Chapter 59
Chapter 59
makaranta da ya kamata ace iyayena ne suka yi min, hatta kuɗin jarabawar karatuna tsaf su suka biya min har muka kammala, don ban daɗe da shiga makarantar ba mahaifina ya rasu abubuwa suka sake harigitsewa a gidanmu. Kowacce mace taƙi fita tare da ƴaƴanta kuma aka ƙi a raba gado kowa ya koma yana zaman kansa ne da kuma zaman gasa a tsakani don kowacce mace tana so ne ace ƴaƴanta sune suka fi samun arziƙi, musamman Innata da take ganin itace ƙarama an riga an rainata ita da ƴaƴanta don haka bata damu da duk wata hanyar da yayyena ke bi su samo kuɗi ba indai za'a samun, burin kowacce kawai ace ita da ƴaƴan ta su ke ƙyallin maiƙo a gidan. Abinda nazo na tarar kenan bayan na kammala makaranta na dawo, wani abu da tun bana saka shi a raina har ya zamo kwanci tashi nima tunanina ya karkata ga hakan, sai dai ni tawa ƙwaƙwalwar ta raina irin hanyoyin da suke bi, na kasa yarda cewa mutum ba zai iya magance matsalolin kansa a rayuwa ba sai ya tsugunna neman taimakon wani daban, don haka na shiga amfani da ƙwaƙwalwata wajen cimma manufata. Almajirin da kakata ta riƙe Awwalu yana aikin masinja a wani kamfani, da taimakon sa da kuma dabara ta na samu aiki a kamfanin a matsayin mai gyara da kuma harhaɗa takardu... In taƙaice miki zance Amina, wata na biyu a wajen nan na fara karbar kuɗi sama da albashi na ba tare da kowa ya sani ba, kafin a shekara kuwa, ni da Awwalu muna samun daidai da abinda ma'aikatan wajen nan ke samu, ban taɓa bawa wani jikina ba sannan ban taɓa bin wani malami ko boka ba, da wayo da dabarata nake komai ta yadda babu mai zargina kuma dukkan wani bincike ba zai taɓa biyowa ta kaina ba. Kuɗin da nake samu a kowanne wata sai da ya zama hatta a cikin gidanmu babu wanda ake kallo sai ni, mahaifiyata da ƴanuwana duk suka dawo suka raja'a a kaina, aka shiga bani wani irin girma da ban san yana wanzuwa a duniyar nan ba, ya zama zan iya taka kowa a gidanmu in zauna lafiya, nasa aka rushe ɓangaren ɗakunan mu aka gina mana danƙarere da ya tsone idon sauran ƴanuwana kafin daga baya suma su dawo su kwantar da kansu." Muryarta tayi shiru a daidai wannan lokacin alamun ta tuna wani abu da ya saka ta murmushi, wani murmushi da har sautin sa sai da ya fito kafin tace. "A wannan lokacin ne kuma na nemowa kaina mijin aure Amina, munyi ƙoƙarin canja kamfanin aiki ne ni da Awwalu don na yarda da karin maganar da hausawa ke cewa zama wuri ɗaya tsautsayi, don haka muka je kamfanin Bakori a wata ranar laraba, inda kafin mu shiga na hango Alhaji Mansoor ya fito daga ciki ya shiga motarsa, tun da na ganshi a wannan lokacin na sawa zuciyata cewa shine mijin aure na, don haka bamu nemi aikin ba nace da Awwalu mu juya, kuma kafin sati ya zagayo na bi hanyar da sani na ya manne a zuciyar Alhaji Mansoor. Na kashe kuɗi sosai a wannan lokacin duk da ba sai na gaya miki yadda na aiwatar da komai ba zan gaya miki cewa sati guda na shafe ina siyan shafi guda a jaridar da Alhaji Masoor ke karantawa, ana wallafa hotona cikin irin ayyukan da na san dole suka ja hankalinsa. Har da masinjan ofis ɗinsa da ma direbansa na haɗa baki dasu suna bashi labaraina, kuma bayan ya yarda da auren nawa, sai da na toshe bakin mutane da yawa wajen fallasa