Skip to content

Chapter 39

Chapter 39

Farar Wuta Book One Complete Hausa Novels 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

"Na san da wuya idan kaci wani abun, ga abinci nan ma nasa Samira ta tanadar maka tun dazu, a miƙo maka ne?" Ya girgiza kansa tun kafin ma ta ƙarasa, don baya tunanin a yanzu ko ruwa zai iya sha, tarin abubuwan da ƙwaƙwalwar sa da kuma zuciyarsa ke rabawa basu da adadin da har zai sami nutsuwa ta cikinsu. Saboda haka sai kawai ya canja zancen da cewar. "Na zata ma kowa yayi bacci Mami." "Baccin mai gaskiya? Yanzun nan fa suka dawo daga kai sauran amaren, ai gidan nan yana nan kamar rana don baka shigo daga ciki bane, kuma naku ɓangaren ai yasha dab-dalarsa, sai da kayi haƙuri da abinda zaka gani." Wani guntun murmushi da bai san dalilin sa baya suɓuce a gefen fuskarsa, don shi a yanzu baya son ganin yarinyar baya jin akwai abinda ya dame shi na harkar auren, sai kawai ya zaro hannunsa daga cikin gashin nasa yana bude kofar motar dashi sannan yace. "Shikenan Allah ya bamu alkhairi, Allah ya huta gajiya, ta amsa kafin ya kashe wayar. Ya tsaya daga wajen yana kallon ginin gidan kafin ya sake komawa kan wayarsa ya danna wata number, bugu ɗaya biyu matar dake ɗaya layin ta dauka, kuma bayan sun gaisa ta tabbatar masa da cewar Hamida tayi bacci sannan ya katse wayar. Inda ya kira ɗin, wani Creche ne kamar asibiti inda ake bawa yara kulawa ta musamman, na wasu ƴan Turkey ne musulmai, amma akwai hausawa a cikin ma'aikatan nasu, asibitin da aka kwantar da Hamidan ne da farko suka bashi shawarar ya kawo ta wajen, kuma sai hakan yazo daidai da cewar bai shirya kaita gida a lokacin da ake hidimar bikin nan ba. Ranar farko da suka je, tayi rigimar cewa ba zata zauna, amma cikin ƙwarewar aikinsu da kuma tarin abubuwan wajen dake kama zuciyar yaro, sai rigimar tata bata je ko'ina ba. A iya kwanakin nan yana zuwa kullum ya ganta wanda hakan yasa yayi sabo da ita sosai don har ta fara sakewa dashi tana amsa duk ƴan ƙananan tambayoyin da yake mata, da farko ne duk maganar da zai yi mata sai dai ta kalle shi kawai, sai bayan barinsu asibitin ne da ya kawo ta nan sannan ta fara yi masa magana, kuma ya fahimci tana da maganar sosai, kawai bata gama sabawa dashi bane har yanzu, amma ya san aƙalla suna making progress din da za'a zo gabar da zata fahimci cewa shi mahaifinta ne. Ya sake kallon gidan, babu maigadi don haka shi ya shiga da motar, sannan ya sake rufe gate din ya dawo, ƙafafunsa suka taka kan barandar gidan sannan ya tura ƙofar falon ya shiga a hankali. Hasken fitulun ɗakin ya shiga idanunsa tare da hotunan kayan da suke ciki, daga kujeru labulaye dama carpet ɗin cikin komai kalar Army green ne da kuma brown, babu wajen dining don haka kofofin korido biyu ne kawai da ya san ɗaya ta kitchen ce ɗaya kuma ta hanyar ɗakuna, sai kawai ya juya a hankali ya rufe kofar falon. Iskar da akeyi a waje mai zafi ce, yaji ta bayan ya fito daga Acn motarsa, amma a yanzu da ya shigo gidan yaga yadda labulayen falon ke dagawa sai yaji kamar ba irinsu ɗaya da ta wajen ba. A hankali ya zame takalmansa daga kafarsa sannan yayi gaba, ya kuwa ji ƙurar da Mamin ke fada amma bai damu ba, ya shiga hanyar koridon a lokacin da yake jin wani abu kamar bugun zuciyarsa na ƙoƙarin canjawa. Ƙofofi uku ne a ciki, kuma bai buɗa kowacce ba don guda ɗayan dake gefe da