Chapter 6
Chapter 6
cikin maƙogwaron sa yana cigaba da kallonsa yace. "Nayi mana booking flight, gobe zamu koma." Kuma ba don kallonsa yake ba ya tabbata ba zai ji sanda ya amsa da 'Allah ya kaimu' ba. Saboda haka kai tsaye sai ya sake tambaya. "Yaya kake ji?" Ma'aruf yasa yatsu biyu ya shafo saman hancinsa har a lokacin bai buɗe idonsa ba yace. "Ina ji ne kamar zan mutu saboda yunwa, nace ka taimaka min da abinci amma kana ta masifa, Idan na sake fita daga nan kar barni kawai kar kaje beli na." Ba shiri wani guntun murmushi ya suɓuce a fuskar Ishaq ɗin na tabbas ɗin da yake dashi cewar ya dawo daidai, don har abada irin Ma'aruf guda daya ya sani a duk tsayin rayuwarsa. Ma'aruf yaji lokacin da ya fita amma duk da haka bai bude idanunsa ba, hoto ɗaya ne ke yawo a cikin kansa, hoton ɗakin bincikensa, yana hasko tarin takardu da kuma hotunan da suke cikin ɗakin nan, sannan yana hasko yadda hanya ta ƙarshe da yake tunanin zata kai shi ga nasara bayan shekaru huɗu ta rushe har garinta, wanda takaicin haka shine sanadiyar tashin ciwon nasa da abinda yayi har suka taho nan. Wata jijiya daga gefen kansa ta bullutso cike da wani sabon takaicin da ya sake ratsa shi, sabon takaici... Don wannan ɗauke yake da wani layi na fargaba da kuma tsoro, tsoron da bai taba ji a ransa game da ciwon nasa ba tsawon shekaru goma da suka wuce, maganganun Ishaq suka sake haskawa a cikin kansa. ...idan komai ya cigaba da kasancewa yadda yake tafiya, kana gab da rasa hankalinka gabaɗaya Ma'aruf! *** Alhaji Muhammad Mansour Bakori, sanannen mutum ne wanda yake da babban Kamfanin yin robobi a garin Kano tare da ƙaninsa Alhaji Usman, wanda su biyu ne kacal a wajen iyayensu, mahaifinsu ya rasu shekaru da daɗewa amma mahaifiyar su tana raye. Alhaji Mansour Bakori yana da mata biyu da ƴaƴa goma sha ɗaya, yayin da Alhaji Usman bai taba haihuwa ba tsawon shekaru talatin da aurensa, wanda hakan ya faru ne sakamakon wani hatsari da yayi tun kafin tun yana saurayi har ya zame masa sanadin hakan, shi yasa kowa a danginsu yake girmama matarsa Hajiya Madina da kuma jinjina mata na zaman da take dashi a duk shekarun nan alhali ita lafiyarta ƙalau. Matan Alhaji Mansour biyu, Uwargidan itace Hajiya Maimuna, wata mata mai kirki da kuma alkunya, ɗanta na farko Jamal ya rasu shekaru goma da suka wuce, daga shi sai Ma'aruf wanda shi a wajen kishiyarta ya girma, sai Shukra, Munaya, Abdurrahim wanda shi tun yana shekaru biyu a duniya ya kamu da matsalar rashin magana amma yana ji kamar kowa, sai kuma autarsu Zahra. Hajiya Kilishi itace mata ta biyu a gidan, wata mace ce mai tsananin kirki da kyautatawa, don faɗa ko da na rana guda bai taɓa haɗa su da Hajiya Maimuna ba tun zuwanta gidan, wani irin zaman lafiya da mutunta juna ne a tsakaninsu tun farkon zuwanta gidan, hakan yasa basu kaɗai ba ko wanda yake nesa ba zai taba cewar su ɗin kishiyoyin juna bane idan ya gansu tare. Ita ta raini Ma'aruf tun daga watannin da aka yaye shi har zuwa girmansa na yanzu. Hajiya Maimuna, mace ce mai hali irin na mutanen da, tsananin kawaici akan abinda suke ganin shine daidai, don haka tun daga ranar da Hajiya Kilishi ta karɓe sshi bata ƙara nuna cewa shi nata bane, a suna kawai Ma'aruf ya santa a matsayin mahaifiyarsa, amma a wajen Hajiya Kilishin da suke kira da Mami ya samu dukkanin wata kulawar da ɗa ke samu daga mahaifiyarsa. Ita ta raine shi da ƙarfin jikinta da kuma