Chapter 13
Chapter 13
da kujerar motar sannan yayi murmushi. "Kana magana kamar kana neman wani yaro ɗan karami, sau dubu nawa a rayuwata na ɗauki mota na fita da daddare Ishaq?" Yaji yadda Ishaq din ya fitar da numfashi cike da takaici. "Wai ka haukace ne gabadaya Ma'aruf? Yanzun nan fa muka dawo ƙasar nan, minti biyar kawai kayi a gida kayi wanka ka fito! Yanzu ƙarfe nawa? Tara fa ta wuce, ta yaya zaka ɗauki mota ka fita a halin da kake ciki?" Ya sanya ɗaya hannunsa ya cusa yatsuntsa cikin gashinsa yana tuno abinda ya faru bayan barinsu Office ɗin Daddyn, tsaf ya zayyanewa Ishaq abinda Daddyn ya shaida masa tun a hanya kafin su ƙarasa gida, kuma zai iya rantsewa kamar yadda maganar ta tsorata shi haka ta daki Ishaq ɗin shima, amma duk da haka ya boye ta hanyar gaya masa cewa ya kwantar da hankalinsa kawai insha Allah zasu daidaita komai a hankali, wasu maganganu da jinsu kawai yayi a lokacin da yake furtawar. Don suna shiga gida wanka kawai yayi ya shirya cikin wasu riga da wando duka kalar baki sannan ya dauki wata rigar mai hula (hood) da dogon hannu ita kalar ruwan toka ya dora akai, ya rufe kansa da hular amma duk da haka ana ganin sumar kansa data taru itama baƙa wuluk da ita kamar kayan. Lokacin da ya fito falo Ishaq ya shiga wanka shima, don haka wayarsa kawai ya dauka da muƙullin motar Ishaq ɗin yayi waje, don shi tasa motar tana can gida ba'a dawo da ita ba tun ranar da al'amarin ya faru (lokacin da ya ɗauko mutumin da yayi wa duka daga Office ya kaishi wajen Daddyn.) Ya tabbata Ishaq yaji lokacin da maigadi ya buɗe masa gate ya fita, don bai ko bar kan layinsu ba kiransa na farko ya shigo, amma bai dauka ba, sai da ya katse sannan ya lalubo nambar Sameera a cikin wayarsa ya kira. Sameera itace kusan komai na gidan nasu don itake kula da kusan harkar komai a gidan, shi yasa duk wanda zaiyi wani abu sai ya neme ta, saboda haka ya sani duk wani information in dai ya taɓa ratsawa da gidan ba lallai ne taƙi samunsa ba. Daddy ya gaya masa cewa mahaifin yarinyar da suke zancen zata shigo rayuwarsa ɗan'uwan Mami ne kuma sunansa Alhaji Sulaiman. Don haka kai tsaye bayan Sameeran ta gama murnar dawowarsa da kuma shaida masa cewar ai direban Hajiya Madinan da yayi clear dashi kafin ya fito titi zai kawo musu abinci yanzu, sai ya tambaye ta. "Waye Alhaji Sulaiman a ƴanuwan Mami?" Shirunta ya nuna alamun tambayar ta bata mamaki amma duk da haka mamakin nata baiyi tsawo ba tace. "Ko wanda yazo jiya? Ɗan'uwansu Hajiyar Mami ne, yana ɗan zuwa dai ba sosai ba." Ya cije gefen lebbensa kafin ya sake tambayarta. "Da yazo jiyan me yayi?" "Bai wani daɗe ba Yaya, Mallam Sani ma aka saka ya tafi dashi office ɗin Daddy wai zasu yi magana." Da jin haka ya tabbata shine wanda yake nema don haka kai tsaye ya sake tambayarta. "Kin san gidansa?" "A'a, amma Mami tace a Gadon ƙaya yake wai wajen layin transformer." Ya gyada kansa. "Kin san sunan ƴaƴan sa?" "Eh, Babbar dai kawai na sani sunanta Amina." Ya riga ya gama samun abinda yake so don haka ya gyada kansa kawai yana gode mata sannan ya kashe wayar, kwatancen daya kawo shi har kofar gidan kenan a yanzu. "Ina Gadon ƙaya." Ya bawa Ishaq amsa ta cikin wayar. "Gadon ƙaya? Wajen wa? Me zaka yi?" "Ni da kai mun sani cewa abinda Daddy ke shirin ba ƙaramin hadari bane Ishaq, don haka zuwa nayi na