Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

ta daga ramin da zuciyarta ke shirin kai ta, taji kamar ta miƙe tsaye tana karkaɗe raunin daya baibayeta tun bayan data ɗora idanunta akan Ma'aruf ɗin. "Shikenan, Allah ya taimaka. Ka taho min da magungunan naka?" Wata ƴar ƙaramar jakar daya shigo da ita a gefensa ya ɗauko ya miƙa mata ba tare da ya janye idonsa daga Tvn ba, kuma da Ma'aruf ya saurara da kyau, zai ji lokacin da ta sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya kafin ta buɗe jakar tana nazarin kayan ciki. A lokacin Samirah ta shigo ɗauke da lemo mai sanyi da kuma cake a faranti, yarinya ce ita mai tsananin kula da son kyautatawa kowa, shi yasa kusan komai na gidan yanzu sai da izininta ake yi, hatta abincin Baffa ta daɗe da karɓar ragamarsa sai dai ko in tana makaranta sai wani a cikin yayyenta yayi, don su Hajiya Kilishi basa girki a gidan. Kuma ko a ɓangaren Hajiya Maimuna akayi baƙi Sameerah ita zata fara tarbarsu da waje da kuma kayan cima kafin kowa, ƙarya ne wani ya shiga gidan nan yace ya fito da yunwa in har tana nan. "Dan Allah Yaya ka bani kwangilar sati ɗaya in cicciko maka da waɗannan kasusuwan, wallahi baka ga yadda ka rame ba." Ta faɗa tana ajiye masa farantin a gabansa. Ma'aruf ya ɗago ya kalle ta yana murmushi lokacin da Hajiya Kilishi ta mike riƙe da jakar magungunan tayi hanyar ɗaki. Kusa dashi ya nuna mata a kujerar yace. "Zo ki zauna muyi ciniki Please, how much do you need? ( Nawa kike so) coz ƙarfi nake nema nima yanzu." Ta kuwa ƙyalƙyale da dariya daidai lokacin da Shukra (ƙanwarsa dake bi masa a wajen Hajiya Maimuna) ta shigo daga hanyar wajensu, kuma ganin Ma'aruf ɗin yasa tayi murmushin dake ƙarawa fuskarta kyau tana fadin 'Alhmdlilah" sannan ta juya da sauri don ɗebo takardun research ɗin da ta tara zai duba mata. Don haka Ma'aruf bai samu shiga wajen Hajiya Maimuna ba sai da yamma tayi sosai. Kuma a falo ya same ta itama, tana zaune daga kan Wheelchair ɗinta tana karatun azkar ɗin yamma, yayin da Zahra da kuma Sahla ke zaune suna kallon video ɗin wani tutorial daga labtop ɗin Munaya da suka aro. Ya durƙusa har kasa a gabanta ya gaishe ta cike da girmamawa, girmamawar da bayan ita baya taɓa kallonta da wani abu. "Yaya jikin naka?" Muryarta mai taushi ta tambaye shi bayan sun gama gaisuwa. "Lafiya ƙalau Hajiya, naji sauki ai." "Allah ya ƙara sauki. Kaje wajen Inna ne?" Ya girgiza kansa. "Yanzu zan shiga idan na fita." Tayi shiru yayin da idanunta ke nazarinsa, ya sunkuyar da kansa ƙasa sanye da dogwayen kaya na farin yadin da ko a ido mai laushi ne don ya kwanta a jikinsa sosai ta yadda ya fito da ƙirar jikinsa mai tsari, wani abu dake ɗaya daga cikin abinda ke ƙara masa kwarjini a idon mutane. A lokacin ne kuna maganar ƴar uwarta a kwanakin baya ta haska a cikin kanta. 