Skip to content

Chapter 28

Chapter 28

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

net. Sai kawai ya gyada kansa sannan cikin nasa kwantaccen turancin yace da saurayin ya fara shiga ya sanar musu zuwansa tukunna, kuma minti guda bayan tshin hayaniyar da ya jiyo a ciki sai saurayin ya fito yace zai iya shiga. Hannunsa ya zaro dubu guda a cikin aljihunsa ya miƙa masa, ai kuwa ya washe baki yana godiya gami da sake buɗa masa ƙofor ɗakin. Da takalmansa ya shiga amma har a jikinsa yana jin dattin da yake takawa akan baƙin carpet ɗin ɗakin, kuma rashin iska da wari ko ƙansnin wani abinci ya hau kansa a take, amma yayi kokarin dannewa ta hanyar murmushi wa tarin al'ummar ciki dake ta ɗebe kaya don sama masa waje ana faɗin. "Welcome sir." Shi kansa Mr. Okaforn jikinsa rawa yake yi na ganinsa balle kuma tarin ƴaƴan sa da kowannensu ya riga ya zube a ƙasa, kuma cikin gurbataccen turncinsa Mr. okaforn ya shiga faɗin. "Ban san da kanka zaka zo ba yallabai, ai na cewa yallaɓai Faruk ne ya bari sai na dawo aiki tukunna, matata ce ba lafiya muna ta faman jinyarta." Ya fada yana nuna wata tsohuwa dake kwance cikin tarkacen kaya, daga nesa ƙaryane ka banbance ta ma da tarin kayan dake wajen. Ya amsa masa bayanin yayin da ya dawo da kallonsa daga kan matar zuwa tarin ƴaƴan da suka zube a gabansa, kusan su tara wanda da kammaninsu kaɗai ya san duka ƴaƴan Mr. Okaforn ne, yaji a ransa yana ƙudirta cewa ya riga ya gama samun bayanin da yake nema don romon da yake shirin kwaɗaitawa Mr.Okaforn wani abu ne da ko mahaukaci ba zai ƙi tayin ba. Sai dai ɗan adam baya taɓa hango tazarar faruwar wasu al'amuran, don a lokacin da ya buɗe baki zai yi magana ne, a lokacin babbar ƴar Mr. Okaforn ta fito daga wani ɗaki ɗaya tal dake manne da falon, hannunta ɗauke da Hamidan da ta saba a kafadarta a lokaci guda kuma tana ƙoƙarin cusa wasu kaya cikin jakar data ratayo tace. "Papa, make I run go drop their pikin that woman go eat me alive if she returned." ( Baba zanje na kai musu ƴarsu, wannan matar zata iya cinye ji idan ta dawo.) "Mary!" Mr. Okforn ya daka mata tsawar da lokaci guda ta dago da idanunta kuma lokacin gudan itama ta durƙushe kamar ƴanuwanta tana faɗin. "Welcome sir." Ya tuna yadda ta dinga rantsuwa jikinta na rawa tana gaya masa cewa kula da yarinyar take a wajen aikinta ce ta taho da ita saboda an kira ta cewar jikin mahaifiyar tasu ya tashi, idanunsa a rufe ya cigaba da hango ta sanda ta biyo shi har bakin motarsa tana fadin yayi mata rai ya bata yarinyar, kuma ya san cewa sanin da tayi cewa shi shugaban mahaifinta ne, shine kadai abinda yasa bata yi masa ihu ba. A hankali ya taso, ya dawo daga gefen Hamidan dake baccinta har yanzu, tun a gidan ya fahimci cewa baccin da take yi yayi nauyi, don har yazo ya sanya ta a mota, sau ɗaya ta buɗe idanunta ta koma bata sake farkawa ba, jikinsa ya bashi cewar tabbas hakan da matsala don haka kai tsaye ya wuce da ita wani asibiti mai zaman kansa inda aka karɓeta da gaggawa kafin likitoci su tabbatar cewar maganin bacci aka bata wanda da alamu ma ta daɗe tana yinsa don jikinta babu kwari sam, a take aka bata gado aka shiga ɗura mata drip mai haɗe da ruwan magani. Kuma sai bayan da ya sami kansa ne sannan ya iya kiran Mami ya gaya mata dukkan abinda ya faru, bai