Chapter 17
Chapter 17
da cin abincinsa yayin da ƙamshin curry da kuma naman dake cikin abincin ke gauraye ɗakin, ya kai hannu yana cusa yatsunsa cikin gashin kansa, wani abu da ya riga ya zama ɗabi'arsa kafin yace. "Ka san me Mami take ce min yanzu? Wai inyi aski kafin in shiga gida, don Inna Danejo na tashi da safen nan abinda ta tambaye ta kenan." Ba shiri Ishaq shima yayi nasa murmushin kafin ya gyaɗa kai don har ya hango irin rigimar da za'ayi da Ma'aruf din da ba zaiyi askin ba da kuma Inna Danejon da ba zata haƙura, don kafin tafiyarsu London ta kawo dalilai sun fi ashirin na cewar rashin lafiyar Ma'aruf tana maƙale da gashin kansa ne, Baffa ne kawai bai bada goyon baya ba da tuni sai dai Ma'aruf ɗin ya tashi yaga kansa ɗal! "Hular sanyi kawai zaka dauka, in zaka shiga wajenta ka saka kace anyi askin ba'a bude kan ne." Ya faɗi hakan lokacin da ya gama neman abinda yake so a jikin Tvn don haka ya ajiye remote din ya juyo ya kalle shi. "Za'a kawo maka motar ka ne?" "Eh, na kira direban Office tun dazu nace yaje ya ɗauka ya kaita Carwash, I'm sure kafin 12 zai dawo da ita." Ishaq ya gyaɗa kansa. "Shikenan mu haɗu a gidan, nima can na nufa idan na tashi insha Allah." Ya faɗi hakan yana juyawa hanyar ƙofa, idanun Ma'aruf suka bishi da kallo yana tunanin wani abu, kuma sai da ya isa ƙofar da zata fitar dashi waje har ya buɗe ta sannan yayi saurin kiran sunansa. Ya kuwa juyo a take kamar shima dama jiran kiran yake yi. Ma'aruf ya girgiza kansa yana kallonsa. "Wallahi ban ga yarinyar ba Ishaq, kawai dai na bata wani saƙo ne da na san dole ba zata taba yarda ba." **** 11:30Am. "Na yarda!" Kalaman guda biyu suka fito daga bakin Amina lokacin da take tsugunne a gaban iyayenta guda biyu da dukkan fuskokinsu ke haskawa da tsananin mamaki. Tata fuskar fayau take, ba abinda zaka iya tsinta a jiki. Ta gyara zamanta sannan ta sake maimaitawa kamar wani ya sata. "Na yarda zan aure shi Baba." Maimaitawar ta fiyo tare da faɗowar flask ɗin ruwan zafin da Amma ta ɗauko don juyewa Baba ruwan wanka, ya subuce a hannunta ya faɗi har ƙasa, kwalbar ciki ta tarwatse yayin da ruwan zafin ya fallatsa akan dukkaninsu. * Me kuke tunani yasa Amina ta yarda da auren Ma'aruf? Wacece ainihin Hajiya Kilishi? Me ya faru da Jamaal? Shekarun cikin labarin sun wuce da wasu abubuwa da zamu fara kwance su daga Babi na gaba insha Allah...☺️ #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. BABI NA BIYAR. ~~~~~ Ana gobe sallah ne ranar, ita da Maryam sun je kasuwa siyayar mayafai da takalmi, tun kusan sha biyu suka fita har mutane suka fara alwalar sallar la'asar basu gama siyayyar ba. Maryam dake riƙe da ledar kayan da suka siyo kalli tsinken kwakwar da suka auno tsawon kafar Hafsa dashi tace. "Ai wallahi dama na san takalmin yarinyar nan shi zai bamu wuya, kafa kamar ba ta mutane ba ƴar firit da ita." Amina ta share gumi a gefen fuskarta tace. Har tunani nake ko ba daidai na auno ba wallahi gashi mun kusa gama siyen komai..." Bata karasa ba ta tuno da sakon garin da Amma tace su siyo zata yi teba dashi da daddare. "Kin san na manta da garin Amma... zo muje wancan layin na san zamu samu." Maryam ta girgiza kanta. "Mu raba tafiyar kawai lokaci ƙara wucewa yake, ga wani kantin takalma