warware komai tun kafin lokaci yaja da abinda ba zai taba faruwa ba." "What?" Ƙarara mamaki da kuma fargaba suka fito daga muryar Ishaq ɗin, kuma Ma'aruf zai rantse ya shiga girgiza kansa lokacin da yake faɗin. "Kar kayi haka Ma'aruf dan Allah, ka juyo ka dawo. Zuwa wajen mutumin nan ba shine zai kwance komai ba..." "Ba wajensa nazo ba don dashi da Daddy duk abu ɗaya ne. Ita nazo gani Ishaq, saboda a yanzu maganar ta koma ni da ita kawai." "Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un... Ma'aruf me zaka yi?" Salatin ya saka shi sake yin murmushi yana cije lebbensa. "Nuna mata zanyi irin ramin da ake shirin jefa ta, nuna mata zanyi da gaske bani da hankali." "B, tsaya kaji..." Dib. Ya katse kiran ya ma kashe wayar gabaɗaya. Idonsa ya sake kallon ƙofar gidan yayin da zuciyarsa ke zana masa dukkan hotunan abinda zai faru kafin ya kashe motar ya fito. Ya sake janyo hular rigar yana ƙara rufe fuskarsa daidai lokacin da wasu yara biyu mace da namiji suka zo shiga gidan idanunsu akan shi da kuma motarsa. Da sauri ya yafito namijin alamun yazo. Ya kuwa taho yayin da macen ta tsaya tana kallon su hannunta rike da wani abu da take ta lasa. "Bigboy ya sunanka?" Amon muryarsa mai zurfi da taushi ya tambaya sanda yaron ya ƙaraso. "Adam." Ya gyada kansa yana murmushi lokacin da ya zaro wata sabuwar ɗari biyar daga aljihunsa yana miƙo nasa. "Idan ka shiga gidan nan Adam kace wai Amina tazo." "Toh." Ya amsa da nasa murmushin shima sannan ya juya, idanunsa ko kaɗan bama su ga kuɗin da yake bashi ba. Da murmushin da bai san dalilinsa ba Ma'aruf ya maida kudinsa cikin aljihu yana kallon tafiyarsu zuwa ciki, ƴar yarinyar har sai da sake juyowa ta kalle shi lokacin da Adam ɗin yaja hannunta zuwa ciki. A hankali ya dawo da fuskarsa kan katangar gidan, idanunsa na hasko masa dukkan abinda zai faru nan da mintunan dake shirin tahowa! *** Me zai faru?? Me zai faru?? . . . Me Ma'aruf zaiyi?? #Aysha Shafi'ee. #FikraWriters #FararWuta. BABI NA HUDU. ~~~~~ "Kiyi hakuri Amina, amma sun shaida min cewa yaron yana da matsalar taɓin hankali!" A daidai sanda ya rufe bakinsa, a daidai lokacin aka haska wata walƙiya har da tsawa a cikin ɗakin! Kuma bayan walƙiyar ta ɗauke a idanun Amina, Baba ya cigaba da maganarsa. "Wannan maganar ita ta sanya a safiyar yau dana shaidawa Kawu mallam dukkan abinda ya faru ya tara meeting din da ya sanya yinin mu a gidan, don har su Kawu Ibrahim da Kawu Hamza sun zo a yau..." Ba shiri tasirin sunayen ya sanya Amina ta sake ɗago da idanunta ta kalli mahaifin nata, yayyen Baba hudu ne kuma shine ƙaraminsu, Daga Kawu mallam sai Kawu Abubakar da suke kira da 'Baban kurna' sai kuma Kawu Ibrahim da Kawu Hamzan da dukkansu biyun suke zaune a garin Abuja tare da iyalansu, don haka bata san adadin mamakin da zata iya kiyastawa ba na cewar saboda maganarta Kawu mallam ya taso su a yau tun daga can suka zo, ganin yadda Babn ke kallonta yana son fassara yanayinta yasa ta maida idanunta ƙasa a hankali yayin da hannunta na dama ya kamo karshen skirt dinta da ƙarfi. "Amina a jiya babu irin boren da mahaifiyarki bata yi min ba akan maganar nan, dukkan ku shaida ne cewa Halima mace ce mai biyayya gare ni, don tun daga ƙuruciyarku har yanzu babu ranar da ɗayanku zai ce kunji kanmu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73