san me ya faru lokacin da suna waya ba, amma sai a wayar Samira ta kira shi daga baya ta shaida masa cewa gata nan zuwa ta cikin hayaniyar da yake jiyowa a gidan. Ya sake gyara zamansa a hankali yana kallon fuskar yarinyar, wani irin abu yake ji yana ratsawa har can bangon zuciyarsa, yana fito da tarin kaunar daya daɗe da binne ta, yawan ƙaunar yana sashi ganin irin ƙoƙarin da yayi a cikin shekaru biyu nayin nisa da yarinyar, yana sa shi alaƙanta abinda yake ji da cewar haka sauran iyaye ke ji idan suka kalli abinda yake gudan jininsu. A hankali ya lumshe idanunsa yana tuno kalaman Rukayya wanda su suka yi sanadin raba shi da ita. "...bata da lafiya har yanzu Ma'aruf, ƙwaƙwalwar ta bata iya gane kowa, ka matsa daga rayuwarmu na wani lokaci, watarana lokacin da kansa zai zabi dawowarka." Kuma ya yarda da maganarta ne a wancan lokacin ba don komai ba sai don nauyin laifin da ya san nasa ne. Don ranar da ya shaƙe Ruƙayya bayan ya karɓe yarinyar daga hannunta yayi wulli da ita, a wannan ranar ne kanta ya bugu da kujera, har buguwar ta haddasa wani ciwo a ƙwaƙwalwar ta wanda da duk da karancin shekarunta aka fahimci cewa bata iya gane mutane a lokacin, kuma sai likitoci suka bada shawarar cewar a ƙaiyade iya adadin mutanen da zata iya sani a ƙwaƙwalwar tata har sai ta fara wayo tukunna, don haka sanin cewar gidansu cike yake da mutane yasa Baffa ya bada umarnin cewa ko bayan an yaye ta baza su karɓe ta daga hannun Ruƙayyan ba sai tayi wayon da za'a tabbatar ciwon yayi sauƙi tukunna. Kuma bayan hakan sai Ruƙayyan ta sanya shi cikin wannan lissafin shima, tace. "Ka taimaka kayi nesa damu Ma'aruf, wannan rayuwar ba itace mafarkina ba, ko kaɗan ba haka nake hango abubuwa ba a lokacin kake gaya min, kuma Allah ya sani na yin dukkan ƙoƙarina wajen gyara maka rayuwar amma ka ƙi barina don ban kasa ba, don haka ina so mu ka barmu mu gyara tamu, Hameeda baƙuwa ce a duniyar nan bata san komai ba, dan Allah kar son zuciyarka ya hana ka bari ta gina tata rayuwar. Allah ya sani ina tsoron kasancewar ta kusa da kai, bata da lafiya har yanzu Ma'aruf, ƙwaƙwalwar ta bata iya gane kowa, ka matsa daga rayuwarmu na wani lokaci, watarana lokacin da kansa zai zaɓi dawowarka." Kuma bayan wannan ranar bai sake ganin Hamidan ba, abinda ya sani kawai shine a cikin shekaru biyun ya tura mata isassun kuɗin da ya san sunyi yawa ma wajen kula da yarinyar, kuma a watanni shida da suka wuce sanda aka ce Ruƙayyan zata yi aure ya san cewa sun kai ta wani asibiti a makkah, ba zai iya zuwa ba a lokacin don haka Baffa ya tura Hajiya Kilishi da Shukra da kuma wata ƙanwar Hajiya Maimuna suka je can suka duba ta suka dawo. Yaji kansa yana ɗaurewa da tsananin mamakin da ya kasa lissafawa, tsawon lokaci... tsawon shekaru an hana shi da yake mahaifinta da kuma ƴanuwansa raɓarta akan dalilin da har iyayensa suka tsaya akansa, don tun su Samirah na naci da ƙorafi akan suna zuwa gidansu Rukayyan ana hana su ganinta har sai da suka daina suka cire ta a ransu, sai gashi yau ya tsince ta a irin wannan gidan, tsakiyar sabon gari zagaye da tarin arnan da bai san adadinsu ba. A lokacin ƙofar ɗakin ta buɗe, wata Nurse ta shigo da takardar jerin magungunan da za'a siya kafin farkawarta kamar yadda

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73