na zuciyarta, har zuwa girmansa kuwa ya zama tsakaninsa da Hajiya Maimuna gaisuwa ce kawai amma Mami ce komai nasa, duk da ƴadda wasu daga cikin ƴanuwan Hajiya Maimunan suke nuna rashin jin daɗin su akan hakan a yanzu da ya zama shine kaɗai namiji babba a gidan. Ƴaƴan Hajiya Kilishi biyar ne, dukkaninsu mata kuma dukkanninsu harafin sunansu ya fara ne da harafin S, Safiyya, Salma, Surayya, Samira da kuma Sahla kamar yadda take so, don a wajen Daddy babu ruwansa da raɗin suna, duk wanda iyayensu mata suka zaba shi zai saka ba ruwansa. Zahra ce ma kawai taci sunan Inna Danejo 'Fatima' kamar yadda Hajiya Maimunan ta nuna tana so a saka. Hajiya Maimuna ta sami matsalar shanyewar ƙafafu bayan ta haifi ƴarta ta ƙarshe Zahra, kuma babu irin maganin da ba'ayi ba a ƙasashe daban- daban amma ba nasara, don haka a dole yanzu sai akan Wheelchair take yawo. Gidan Alhaji Mansour dake unguwar NNDC quarters a garin Kano, ƙaton gida ne mai ɗauke da bangare-bangare, akwai ɓangaren iyalansa guda biyu wanda kowanne iri daya ne, ƙaton falo da ɗakuna hudu kowanne da banɗakinsa a ciki da kuma sauran wajaje irin Kitchen, store, courtyard da dai sauransu, sai bangarensa inda shine waje na farko a gidan mai ɗauke da ɗakuna biyu da falo da kuma wajen meeting ɗinsa inda yake ganin baƙi a gida. Akwai bangaren boys quarters inda masu a gidan suke zaune sai kuma wajen Inna Danejo kakar gidan, wato mahaifiyarsu Alhaji Mansour inda itama take da ƙaton falo, ɗaki ɗaya da kuma toilet, sai ɓangaren ƴan aiki, sai kuma bangare na karshe daga gefen hagu na harabar gidan, wato bangaren Alhaji Usman da suke kira da Alhaji Baba, wanda shima da a gidan yake tare da matarsa daga baya sai ya siyi wani gida gaba dasu kaɗan ya koma, don haka wajen a ƙulle yake babu kowa. Ishaq abokin Ma'aruf ne kuma ɗan'uwansa, don da Mahaifiyar Ishaq ɗin da Hajiya Maimuna iyayensu ɗaya, asalin mahaifinsa ɗan Kaduna ne kuma shi kaɗai iyayensa suka haifa, mahaifinsa ya daɗe da rasuwa amna mahaifiyarsa sai da yazo matakin shiga Jami'a ne sannan Allah ya ɗauki ranta, don haka da shawarar Mami, Hajiya Maimuna ta tambayi Alhaji Mansour da kowa ke kira da Baffa, Ishaq ya dawo gidansu da zama daidai lokacin da Ma'aruf ke kokarin shiga Jami'a. Mamin tayi haka ne don ganin ta samowa Ma'aruf sauki akan halin alhinin ɗanuwansa da har a lokacin bai gama warkewa daga ransa ba, don haka tare da Ishaq ɗin Baffa ya ɗauki nauyin karatunsu a wata Private University dake London har suka kammala, kuma hakan ya sanya shaƙuwa sosai a tsakaninsu duk da cewar ɓangare daban-daban suka karanta. Ma'aruf ya karanci harkar Kasuwanci ne yayin da Ishaq ya karanci ɓangaren aikin lawyer kamar yadda yake da buri tun yana yaro. *** Washegari... No. 58 Mafara Street, NNDC Sharaɗa Qauters. .07:30 Pm. Tun daga ƙofar gidan zaka gane cewar anyi wani taro ne a gidan an watse, don hatta gate din a bude yake gabaɗaya sannan ga motoci daga ciki suna kokarin fitowa. Idan ka biyo ta cikin mutanen, zaka wuce ko'ina hanya ta kai ka har ɓangaren Hajiya Maimuna inda taron mutanen yafi yawa musamman a ƙaton falon ɓangaren da zaka tarar wanda yake cike da tarin mutane gabaɗayansu mata, kowa na zaune da abokin hirarsa yayin da ƙamshin turarukansu ya haɗe da ƙamshin daddaɗan abincin da aka gama ci a falon, don ga tarin plates nan wasu ma har da ragowar abincin sannan kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73