kuma ta can karshe ta kasan kofofinsu ya kula duk fitulunsu a kashe suke, ta farko daga gefen daman sa ce kawai hasken cikinta ya saje da na cikin koridon. Don haka kai tsaye ya ƙarasa gare ta ya ɗora hannunsa akan mariƙinta, sannan ya buɗe ta a hankali ba tare da tayi wata ƙara ba, kuma babu wani hijabi idanunsa suka sauka akan matar da kowa ke kira da tasa, ɗan karamin frame ɗin jikinta na naɗe a gefen gadon ɗakin, ta jingina kanta da gefen gadon idanunta a rufe, rabin fuskarta na shigewa cikin gadon yayin da hasken fitilar ɓangaren ɗakin ya haske ɗaya gefen fuskar tata. Hijabin dake jikinta ne ya shaida masa cewa sallah tayi, kuma kafin ya iya sake wani tunanin ta buɗe idanuwanta duka biyun ta kalle shi. Bai san me ya zata ba, bai san yadda yayi tunanin zai zo ya ganta ba, bai taɓa ma hasko ta a cikin kansa ba balle ya kintaci yanayinta, amma a lokaci guda yaji wani abu ya balle daga cikin zuciyarsa ganin ƙanƙantar ta, don duk a lissafinsa irin Ruƙayya zai gani, amma wannan ƙarama ce sosai, idanunta are so young haka ma jikinta ƙarami ne, yawun da ya sake haɗiyewa yana kallonta yasa wannan karon Adam's Apple dinsa motsawa sama da ƙasa. Kuma a lokaci guda kallon dake cikin idanunta ya canja zuwa wani abu kamar tsoro, yaga ta mike tsaye da sauri rike da hijabinta sannan ƙafafunta suka yi taku biyu baya, a yanzu ya tabbatar tsoratar tayi. * Lokacin da ta mike tsaye tana kallonsa, zuciyarta ta shiga tseran kilomitoci a ƙirjinta, yayin da take jin ƙafafunta na rawa kamar ma zasu iya daukanta ba, don haka ba shiri zuciyar tata ta shiga ambaton kalaman Innalillahi har zuwa ƙarshe yayin da take cigaba kallonsa. Bata yi tunanin kawai bude ido zata yi ta ganshi tsaye a gabanta ba, bata ma yi tunanin haka yake ba, yadda take hango shi a tunaninta ya zarta hakan, dogo ne sosai ɗan siriri amma kuma mai cikar halitta, ba fari bane ko kadan haka nan ba baki bane, idanunsa na kallonta da wani yanayi da suke lumshewa, fuskarsa fayau yana tsaye yana kallonta daga bakin ƙofar, kayan jikinsa kalar ruwan toka ne mai irin sealed dinkin nan, babu ko hula akansa sai gashin kansa mai yawa da ya taru. Zuciyarta ta cigaba da fat, fat, tana kallonsa, so take yi ta tantance idan har shi ɗin ne ma ko kuwa aljani, tunda bata ko ji sallamarsa ba, sai kuma wata zuciyar tace mata ta yaya mutumin dake shirin fara nuna mata wutar da ta kawo kanta zai fara da yi mata sallama? Taji kamar ta tafi ta shige toilet din dakin kawai ta kulle kanta, amma wani bangaren zuciyarta ya ture hakan, yana gaya mata cewa ya kamata ta jajirce ta fara ganin abinda zai yi tukunna, don ta gayawa zuciyarta zata iya yafi cikin carbi, kuma dukkan kalaman da ta faɗawa mahaifinta dama kowa suna nan a cikin kanta, don haka bai kamata ta fara karaya tun yanzu ba. Kuma ga mamakinta sai abinda take jira din ya faru. "Assalamu alaikum." Muryarsa mai zurfi ce da a lokaci guda ta daɗa hargitsa tunaninta, tasa numfashinta katsewa a maƙogwaronta. Ma'aruf ya sake lura cewa a tsorace take, don bayan yanayin fuskarta yana iya ganin yadda ta damke hijabin jikinta da duka hannayenta biyu tana cigaba da kallonsa, bata amsa sallamar ba, kamar ma bata ji yayi ba, kamar jira kawai take yi yayi wani abu ta ɓace daga dakin. Ya fitar da numfashin daga

Table of Contents

Chapters

73 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73