wani abu mummuna akaina. Lokacin da na shigo gidan nan kuwa Amina da naga Maimuna, a lokaci guda na raina kaina na kuma ƙara yarda cewa sa'ata ce kawai ta shigo dani cikin rayuwar Baffa, don wanda yake da mata irin Maimuna babu abinda zai kaishi auren irina. Amma ban damu sosai ba, tunda na san na shigo daular arziƙi ne kuma na ciri tuta a cikin ƴanuwana da a lokacin suka maida ni kamar mahaifinmu saboda biyayya. Ban daɗe ba lokacin da Maimuna ta sami cikin Shukra ƴarta ta uku, don haka sai nayi amfani da hali irin nawa na ja ɗanta na biyu wato Ma'aruf a jikina, na so haɗawa har da Jamal ma amma shi da yake yafi wayo a lokacin sai ya mannewa uwarsa. Ni na yaye Ma'aruf da hannuna Amina, ni na raine shi tun daga wannan shekarun har zuwa girmansa, don ko bayan haihuwar Maimuna bai bar wajena ba itama kuma bata yi magana ba saboda nauyi na da take ji a sannan, don a lokaci guda na zage na karɓi gidan, ni nake yin komai musamman da bata da lafiya, bayan tayi haihu kuma ni nayi ɗawainiyar da ƴanuwanta ma basu yi ba, hakan yasa a lokaci guda na samu soyayyar kowannensu, hatta Baffa kuwa, don sanda ya aure ni ba zan tantance irin son da yake min ba, amma a cikin shekara guda sai da na tabbata ni da Maimuna munyi kunnen doki a zuciyarsa. Soyayyar kowa na siya tsakani da Allah don bana yarda da gaibu Amina, kamar yadda baba yarda da aikin wani boka ko malam da baya zuwa ko'ina, ni ina yin shiri na shekara da shekaru ne ba na wani ɗan lokaci kaɗan ba. A haka rayuwa ta cigaba da tafiyar mana har ta kai na fara haihuwa nima, a wanann lokacin tsananin kirki da kyautatawata yasa na kere Maimuna a zuciyar Baffa ta yadda ita kanta bata damu ba, don tana ganin cewar na cancanci hakan." Tayi shiru wucewar wasu sakanni tana kallon Aminan kafin ta cigaba. "Bari na gaya miki wani daga cikin babban sirrina don ki ƙara tabbatarwa cewa da gaske nake al'amarina... Nice na gurguntar da Maimuna..." Babu shiri Amina ta ɗago ta kalle ta, idanunta na haskawa da tsananin mamakin da yake ƙaruwa akan wanda take ciki. Sai kawai tayi murmushi mai zurfi tana kallonta itama. "Ƙwarai Amina, ni na saka Maimuna ta rasa ƙafafunta, kin san dalili?" Ba ta bata damar amsawa ba ta cigaba. "Na gaya miki Maimuna tana kyau, to labulen ɗaki na kawai nake ɗagawa in hango ta ranar girkinta ta nufi ɓangaren Baffa, idan tayi kwalliyar nan bana iya daurewa kishina dake tasowa Amina, rana daya na yanke cewar ba zan iya jurar cigaba da ganin zuwanta ba don haka takanas na tafi asibiti na samu wani ma'aikaci a ɓangaren ƙashi, na bashi maƙuden kuɗaɗen da a lokaci guda ya bani wani magani mai kama da poison wanda ke lalata har ƙashin mutum. Kuma sai da na jira har bayan watanni huɗu da rashin lafiyar zazzaɓi ya kamata sannan na haɗa baki da wani yaro daga Nijar yazo har gida yayi mata allurar maganin nan a matsayin likita, kuma babu wanda ya san ni na dauko shi don nambarsa na sanya a wayar Baffa da sunan likitan gidan Dr. Ashiru, nace idan yazo yace Dr. Ashirun ne ya turo shi. Kuma bayan yayi mata allurar ƙafafun nata sun lalace gabaɗaya na bashi kuɗi ya koma ƙasar sa Nijar, shi kuma Dr. Ashiru yazo yace bai san yaron ba, da aka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73