɗin data yanko kankana tace. "Ni kuwa Halima wai yarinyar nan kaya kala nawa ta ɗinka a cikin lefen?" Amma ta ajiye farantin hannunta a tsakiyarsu kafin tace. "Ina ga kusan rabi ne, ai tun zuwan su Momi ƴar gidan Kawu Mallam wancan satin suka ɗiba suka kai mata wajen mai ɗinkinsu, har da na fitar bikin." Tanti ta gyada kanta tana faɗin. "Ko da naji, don na lura ita bata da wannan niyyar, a baki kawai Amina ta karɓi zancen auren nan amma banda a al'amuranta wallahi." "Kinga ko jiya..." Ɗaya ƙanwar Amman mai suna Ma'u ta shigo zancen. "... Abinda nake gaya mata kenan, nace tunda dai har ta amsa, ya kamata ta saki ranta tayi komai kamar kowacce amarya a haka ne zancen zai cigaba da rufuwa, komai ya tafi daidai." Ɗayar da take ƴar autarsu Safiya tace. "Ai ce miki zata yi hankalinta a kwance yake, ba irin faɗan da banyi mata ba wancan satin amma ƙiri-ƙiri ce min tayi ita ba abinda ke damunta." "Allah ya kyauta, yaya kuka sake yi da ita Hajiya Kilishin? Yaushe za'a fara kai kayan ne? Ya kamata ma aje a ga wajen." Aunty Zahra'u ta tambaya tana rufe ƙaton kwalin da ta gama tara ƴan ƙananun kayan kitchen a ciki. Kuma tambayar ta dawowa da Amma tarin abubuwan da suka faru a cikin wucewar sati uku, yadda ka ranar da taje gidan Tantin a goron dutse, ta hau ta da fada bayan ta shaida mata komai, tace Uba yana da ikon zaɓawa ƴarsa mijin aure don haka ita bata ga aibu a cikin zancen ba, tunda a yadda ta san Baba ta ba zai aurawa ƴarsa mara hankali ba kamar yadda Amman ta kira lamarin. Don haka babu yadda ta iya dole ta ja bakinta tayi shiru, kuma kamar wasa al'amarin auren ya cigaba gudana bi da bi, a yanzu saura sati guda bikin, an karɓi kuɗin aure hade da lefen da bai wani girgiza su ba kamar yadda take zato a gidan Kawu mallam, sannan har sau biyu Hajiya Kilishi ta kira ta a waya tana shaida mata yadda wasu daga cikin al'amarin bikin zasu kasance a wajensu da kuma cewar gidan da za'a kai Aminan a cikin gidan da suke ne. Sannan a jiya ta aiko da ɗan aike ya kawo tulin wasu katinan ɗan aure da ba su ko san yadda zasu yi dasu ba, don haka a dole ta karɓi al'amarin itama suka fara shiri sosai, Baba yana ta fafutukar kayan katako da ƴan kudin hannunsa da kuma wanda yayyensa suka haɗa masa, yayin da ita da ƴanuwanta mata ke iya nasu ƙoƙarin na kayan kitchen da kuma sauran na amfanin gida, wanda su Aunty Safiyan ke ta sintirin zuwa kasuwa tun wancan satin. Sai da al'amarin ya kai duk da irin halin da zuciyoyinsu ke ciki, shirye-shirye a yanzu sun kama kamar dama sunyi tanadin lokacin. Don haka kafin ta bawa Tantin amsa su Aminu suka yi sallama a lokacin suna shigowa da buhun shinkafar nan. "Yawwa master, nagode sosai..." Cewar Aminun bayan sun jingine buhun shi da wani saurayi daya kamo masa, saurayin yayi waje yana fadin babu komai yayin d shi kuma ya juyo ya kalli su Amma dake kallonsa suna jiran ba'asin abinda zai ce. "Haba Amma ke ma fa kin san bana sata, Baba ne ya kira ni yanzu naje na karɓo a wajensa." Ya faɗa cikin raha yana kallon Amman. Aunty Ma'u tace. "Na ga ranar da zaka yi al'amarin ka kai tsaye Aminu, in ma satar kake ai kowa ya san ba zaka kawo gida ba." "Ameen wallahi..." Cewar Aunty Safiya. "Amma da ƙyar ne canjawar Aminu, ai hali ZANEN DUTSE ne." Ya ƙaraso ciki da dariyarsa yana shirin buɗe babin shafin tsokanar Aunty Safiyan da yafi rainawa, amma tun kafin ya zauna Amma ta katse shi. "Zaka koma ne?" Ta tambaya. "Eh yace in ɗebi kati in kai masa." Kai tsaye ya bada amsar da a lokaci guda ta shiga kunnen Amina wadda ta fito daga ɗakinsu a lokacin riƙe da tsintsiyar laushin da abin kwashe sharar data ɗebi abinci fal a ciki kasancewar Aunty Safiya da Aunty Ma'un duk sun zo da ƙananun ƴaƴansu, suna ta dabdala a ɗakin. Riga ce ƴar kanti a jikinta kalar ruwan toka da wani tsohon zanin atamfa da babu mitar da Amma bata yi ba amma ta kasa rabuwa dashi saboda daɗin ɗaurawarsa, sai ta bayar da sabuwar atamfa ma amma shi yana nan, Gashinta mai laushi yana ta fitowa ta saman ɗankwalinta dake zamewa. Tayi wajen sharar ta zubar lokacin da su Amma suka cigaba da zancensu, Aminu kuma ya dage wai sai sun yi cinikin sabuwar motar Aunty Safiyan da mijinta ya siya mata kwanakin baya kasancewar sa mai hali. Sai ta juya ta koma ɗakin a lokacin da wata ƴar Aunty Ma'u mai suna Yusra ke janyo kaya daga cikin drawer ta. "Me kike nema anan Yusrah?" Yarinyar ta juyo ta kalle ta. "Hijabi Aunty Amina, Sallah zanyi." "To ya zaki yi da hijabina, duka sun fiki tsawo... Kije ɗakin Amma ki ɗauko na Hafsa, me yasa ma baki bi su Hafsa aiken ba?" Ta faɗa sanin cewar Hafsan da ƴar gidan Tanti da kuma ɗaya yayar Yusran basu daɗe da fita siyan kayan miya ba. Adam ma tunda ya samu sa'ansa ɗan gidan Tanti mai suna Mubarak suka fita filin ball shikenan sai an gansu kuma. Ta tsugunna tana ƙoƙarin kwashe kayanta bayan fitar Yusran, yayin da hayaniyar ƴan ƙananan yaran da suka ɗane katifar

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73