can, bari naje na duba idan ma ban samu ba zan jira ki sai kizo ki same ni anan." Da haka suka raba tafiyar, Maryam ta tsallaka ta cikin cunkoson mutanen ta nufi kantin ita kuma tabi layin gefensu inda nan ɗin ma turuwar mutanen ce wadda dama sun riga sun shirya mata, don tun ana saura sati ɗaya sallar suka so zuwa kasuwar amma rashin haɗuwar kudin yasa dole sai yau suka samu suka fito. Ga rana, ga azumi amma yadda mutane suka hargitse baza kace kowa a gajiye yake ba. Da kyar ta samu ta ɓulla layin da masu garin suke, kuma akan ragin naira hamsin ɗin da zasu yi kuɗin mota dashi, sai da ta kusan shanye layin tana tambaya da ƙyar ta samu wani acan ƙarshe yace zai rage mata. Tana tsaye yana ƙoƙarin auna mata, wani yaron shagon nasa ya shigo, irin samarin nan ne masu magana, yana shigowa ya haye kan ɗaya daga kantocin shagon yana fadin. "Allah na tuba a yadda ake wannan ranar ga azumi ai wallahi komai talauci na ba zanyi aikin sauke gari ba, don mugunta kaga yadda suke jefo musu buhun nan daga sama, wani har sai ya kai ƙasa wallahi kafin ya ɗago." Maganar ta ɗauki hankalinta, tana hango yadda nauyin buhun gari yake ace mutum ya dauka a wannan ranar. "Yau ma mota ta sauka ne?" Mai shagon ya tambaya yana miko mata ledar garin. "Gata can yanzu ta tsaya, ka san shi Auwalu ko da goma yaga sunyi ƙasa sai yayi aike." Ta miƙa masa kuɗin tana faɗin ta gode, amma kafin ya karba saurayin yayi saurin miƙo hannu ya karba sannan ya miƙo mata yana mata murmushi, irin halin ƴan kasuwa. A kofar shagon kuwa tana fita taga motar ana ta sauke garin, tausayin masu yin dakon ya tafi har cikin ranta ganin yadda ko a ido buhun ke da nauyi, tana tafe tana ganin fuskokinsu lokacin da idonta ya kai kan fuskar da ta sa ba shiri hannunta ya saki ledar garin nan... Mahaifinta ta gani dauke da wani katon buhu yana ƙoƙarin kaiwa inda sauran ke saukewa, mahaifinta dai Baba, Baban daya shirya tsaf a yau ya fita suna yi masa a dawo lafiya. A wannan lokacin yana gaɓar farfaɗo wa daga karayar arzikinsa ne, don duk da kokarinsa wajen yi musu kayan sallah, har saida aka haɗa da kuɗin Aminu kafin komai ya isa, bata san lokacin da hawaye ya fara biyo kuncinta ba, taga ya sauke ya koma sake ɗauko wani... Baba mutum ne mai tsananin son dogaro da kansa kowa ya sani, yayyensa duka sunyi kokarinsu wajen tallafa musu tunda al'amarin ya faru, amma babu wanda ya isa ya ɗauke maka cin yau da gobe sai Allah, don haka ta san nauyin ya cigaba da tambayarsu ne yasa har ya kawo kansa yin wannan aikin don kula dasu. Hawayen ya cigaba da bin fuskarta yayin da zuciyarta ke rawa a kirjinta, tunanin ta ɗaya ne a lokacin, idan har mahaifinta zai iya sadaukar da girmansa yayi wannan aikin don kawai ya fita kunyarsu meye su baza suyi don fita tasa kunyar a duniya da kuma lahira ba? Ta share hawayenta lokacin da wani mai wulbaro ke miko mata ledar garin da Allah yaso bata fashe ba. Kuma bata fadawa Maryam abinda ta gani ba, bata fadawa Amma ba, bata fadawa kowa ba, don ta san hakan wani abu ne da Baban ba zai taɓa so waninsu ya sani ba. Kuma a wannan daren sai gashi ya dawo da ledar kaza har guda biyu ta miyar sallah, su Hafsa suka yi ta tsallen murna yana binsu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73