'Ban ce ki tada hankalin gidan ki ba Maimuna, amma abin yayi yawa, kin rasa Jamal kuma Ma'aruf shine Babba a gidan yanzu, ko yaya ne ya kamata ya dinga tunawa cewa ke kika haife shi ba ita ba...' Tayi saurin kawar da wannan tunanin tana haɗiye wani abu da batasan sunan sa ba, a lokainda ƙwaƙwalwar ta ke tuno mata damagaar da Baffa ya yanke taauresa jiya da daddare, sai dai har ta buɗe baki zata yi masa magana kawai taga ya miƙe tsaye yana yi mata sallama, sai ta mayar da maganarta a hankali sannan ta amsa, kuma murmushin da yayi wa su Zahra a matsayin amsa tasu sallamar ya sake ɗago wani abu a zuciyarta da ta daɗe tana danne shi tsawon shekaru. Idanunta suka bishi da kallon da har ya rufo mata ƙofar falon hankalinta bai koma kan karatun da take yi ba. A falon Inna Danejo Ma'aruf ya tarad da ita tana sallah daga kan sallayar ta da anan take kwana ta yini in har ba tashi ne ya kamata ba, don haka ƙafafunsa suka tako cikin falon a hankali, yana jin kamar zai nutse a sabon carpet din da aka shimfide mata falon dashi, (wall to wall). Ya karaso ya sami waje daga gefenta ya jingina da wasu ƙullin kayanta da ya san na wanki ne sannan ya zaro wayoyinsa daga aljihu. Tarin messages ɗin da har yanzu bai duba ba suka shiga tururuwa akan screen ɗinsa, sai ya zura hannunsa ɗaya cikin gashin kansa kawai sannan ya cillar da ita a gefe ya dauko ɗayar. A ciki ya lalubo nambar Faruk, aboki ɗayan da yake dashi bayan Ishaq kuma mataimakinsa a wajen aiki. "Ka gaya min ba maganar aiki bace dan Allah B, don wallahi as we are talking now ina Coldstone ni da yara, kowa yana son hutu a rayuwarsa Ma'aruf." Faruk din ya faɗi hakan tun kafin yace komai, don shi kansa ya sani ba zai iya kirga adadin wayar da suka yi akan zancen Office ɗin ba tun bayan dawowarsa. Sai dai kalmar yaran da ya furta ta daki zuiyarsa da wani irin tasirin da baya taɓa sabawa dashi don haka ba shiri ya tafi kai tsaye ga abinda yake son tambayarsa. "Account number Daniel zaka turo min." "Me zaka yi da ita? Na gaya maka gayen yana can har yanzu da kumburarriyar fuska wallahi." Ya cije leɓɓensa a hankali yana hango fuskar Daniel ɗin a idanunsa, sanda ya cakumo wuyansa yana kai masa naushin da baya ƙarewa, kuma duk da zafin dukan nan Daniel baya kare ba ko sau ɗaya, kallonsa kawai yake da idanunsa dake nuna tsantsar mamaki da kuma ruɗani har ya fita daga hayyacinsa. Ya sake tuno yadda ya jawo shi ya fito dashi har waje ɗimbin jama'ar Office ɗin na kallonsa, da lokacin da ya saka shi a boot din motarsa ya rufe sannan yaja motar zuwa gida, yaje gidan kuma ya fito dashi dashi daga boot ɗin motar ya ja shi har falon Baffa a lokacin ma ya riga ya suma... Sai kawai ya sake mai da kansa baya, yana motsa ytsunsa cikin gashin kansa a hankali, idonsa ya cigaba da hango masa yadda a lokacin duk da baya cikin hayyacinsa amma nauyin idanun Baffa suka sa ya durƙushe akan gwiwoyinsa sanda ya kai Daniel ɗin har gabansa, amma kuma duk da hakan bai fasa gayawa Baffan cewar wai ya kawo shi ne ne don ya kore shi daga aiki ba... "Just send it Umar..." (Kawai ka turo min...) Ya faɗa yana katse tunaninsa kuma bai ƙarasa abinda zai ce ba hayaniyar yaran nan ta shiga kunnensa daga cikin wayar, don haka ba shiri ya katse kiran yana ƙoƙarin ture abinda ke ƙoƙarin tasowa daga ƙasan zuciyarsa. Ya cillar da ita gefen ɗayar itama sannan ya rufe idanunsa yana cigaba da motsa yatsunsa a cikin gashin nasa daidai lokacin da Inna Danejo ta idar daga sallarta. "Wai rana kika koma bautawa ko me? Wannan wace irin sallah ce bayan la'asar?" Inna Danejo ta kalle shi zuciyarta fara ƙal! da farin cikin ganinsa lafiya ƙalau, don a cikin addu'inta na tsukin kwanakin bata jin ko kanta ta ambata a cikin addointa banda fatan nema

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73